in

ZULFA CHAPTER 3

ZULFA CHAPTER 3

tace”Fakih you never fail your promise so don’t fail it this time around” Murmushi yayi yace”trust me sis” “In haka neh to I will forever be grateful to you”tafada cikin farinciki,cos tasan tinda Fakih yamata Alkawari toh magana yakare… Azaune take Daure da towel akirjin ta wanda yakawo mata dai dai cinya,tindazu take jiran Fakihah wanda taje dauko kayan da zata fita dashi tindazu har tana neman minti 30kenan. Sosai taji dadin yanda Ammi da Fakihah suka tarbeta they are so nice amma yanda Fakih yamata neh yake cin mata tuwo a karya,saikuma wannan balarabiyan dabatasan waye ita bah. Amma tabbas tasan wannan balarabiyan tasanta tinda har take mata kallon hadarin kaji kaman daman akwai differences atsakanin su. Turo kofan da akayi neh yasata fara magana batareda ta juyo bah” haba DanAllah tindazu dakika tafi,ai da mai basir neh dayanzu ya motsa,kin wani shanya ni bacin kinsan banason yay Mou dina yayi ta jir….” Shiru tayi SAKAMAKOn rashin amsa da isowar Fakihah da take jira bah, ahankali take juyawa. Dasauri ta tashi tana dafe kirjinta sabida wata faduwar gaban daya ziyarce ta dalilin ganin wanda batayi tsammanin gani awannan lokacin…. *Kowaye tagani haka??**Mourad* Dasauri ta tashi tana dafe kirjinta sabida wata faduwar gaban daya ziyarce ta dalilin ganin wanda batayi tsammanin gani awannan lokacin bah. Cikeda takama take takowa harta isa gaban ta,itama din daidaita nutsuwar ta tayi dukda sosai tsoron Siyah ya darsu aranta. “Zulyn Mourad koh”tafada cikin ya mutsa fuska kaman mai taunan kashi. Hadiye wani abu tayi sannan tace” wannan bah karya bane nice nan Zulyn Mourad amma saidai ni bansan wace ke bah” Wani irin bakin ciki ne yasake ziyartar ta,ace duk shekarun nan dasuka yi da Mourad amma baiyi ma Zuly maganar ta bah amma gabadaya shekaru hudu kawai Mourad yayi da Zuly amma duk wanda suke kusa dashi sun Santa. Murmushin dayafi kuka ciwo tayi sannan tace”suna na QUDSIYAH!!!Mourad baitaba fada miki cewan nine zai aura bah?” Gabanta neh yayi mugun faduwar dajin abinda Siyah tafada amma saita daure tace” ya Salam abin mamaki nikam tinda nake arayuwa ta kome irin sunanki mah bantaba ji bah, kuma ni a iya sanina haryanzu yay Mou dina baiga wanda zai aura bah, so ya akayi Kika zamo wanda zai aura bansanibah?? Siyah alokacin tagama cika amma saita ce “abu daya nazo fada miki,kisani cewan Mourad nawa neh ni kadai,cos da iri na yadace bake bah kuma kiyi gaggawan fita daga rayuwar shi inba haka ba…” “In bah haka bah miye zai faru Siyah??” Fakihah takatse ta da tambaya Kallonsu suka miyar ga Fakihahn dake rike da trolley din kaya, batareda Siyah takara magana bah tayi waje cikin jin haushi. “Waye ita??”shine abinda tasamu bakinta da fada, ajiye trolley din tayi sannan tabude tafito da makeup kit tareda zaunar daita akan kujera Sanda tafara mata kwalliyan tace “Sheik Maktoum bin Rashid Al Maktoum shine ainihin sunan baban mu wanda yakasance Emir din Dubai shekaru dasuka wuce, yana da mata 4 wanda Ammi dinmu ceh nafarkon su kuma takasance yar Nigeria kuma bahaushiya. Mu uku Ammi dinmu tahaifa inda Yay Mou dinki yakasance babban cikin mu. Tinda muka tashi Ammi bata mana magana da labaraci saidai Hausa cos cewa tayi bata son yarenta ya bace, shiyasa kikaga mun iya Hausa sosai. Mamaki ne yacika Zuly jin waye su Mourad cos koda kadan baitaba mata wannan zancen bah ita dai kawai tasan suna da kudi amma ba wannan bane yadameta so take taji alakar dake tsakanin Siyah da yay Mou dinta Numfasawa tayi sannan tace “bayan nan fah?” Mourad yayi karatun shi a Royal College of Surgeons in Ireland (Dubai) shida Siyah inda suka karanci Cardiology har PhD suna dashi. Sun kasance one of the best doctors damuke dashi cos basu taba yin operation din da baiyi successful bah. Sun samu Awards dayawa kuma bayan nan yayana shine CEO din companyn Abuu dinmu. Mourad yakasance mutum mai rauni amma fa akanki, in Kika ga Mourad bazaki taba cewan he’s a cardiologist bah. Tin suna yara Siyah takamu da matsanancin son yayana sanadiyar shakuwan dake tsakanin su cos komai tare sukeyi dukda yaya ya girme ta da shekaru 6. Tin kafin yasanki yake bala’in son wanda sunanta yafara da Z harya kaishi dayin tattoo da farkon sunanki Tin kafin ki shigo rayuwar yayana Siyah ta bayyana mai sonda take mishi amma yayana cewa yayi shi amatsayin kanwa yadauke ta kuma yasan tabbas wata na jiranshi. Bayanda ba’ayi da Siyah tayi aure bah tinda tanada manya