in

ZULFA CHAPTER 3

ZULFA CHAPTER 3

yace”yaushe zaki tafi??” “Ai inaga gobe Zan wuce and make sure kin zo idan kin gama exams dinki”Umma tafada Zaro ido Zulfa tayi sannan tace”wai ni dadewa zakiyi neh??” “A’a duk yanda takama” Ajiyar zuciya tasauke kamin tace”bari na Kira James(pilot) saiya shirya”dayake tanada 3different private jets, daya Mourad neh yabata shi amatsayin birthday gift,daya kuma tasiya da kudin ta while dayan daya rage mah it’s also a gift. Kiran James tayi dakanta sannan tafada mai zaitafi da Umma Nigeria washe gari cikin commanding tune. “Bari na tayaki shirya kayanki” Zulfa tafara wa Umma Gyada Kai kawai Umma tayi Sai suka tsinkayo muryan Mourad inda take musu saida safe. Rakiya tamishi har bakin mota cikeda rashin jin dadi cos bataso yatafi yanzu bah amma babu yanda taiya… *2weeks later….* Bayan tafiyan Umma sosai abubuwa suka mawa Zulfa yawa ga exams, shopping mall dinda akayi a Abuja har an bude shi(Zulyn Mourad shopping mall) amma batasamu hallartar taron bah soboda exams amma an wakilce ta ga kuma taron bude *art gallery*dinta a Dubai wanda yanxu baifi sauran kwana biyu bah… Sosai suke shirye shirye inda tayi ordering tsadaddun kayan dazasu sa ita da Mourad dinta… Ga Umma ta matsa mata tadawo Nigeria, ita Sam bata son komawa yanzu,batason barin Mourad dinta cos ji takeyi ajikinta in takoma zata jima bata dawo bah… Mourad kam yarasa miyesa in Zuly tace mai zata koma Nigeria yake jin faduwar gaba… *P sector,Villa in Emirates Hills Dubai…* Motoci masu daukan ido kusan 10 neh suka shigo ajere Sai wani White *rolls Royce sweptail*atsakiya, ma’aikata duk sunyi tsaye anajiran su wuce cos ka’idar gidan neh in dan gidan yazo wucewa to dole neh atsaya… Ammi nagani cikin shigar alfarma na manyan mata masuji da ilimi,kudi,mulki da sarauta, tsaye take abakin kofa, while bayunta suna daga bayanta ajere. Murna datake ciki baya misaltuwa kasancewan yau zata fara gin ido da ido da sarauniyar birnin zuciyan danta. Fitowan shi daga cikin motan neh yasa ma’aikatan dada kamewa,cikeda izza yake takawa har ya isa dayan bangaren murfin motan. Murmushi kwance asamar fuskarshi ya bude murfin mota, mika mata hannun shi yayi sannan takama,fitowa tayi ahankali tana shire shade din idonta domin ganin cikin gidan da kyau. Masha Allah shine abinda tafurta azuciyar ta cos gidan yayi mugun haduwa,iska ya hura mata ganin kaman hankalin ta baya gareshi,cikin tsokana yace “Kodai kauyancin neh ya motsa”buge kirjin shi tayi sannan tace, “Babu wani kauyanci ai ko mai kudin dukka duniyar nan yazo nan Sai ya saki baki balle kuma ace ni Zulyn Mourad” Dariya sannan yace “see you toh ai infada miki gidanmu yafi wannan haduwa indai haka neh” “DanAllah fah?.”tafada cikin zaro ido “Erh mana” yafada da murmushi afuskarshi “Wow can’t wait to see it”tafada cikin shagwaba Lumshe idonshi yayi cos alokaci daya yaji tsigar jikinshi ya tashi. Ammi kam dataga tindazu sun fito amma alama mah basu mah San daita awajen bah yasata karbar wayanta sannan da danna mai Kira. Karar waya neh ya katsesu,hannu yasa a aljihun jallabiyan shi sannan yaciro waya ganin Ammi neh take kira yasa yayi saurin dauka cos gabadaya yamanta da mah sun iso gida. “Ammi gamu nan mun kusa iso…*Meeting his family* “Ammi gamu nan mun kusa isowa mah” sanda Ammi takalli wayar sannan ta kalli inda yake tsaye kafin tasake miyarda kallon ta kan wayan kafin takara fadin. “Kai banson shashashan ci fah” “Ammi dagaske munkusa isowa”yafada a shagwabe “Turn around and see something” Ammi tafada Juyawan dazai yi idonshi ya shiga cikin na Ammi, sakin Zuly yayi yafara waige waige ai kuwa nan yatuna ashe har sun iso gida wani mugun kunya yaji ya shige shi. Dariyar da Zuly keyine ya miyarda hankalin shi kanta “Mun kusa isowa mah” tafada cikeda tsokana tana barin wajen Shafa kanshi yayi sannan yace”in na kama ki kou??,ai naga duka laifin ki neh dakika mantar dani inda nake” “Babu wanin nan”tafada daidai ta iso wajen Ammi,bude mata hannu Ammi tayi alaman runguma aikuwa bah bata lokaci ta rungumeta. Cikeda murna Ammi tace”yau dai nakalli Zulyn Mourad azahiri” Batareda tayi magana bah ta sunkuyar da kanta kasa,ganin yanda tayi bakaramin dadi Ammi taji bah, aranta tace” lallai Mourad ya iya zabi” “Ina wuni Ammi??”tafada cikin sune kai “Lfy lau Zulyn Mourad”ta amsa mata cikin farinciki “Ammi nah yau kuma an manta dani neh”ya katse mata tunanin