in

ZULFA CHAPTER 7

ZULFA CHAPTER 7

“Karki damu zuwa jibi zaki fara makaranta”+

Cikin sauri nakoma ta inda yake zaune nace” dagaske kakeyi??”

Batareda ya amsa min bah ya mike tsaye yajuya gurun Umma nah yace” bari nashiga na watsa ruwa”

“Toh afito lafiya”

Tsayawa nayi sororo ganin bai amsa min tambaya ta bah, baikaiga shigewa bah cikeda rashin kunyan dana kware ayinshi nace” Yay Mou hala icce neh ke maka magana anan??”

Tsayawa yayi cakk kaman zaiyi magana amma sai kawai ya cigaba da tafiyarshi yana mai mamakin yanda tayi mishi magana yanxu cos shi Sam baisan hallayarta bah…

Zan sake magana kenan Umma tamin alaman nayi shiru, badan naso bah nayi kum da baki na amma sosai rai na ya baci…

Wanka yakeyi amma gabaki daya hankalin shi akaina yake,babu abinda yafi tabashi sai yanda na mishi magana da bah dan son dayake min bah da yau saiya nuna min matsayina…

Umma nah kawai ya hango azaune cos nikam tsantsan bacin rai bansan yaushe na shige daki yin bacci bah dukda uwar yunwan danake ji…

Bayan ya zauna yace”Ina take Umma??”

“Inaga bacci tashiga yi”Umma ta bashi amsa

“Taci abinci kuwa??”

“Bata wani ci bah wai tace abincin bai mata bah”

“Dadi take nufi ko miye??”

“Erh wai bai mata dadi bah”

Zaro Ido yayi yace”unbelievable!!!”

“Miye faru?” Umma ta tambaye shi

“Umma wlhy mamaki naji ,takuwa san waye mai yin girkin gidan nan kuwa??”

Ido Umma ta zuba mai tana jiran miye zai ce,jin baiyi magana yasa Umma tace”waye mai girkin gidan nan??”

Sanda ya shafa kanshi tukunna yace” bakowa bane face _Mario Batali_wanda ya kasance mutum na biyu acikin mutane goman dasuka yi fice a girke girke acikin fadin American nan(wato second top chef in America)”

Rike haba Umma tayi da jin abinda yafada, itama tasan Zulfa tafada neh kawai amma hakikanin gaskiya abincin bakaramin dadi yayi bah…

“Bari na tasota karta kwana da yunwa yau ma” bai jira cewarta bah yayi dakin su…

Akan gado yasameni wanda nayi nashe nashe ina kwasan baccin wahala.

Sif ya nufa yadauka min doguwar riga da gyale cos harna cire kaya nadaura towel dukda uban sanyin da ake agari amma kasancewan akwai room heater acikin dakin shiyasa ban wani ji sanyi bah…

Dawowa yayi yazauna agefen gadon ahankali yajawo ni jikinshi tareda saka min kayan daya dauko min yana gama samin ya zare towel din sannan ya hau tashina…

Juya mishi baya nayi cos nariga nagane shine soboda perfume dinshi dana shaka

Cikin sanyin murya yace”Zulynah”

Turo baki nayi nace” kadaina kiran suna na tinda daman banda amfani awajen ka”

“Miyesa kike magana haka neh Zulynah??”

“Ai dole katambaya tinda har nine zan tambaye ka abu kaki bani amsa”

“Am sorry amma kin bata min rai neh shiyasa nayi shiru”

Cikin sauri najuyo jin abinda yafada kallon shi nayi da kyau nace” na bata maka rai fah kace??”

“Erh mana” yafada in serious tune
“Miye nayi toh??” Ta tambaye shi

Tashi yayi tareda Mika min hannu yace”You somehow lack manners”
Hannu na nima na mika mai kafin na girgiza kai nace” nifa nace maka bana jin abinda kake fada da turanci”

Samin dankwali yayi yace”Toh saiki ajiye acikin kwakwalwar ki duk randa kika fara jin turanci zaki san ma’anar abinda nace”
Tabe baki nayi nace”toh, amma ina zamuje naga kasamin kaya??”

Atakaice yace”Restaurant”

“Ina neh kuma hakan??”natambaye shi

“Wajen cin abinci neh”

Tabe baki nayi nace”abincin da duk babu dadi nidai babu inda zanje”

Rike hannu na yayi gam yace”mu jeh dai cos yunwa nakeji sosai tin safe ban karya”

Zaro Ido nayi cikeda tausayin shi nace”ayyerh sannu yay Mou dina”

Gyada kai kawai yayi muka fito palour,kallon Umma nah yayi yace”Umma bari muje mu dawo”

“Toh adawo lafiya

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 6

GADAR ZARE CHAPTER 1