manyan manema amma tayi burus tace Sai yaya. Bayan rasuwar Abuu dinmu aka nada kanin Abuu dinmu wato Muhammed bin Rashid Al-Makhtoum, Wato the vice president,prime minister and also the Emir of Dubai wanda yakasance uba ga QUDSIYAH kenan we guys are cousins “Idan nagane bayanan ki kenan sokike kice min ita kadai ke kidanta dakuma rawanta??”tafada cikin murmushin farinciki “Tabbas haka wannan batun yake Zulyn Mourad” itama ta miyar mata da murmushin. Izuwa lokacin kuma har Fakihah tagama tsara mata Arabian glam makeup dinta. “Mungama”Fakihah tafada tareda barin gaban mirror din, gwalalo ido Zuly tayi SAKAMAKOn harbawan data yi da new look dinta. “Kinyi kyau sosai Zulyn Mourad anya zaki bar yayana yasha ruwa kuwa??” Fakihah tafada cikeda zolaya Sunkuyar dakai kawai tayi domin tinda take bata tabayin kwalliyan dayakai wannan kyau bah. “Fakihah nagode sosai” “Ba damuwa ai yiwa kaine kuma InshaAllah a aurenku baza’a wani bata kudi wajen dauko mai makeup bah nida kaina zan chanchara miki”tafada lokacin da tayi loosing ribbon din jikin gashin Zuly. “Kai Zulyn Mourad kinada gashi saikace bafulatana” “Ai mahaifiyata bafulatana ce babana ne bahaushe” “Gaskiya Kam alamu sun nuna hakan” batareda sun sake magana bah Fakihah tafara gyara mata gashin ta. Katse shirun Zuly tayi dacewan”ina babynki??”(daman tana da aurene??) “Yana wajen babanshi kinsan yau ba yayinshi nakeyi bah tinda gaki kinzo”. Dariya kawai Zuly tayi tana mai jin dadi azuciyar ta. Wayarta dake karane yasasu dakatawa daga tayata sa kayan da Fakihah keyi,daukan waya tayi da murmushi afuskarta tareda karawa a kunne “Yay Mou dina !!!” Tafada cikin shagwaba Wani irin yanayi mai wuyar fasaltawa yajishi aciki na yen secon ni kafin ya furzar da iska sannan yace”Zulynah kinyi sallah kuwa” Kaman tana gabanshi tafara girgiza kanta Jin tayi shuru yasa shi sanin batayi sallahn bah ahankali yace”oya aje ayi sallah kafin lokaci yawuce” “Ohk Yay Mou ” Batareda yasake magana bah yakatse Kiran daman ita yake jira cos yariga yagama Shirin shi. Dakin Ammi yawuce inda anan ya hadu da Fakih nan kuwa ya tsigaleshi tass Ammi ma harda sa baki. Wani haushin Zuly neh yasake kamashi cos tinda yake ba’a taba mishi fada bah sai akanta amma ya dau Alwashi Sai Mourad ya auri Siyah takowani hanya. Daman Already tanada Alwala sallah ta tayar ita kuma Fakihah ta fice domin yin wanka. “Masha Allah”shine abinda suka furta atare sanadiyar hango Zuly dasuka yi cikin wata peacock feather flowing gown mai kyaun gaske wanda yazauna dass ajikinta. Kwalliyan dake fuskarta mah abin duba neh saida wani Hermès birkin bag na companyn Japanese designer mai shegen kyau.(nace ko ran aurenta Sai ahaka) Kanta yane da Lace Juliet Cap Veil sosai yamata kyau, Fakih mah saidaya yabata acikin zuciyan shi, Siyah kuwa gabadaya saita raina nata kwalliyan datayi… Ahankali take takowa ga bayan riganta sai shara yake yi, Karan cameran dataji neh yasata dago kanta caraf Mourad yakara daukan wani. Murmushin ta mai kyau tasakar mai shikuwa harda wani lumshe ido tareda miyar mata da murmushin. Hannun da Ammi tamika mata takama,kissing din hannun Ammi tayi cikeda sha’awar ta sosai tadinga Adduan Allah ya mallakawa danta wannan baiwar Allahn azuciyar ta. “Tabarakllh Zulyn Mourad”Ammi tafurta tareda runguman ta,breaking hug din tayi tareda juyawa wajen Mourad daya kafeta da idon shi har lokacin kuwa murmushi neh kwance asamar fuskarshi. Mika mata hannu yayi alaman ta taho batayi musu bah ta isa gareshi,hannunta yakama shima yayi kissing. “You look extremely taking away” cikin rada yafada mata daidai ya hadata da jikinshi. “Ai kafini haduwa yay Mou har banson kafita ahaka” Waro ido yayi bayan sun raba hug din cos yasan in suka dade ahakan zai iyayin abin kunya sannan yace”ai ni yakamata nace banson kifita ahaka amma kuma lokaci yakure da babu inda zakije ahaka” Dariya tayi tareda zaro harshen ta alaman gwalo. “Karki sa na chanza mind dina fah” yafada kaman wani boss harda su zare ido Gwalo idanu itama tayi sannan ta turo bakinta kafin tace”toh kayi hakuri” Gyaran muryan da Fakih yayi neh yasata nutsuwa cos ko kadan batason tayi ba daidai bah a gabansu. “Zoh ki karba Zulyn Mourad kafin ku makara” Ammi takirata Komawa tayi wajen Ammi din, mika hannu Ammi tayi Sai ga yar aikinta daya da tray a hannun ta. Tana karasowa Ammi tacire kyallen da aka rufe shi dashi,gwalalo ido Zuly tayi dalilin

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 4