in

ZULFA CHAPTER 3

ZULFA CHAPTER 3

ganin…Tana karasowa Ammi tacire kyallen da aka rufe shi dashi,gwalalo ido Zuly tayi dalilin ganin wata Heart of the ocean necklace mai shegen kyau da tsada… “My sweet Zulynka tayi yi kyau sosai”Siyah tafada cikin danne kishinta Murmushin samar fuskar shine ya fadada cikin jin dadi yace” kaii mungode kuma kema kinyi kyau. Wani dadi taji yaziyarce ta cos rabon dayace tayi kyau harta manta zatayi magana kenan sukaji muryan Zuly “Yay Mou dina inasonka” tafada yanda zasujita bayan Ammi tace mata shi ya siya. Mamaki ne yakama su Ammi jin abinda tafada bako kunya. Duk wani farincikin dataji saita neme su tarasa zuciyar ta har zafi zafi yakeyi amma dukda haka danne… Ammi ce tadauko necklace din bayan tagama makala mata dankunnen shi. Rike hannu Ammi din tayi cikin sunkuyar dakai ahankali tace” Ammi karmu wahalar dake” Kafin Ammi din tayi magana har takarbe necklace din tareda yin wajen Mourad dashi. Tana mika mai ya karba cikin murmushi tareda daura mata a wuya, runguman shi tayi sannan tace “godiya nake yay Mou dina” Murmushi kawai yayi while tayi breaking hug dinsu. Yanxu kam mah sun daina mamakin su… “Muje karmu sasu suyi tajira”yafada mata tareda riko hannunta “Mun tafi Ammi” yasake fada tareda nufar daita wajen mota “Allah lafiya” Ammi mah tafada cikin jin dadi cos bakaramin burge ta sukayi bah. Su Fakih ma nufar motansu sukayi cos tare zasu tafi.. “Sis nalura da wani abu”Fakih yafada lokacin da suka shiga mota dayake mijin Fakihah yazo(Wato tare zasu tafi) “Miye fah” tafada cikin boye damuwar ta “In kinason yaya yadawo kula ki sosai toh dole Sai kin ajiye kishi agefe kin nunawa abinda yake so soyayya”yafada tareda yin shiru “Anya Zan iya kuwa??” Ta tambaye shi “Zaki iya mana,just try to show that thing a fake love agaban shi” “Ohk I will try” “Yauwa sis,Allah yabaki Yaya” Bakunya tace Ameen. Suna isa wajen taro akafara shooting dinsu ta kowani bangare, kuma bakaramin dacewa sukayi da juna bah wasu mah sun dauka miji da mata neh… Wata hadaddiyar tray mai dauke da scissors aka kawo mata ba bata lokaci suka yanka… “Miye kike nema neh wai??” Taji yatambaye ta soboda waige waigen datake tayi. Kirkiran murmushi tayi sannan tace”babu komai” Amma aranta mamakin abinda ya hana shi zuwa take, ai kodan ita ta tura mai invite din dakanta yakamata yazo. Dukda mah last dasukayi magana yace mata yana son su hadu,kenan mah karya yakeyi… Sosai abin yamata zafi aranta amma babu yanda taiya danne duk abinda ke damun ta tayi gudun kar Mourad ya fahimta. Wani tunanin da ya shige ta neh yasa tayi maza taciro wayarta acikin jaka. Kiran numbern shi take yi amma harya tsinka ba’a dauka bah. Hadiye duk wani abu tayi sannan ta miyarda wayarta cikin jaka cos aduk rayuwarta Mourad neh kawai take iya mishi missed calls dayawa amma sauran kam inta Kira sau daya ba’a dauka bah toh shikenan. Yana Lura da yanda take yi ya danne zuciyar shi ya share tinda tace babu abinda take nema amma sosai nutsuwar shi ya koma gareta. Suna hada ido tasakar mishi murmushi,mutane Sai congratulating dinta sukeyi. Abinda yabata mamaki shine yanda Fakih da Siyah suke kaffa kaffa daita,sosai suke nuna kulawar su gareta wanda yasa ta aza ayar shakku akansu. Ganin yanda suke mawa Zulynshi neh yasashi sakar musu fuska sosai harda darawa sukeyi. Sosai abin yamawa Siyah dadi tinda gashi sanadiyar fake love dinda take nunawa Zuly yake kulata. Angama taro lafiya, anci ansha sannan kowa yakoma muhallinsa, Siyah kamar karsu tafi cos rabon da tasamu care irin wannan daga wajenshi harta manta,itakam Zuly tasaki ranta tinda tasan yay Mou dinta bason Siyah yakeyi bah. ”’washe gari”’ Zaune suke akan dinning table zasuyi breakfast amma tsantsan gulma irin na Fakih da Siyah Sai suka sanya Zuly atsakiya cos su suka dauko ta daga daki. Tinanin inda tashiga yake yi amma hangan ta dayayi atsakiyar su Siyah yasa shi sakin murmushi tareda Adduan Allah ya bama Siyah din