in

ZULFA CHAPTER 3

ZULFA CHAPTER 3

gaskiya sosai abin yamata dadi tinda taji Alkheri,batareda ta gama jin abinda suke fada bah tayi gaba abinta. Kuma tasha alwashin saita raba tsakanin su tinda ta lura Zuly akwai iya kishi. Share hawayen shi yayi tare da tattara duk nutsuwar shi yahada waje daya sannan yace “Zulynah so kike ki Kashe ni neh??” Cakk kukanta yadauke cos yanda yayi maganan muryan shi na rawa. Cikin sauri tajuya wajen shi still hawaye na zubowa daga idonta. “Zulynah wlhy Siyah is just my cousin and nothing else kinji na rantse” “Really??” Gyada kanshi yayi while zuciyan shi tafara rage tsallen dayake hoping zata fahimce shi. “Shine tace kai zaka aureta??take kiranka da my sweet??”tasake tambayan shi “I can explain” yafada Kura mishi ido kawai tayi sannan tace”with that passionate hug??with that melting smile of yours??and you said you can explain?? Explain what in the first place?? I don’t think i need your explanations you should keep that with you cos bazai min amfani bah illa bakin cikin da zai kara min. Zaiyi magana ta katse shi dafadin” and yes I need some fresh air, I mean I need privacy you should excuse me, and tell Ammi anjima Zan tafi. Tana gama magana tashige bayan gida tareda slamming kofa, yasan koya buga kofan ba lallai tajishi bah soboda ruwan data kunna. Jiki asanyaye yafice zuwa dakin Ammi, dukkansu yasama adakin straight wajen Siyah tanufa ai baiyi wata wata bah yatsinka mata mari. Agigice tamike cos zata iya rantsuwa tinda take arayuwar ta ba’a taba marinta bah. Fakih mah mikewa yayi, yatsa yanuna mata tareda fadin”miye Kika fada wa Zulynah??” Nan da nan jikin ta ya hau bari Fakih neh ya janye shi tareda fadin” haba yaya wannan wani irin abu neh?? Gwada ta fah mukayi yi koh itama tana sonka. Wani tsaki yaja sannan yace”sa ku nayi ?? Girgiza kansu sukeyi, Siyah kam Sai tsine wa Zuly takeyi azuciyar ta. Zai sake magana kenan Ammi takira shi,ai kaman jira yakeyi daman takira shi din. Dasauri yanufe ta ,yana zuwa yazauna akasa tareda daura kanshi akafarta yana mai fashewa da kuka. Gabadaya dukkansu mamaki neh yacika su jin abinda yakeyi sunsan yana sonta amma basu taba zaton zaiyi kuka soboda ita bah. Shafa kanshi takeyi tareda fadin”fada min abinda yafaru” “Ammi nah tayi fushi dani” yafada cikin shesheka gabadaya Sai Siyah taji bah dadi aranta Ajiyar zuciya tasauke sannan tace”saikuma miye??” Shiru yayi sannan yace”tace tafiyanta zatayi anjima, tace karna sake mata magana,Ammi DanAllah kitayani bata hakuri kice mata bazan kara bah” yafada hade da tashi yana mai Jan hannunta. Sai binshi takeyi harya kawo ta gaban kofar dakinta,suna isa ya share hawayen shi tareda bude wa Ammi kofa. Zai shiga kenan Ammi ta dakatar dashi”excuse us koh soboda naji dadin tsara maka ita” Gyada kanshi yayi tareda sakin murmushin dabai shirya yinshi bah. Shiga tayi cikin dakin tasami Zuly akan gado, jin anshigo dakin neh yasata fadin” nace maka I need privacy koh” Jin ba’a yi magana bah yasata sakin wani kuka “Yah Salam!!!” Ammi tafurta asarari, jin muryan Ammi yasata