in

ZULFA CHAPTER 6

ZULFA CHAPTER 6

ZULFA CHAPTER 6

Umma dake jinsu acikin gida tasake murmushi jin abinda tace” ni bazan bika nabar Umma nah bah”+ Ajiyar zuciya yasauke jin abinda tafada kuma yaji dadin hakan da tayi “Ai da Umma zamu tafi” Cikin zumudi tace” dagaske kake yi??” “Ai bazan miki wasa da irin wannan abin bah” “Wayyo dadi kenan bazamu rabu bah kullum Muna tare ” tafada cikin murna Murmushi yayi yace”erh Muna tare” “Ina zuwa” ta tashi tareda nufar cikin daki “Umma ki fara hada mana kayanmu mun kusan barin gari” Kallon ta Umma ta tsaya yi tace ” ai naga babanki bai yarda bah tukunna” “Sai ki dinga kiranshi da
baba na” tafada tana murguda baki Wani dum Umma taji acikin ranta tace”ai baban ki neh” Girgiza kanta tayi tace” ai dolanci na bai kai haka bah,bayan ko yaushe a class sunan babana daban dana su Marwa” Ajiyar zuciya tasauke tace”koma dai Yaya neh sai ya yarda tukunna” Batareda tayi magana tafice zuwa palour inda Mourad yake jiran ta… ”’washe gari”’ ” Haba mai martaba taya za’ayi kace Umma ceh zata bita??”Hindatu uwar gidan Malam tafada cikin Jin haushi “Daman waye zai bita??” Ya tambaye ta cikin isa “Naga akwai Marwa miye zai hana su tafi tare kuma kaga duk sa’oin juna neh sai su cigaba da karatun su “Wannan wani irin magana kike fadi neh hakan?? Taya za’ayi atura kana nan yara su kadai uwa duniya… Caraf Zuwaira Amaryan Malam tace” gani sai na bisu na kula dasu” Girgiza kanshi yayi cikin takaici yace”kun dai san mahaifiyar yarinyan nan bazata yarda bah” ” Malam ko ka manta ba ita ta haifeta bane Kam??” Ta tambayan daidai isowar Umma da Zulfa wajen “Gaskiya Kam Malam ai muma muna da iko akan yarinyan kawai dai munyi shiru neh,in tana son tayi iko akan y’a ta haifo nata itama” Zuwaira tafada Wani irin nauyi Umma taji akirjin ta kaman an daura mata katuwar dutse akai. “Erh bazallan ita keda iko akan Zulfa bah”Malam yafada Zuciya neh taciyo Umma tace” sai miye in bani nah haife Zulfa bah? Nace sai miye??” Afirgice Zulfa ke kallon fuskar Umman ta tareda girgiza hannunta “Basai kunmin gori bah yau na yarda bani na haife ta bah amma kusani ko iyayenta bazasu kaini sonta bah, ina ce don karna bita kuka tada magana?? Toh bazan bita bah saiku zuba ruwa akasa kusha” Kallon Zulfa Umma tayi hawaye na zubowa daga idonta tace” bazan iya cigaba da boye miki bah Zulfa bani ceh na haife ki bah ni kanwar mamanki ceh” Wani kuka Zulfa tafashe dashi tace” ni ke kadai nasani kece Umma nah kuma ke kadai nakeso. “No Zulfa sun riga sun fada abinda ban kaunar ji so kisani ni bah mamanki bace”tana gama fadin hakan ta fice cikin sauri. Sosai jikin su yayi sanyi ganin yanda Umma tafita tana kuka mai tsuma rai. Itama Zulfa dagudu tabi bayan Umman ta, daki tasamu Umma sai kwasar kayanta takeyi tana sa wa a

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 5

ZULFA CHAPTER 7