miji nagari. “Yay Mou dina kashigo mana ” tafada tana lumshe ido Lumshe idon datayi neh yasasu tabe baki tareda juyawa baya suka kallo bakin kofa ga mamakin su sukaga Mourad ya harda hannuwan shi a kirji yana kallon su Cikeda mamaki Siyah tace”ya akayi kikasan ya shigo bayan kin bashi baya Murmushi tayi sannan tace” aduk lokacin da yay Mou ya bayyana awajen da nake toh ba makawa zuciya tace zata fara sanar dani isowar sa” Mamakin irin wannan soyayyan su neh ya rufe su ,Sai Siyah tafara jin ashe son da take mishi mah bakomai bane(Kin fara Karaya kenan…hhh) Tashi tayi daga inda take zaune sannan taje ta mishi iso cikin murmushin ta mai sace zuciyar mutane. “Barka da safiya yay Mou” tafada dukda dazu bayan an dawo daga masallaci sun gaisa( muryan shi take ji last kafin tayi bacci,kuma shi take fara ji dasafe). Jan kumatunta yayi sannan yace”ya Kika kwana?” “Alhmdllh gidan nan so sweet wlhy’ tafada cikin murmushi “Haka dai Kika ce” “Muje kazauna kafin Ammi tafito”tafada tana janshi zuwa kan kujera ,yana zama kuwa saiga Ammi mah ta shigo. Cikin sauri taje ta tare Ammi din tareda mata ina kwana, amsa mata Ammi din tayi cikin fara’a while bakin ciki gona sha biyu suka dabaibayi Siyah. Zama sukayi suka ci abinci sannan Siyah tace tadan hada wa Zuly karamin walima. Sosai suka ji dadin abinda tayi Mourad kam ma harda rungumeta ajikinshi. Wannan abu yamata sugar sosai itakuwa harda pecking dinshi tana shashafa mai kirji ,abinda take mishi bakaramin dadin shi yakeji bah sai lumshe ido yakeyi kaman Ammi bata wajen amma saidai abinda sukeyi da Mourad neh yakona wa Zuly zuciya. Nan da nan kuma annurin fuskanta ya bace wanda Ammi ta lura da hakan. Excusing kanta tayi domin ganin yanda Siyah take shishigi mai, abin bakaramin dukan kirjin ta yayi bah kuma gashi Mourad dinta ya boye mata Ganin tabar wajen neh yasashi bin bayanta cikin sauri cos yaga yanayinta ya chanza… “Zulynah miye sameki??” Yatambaye ta daidai ya cin mata adaki. Kawar da kanta tayi alamun batason ganin shi, nan da nan hankalin shi yatashi “Miye neh wai??” Yatambaya agajiye “Why do you care??” Ta tambaya a hasale Zaro ido yayi cos bata taba mishi magana cikin irin wannan sigar bah “Wai miye kike magana haka” “Karka takuramin min kaji, kaje kasame wanda kake ta rungumewa nasan tana chan tana jiranka”tafada tareda fashewa da kuka cos in tatina yanda Siyah take shishige mai saitaji zuciyar ta na zafi Sosai abin yabashi dariya ai nan kuwa yahau darawa ganin kishin shi takeyi.. Dariyan shi neh yasake tunzirata nan kuwa zuciya ta debe ta batareda tasake yin magana bah ta wuce straight wajen sif. Kayanta ta hau tattara wa tana zubasu acikin trolley daman sunyi akan zatayi one week neh amma abinda yafaru yau yasa taji bazata mah iya ko kara kwana bah. Ganin abinda takeyi neh yasa dariyan shi dauketa, cikin sauri ya isa wajenta. “Haba Zulynah miye abin fushi anan” yatambaya cikin Sanyin murya Ko magana batayi bah ta cigaba da abinda takeyi ganin tana niyar zuge trolley din neh yasashi finciko ta jikinshi. Tirjewa tashiga yi ga hawaye sunki daina gangarowa daga kwarmin idonta. Ganin zata bata mishi lokacine yasashi rungumeta tsam ajikinshi,itakuwa banda bugu babu abinda take kai mishi. Tureshi tayi da duk karfin da Allah yabata nan kuwa suka rabu Idonta arufe take fadin”karka sake rungumata kaje wajen wancan ka rungumeta,wlhy tafiyata zanyi bansake kwana daya agidan nan kuma daga yau karka sake min magana nima bazan sake bah daman kuma tace min aurenta zakayi sbd haka nabarku tare” Gabadaya ji yayi duniyar namai zafi, wasu zufa ce suka shiga tsatsafo mishi soyake yayi magana amma yakasa. Kawai saiga hawaye sun fara zubowa daga idonshi, ga sautin kukanta bakaramin wargaza mai kwanya yakeyi bah. Siyah dake labe abakin kofa tanajin komai tasake wani murmushin farinciki sannan tajuya tayi gaba, tasan ance babu kyau labe amma hakikanin

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 4