tashi tana share hawayen fuskanta. Murmushin yake ta aza asamar fuskarta tareda nufan inda take “Sannu da zuwa Ammi, ai dakin min magana nazo” tafada kaman babu wani abin aranta “Miye sameki kike kuka?” Ammi tafada cikin son jin abinda zatace “Babu komai fah Ammi, yauwa Yay Mou yafada miki yau zankoma koh??” “Haba dai??”ta tambaya kaman daman bata sani bah “Erh Ammi zantafi, zuwa 4 pilot dina zai iso” “Mun miki laifi neh kike son komawa yau??” “a’a Ammi” “Toh miye faru tsakanin ki da Mourad??” “Babu komai fah Ammi”tafada with full confidence “Basai kin boye min bah ya fada min,danAllah kiyi hakuri ki yafe mai” Ammi tafada tareda hade hannayenta “Haba Ammi basai kin bani hakuri bah Allah komai yawuce yanzu”tafada tana ware hannun Ammi din “Kice kin yafe mai soboda naji dadin mishi albishiri” murmushin jin dadi Zuly tayi sannan tace “Nayafe mai Ammi” Murmushi Ammi tayi sannan tace “yauwa Zulyn Mourad Allah yamuku Albarka” “Ameen Ammi” “Yau din zaki tafi ko kin fasa??”Ammi ta tambaya “Naso na tsaya amma nariga da nayi rantsuwa” tafada cikeda rashin jin dadi cos saiyanxu tayi danasanin rantsuwan da tayi “Ai shiyasa akace babu kyau rantsuwa da dawuri”Ammi mah tafada tareda tashi ” Barina rakaki” Fita sukayi suka har daki ta raka Ammi anan neh Kuma ta hadu da su. Yana ganin ta ya nufo su, ganin yanda idon Zuly yakumbura yasa shi sanin har ya fita kuka takeyi. “Am so sorry Zulynah”yafada tareda kama kunne, dasauri tacire hannunshi daga kunnen sannan tace “It’s okay” “Sure”yafada cikin murna Gyada kanta tayi,cikin tsantsan farinciki ya rungumeta ajikinshi, dan tureshi tayi daga jikinshi wanda abin bakaramin bashi mamaki yayi bah. Zaiyi magana kenan Siyah tarigashi inda tace”am sorry Zulyn Mourad” Murmushin yake suka sakar wa juna batareda sun sake fadin komai bah. “How far inace kin fasa tafiyan??” Siyah tafada amma azuciyar ta Addua takeyi Allah yasa tafiya zatayi “No zantafi cos nariga da nayi rantsuwa” wani Farinciki neh ya dabaibayi Siyah amma saita boye tace “Ayyerh yanzu how about the waliman danace nashirya miki??” “Nagode sosai amma am sorry saidai in wani lokaci” Cikeda nuna rashin jin dadi tace “toh Allah yakaimu wani lokacin” “Ameen” *3:45pm* Angama shigar mata da trolley dinta cikin mota while kowa na tsatsaye ana jiran fitowan Ammi. Ga Fakihah mah da danta saikuma balaraben mijinta,su Siyah kaman su zuba ruwa akasa susha tsantsan farinciki amma a fuska sunfi kowa nuna basu ji dadin tafiyan ta bah. Hannun Mourad cikin na Zuly cos sosai yashiga matsananci damuwa soboda jikinshi na bashi cewan Zulyn shi takusan barin shi.+ Fitowan Ammi da leathern shopping neh yasasu miyarda hankalin su kanta. Nufan wajen Zuly tayi tareda mika mata leathern sannan ta rungumeta ” Zamuyi missing dinki Zulyn Mourad”tafada cikin sanyin murya “Nima haka” Ammi nasakin ta Siyah ta matso kusa daita tareda bata wani karamin leather. Itama runguman ta tayi sannan tasa bakin ta adaidai kunnen Zuly yanda babu wanda zaiji ta sai Zulyn sannan tace…

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 4