ta tareda riko hannunta “Dallah sake ni bayan kai ma kamanta dani”tafada looking serious “Kai Kai na isa in manta da Ammi nah neh?, kullum kina raina yau dinma dai Zulynah neh tadauke min hankali”yafada yana riko hannunta tareda yin hanyan cikin gida daita while ita dinma hannun Zuly neh rike da dayan nata. Suna shiga cikin gidan wata kamshi mai gusar da tunanin mutum ya ziyarci hancin su. “I love this scent”shine abinda Zuly tafada batareda tasan tayi magana bah. Murmushi kurun Ammi tayi sannan tace”you guys should come and eat lunch,kafin lokacin sallah yayi” “Ohk Ammi” yafada tareda heading towards the dinning room. Fadin girman dining room din bata lokaci neh,iya haduwa kuwa dinning dinnan ya hadu. Dining table din shake yake da abinci kala kala cikin expensive beautiful coolers “Ammi inasu Fakihah??” Zuly tafada cikin nutsuwa Sosai Ammi taji dadin tambayan,zatayi magana kenan sukaji magana abakin kofa ,dayake basu riga sun zauna bah tukunna yasa suka juya gabadayan su. Wasu kyawawan larabawa guda uku neh suka shigo,mata biyu Sai namiji daya sanye cikin shigan alfarma amma saidai na daya daga cikin matan yazarta nadayan kuma ita harda make up fuskarta. Cikin tsananin farinciki Fakihah tarungume Zuly tareda fadin “Barkanki dazuwa Zulyn Mourad” “Nagode” tafada cikin murmushi Wajen Mourad sauran biyun suka nufa,itadai tasan Fakih amma batasan fuskar dayan matashiyan bah “Kun iso lafiya bro” Fakih yafada tareda runguman Mourad,murmushi kawai Mourad yayi Sai ta tsinkayo muryan matashiyar tana fadin “My sweet Sannu da dawowa”wani irin abu Zuly taji yatsaya mata arai kwakwalwar ta sai son nemo ma’anar sweet takeyi,nan da nan annurin fuskanta yafara raguwa cikin dauriya tace “Fakih bah magana neh” Kallon ta yayi cikin yatsine cos ko kadan baison *TARAYYA*n Zuly da yayanshi yafison Siyah , cikeda gadara yace daman nikike jiran nafara miki magana??” Ga bakidaya basuji dadin yanda ya mata magana bah itadin mah Zuly sanda taji wani iri. Cikin bacin rai Mourad yace”wannan wani irin magana neh Fakih??” Ganin yadauki maganan da zafi yasa Zuly cewa”kai yay Mou dina ai wannan bah abin bacin rai bane,he’s right nine yakamata nafara gaishe shi amma Sai nayi shiru,don’t blame him am the one to be blamed”. Sosai abinda Zuly tayi ya burge Ammi cos tasan soboda Zuly bata son ya’yan ta creating rift atsakanin su shiyasa tafadi hakan amma hakikanin gaskiya abinda Fakih yayi baimawa Ammi sugar bah. “Nasameku lafiya “tafada tana mai kallon su. Kaman baison magana yace”lafiya” Gefenta Mourad yatako tareda kama hannunta zuwa wajen dining chairs din, jawo guda daya yayi sannan yazaunar daita akai. Cikin murmushi tace”thank you yay Mou dina” kumatunta yaja kafin yace “You’re always welcome Zulynah” sannan shima yazauna a gefenta. Wani irin kululun bakin ciki da kishi ne yaziyarce zuciyar Siyah,ace akan yar wannan abun Mourad dinta ke hauka, wannan abun!!!? Sosai abin kecin zuciyar ta. Kwallan dasuka taru a idonta tayi saurin miyarwa gudun kar a gani amma ta makaro domin akan idon Fakih kwallan suka taru. Cikeda tausayin ta yakarasa gefenta tareda riko hannunta, jin an rike mata hannu yasata kirkiran murmushi. Janta yayi har kan chair din sannan ya zaunar daita,alokacin kuma su Ammi ma har sun zauna. Serving dinsu wata yar aiki keyi cikin kwarewa,sanda taiso kan Zuly,cewa tayi takawo. Tana bata ta dibi wanda zai musu a plate daya,su dai kallon ta sukeyi cos azaton su ita kadai zata ci nan kuwa basu san mudun in cin abinci ya kamasu awani waje toh tabbas a plate daya zasuci(inda kaga sun raba plate toh atabbatar basu tare ne). Tana gama zubawa tasa spoon biyu acikin plate din sannan ta tsiyaye ruwan su a cup daya,juice mah a cup daya daban(inkaga sun raba cup toh a restaurant neh,ko kuma haka aka basu) Su Ammi kam mamaki neh yacika su barinma Siyah da Fakih,Fakihah kam babu ruwan ta cos salon soyayyan su bakaramin burge ta yayi bah.(nace bakima ga komai bah tukun) Ahankali suke cin abinci su, jefi jefi kuma suna hada ido da Siyah take banka mata harara, abin bakaramin mamaki yake bata bah amma haka tashare. Kwarewan da Zuly tayine dalilin maganan datakeson mishi ne yasashi tsurewa,ruwa ya bata amma still bata daina bah aikuwa ya rude,wani ruwan yasake bata tareda shafa gadon bayanta gabadaya idonshi Sai yayi Jah(nace ikon itada kwarewa kai da shan wahala) “Inace na hanaki magana inkina cin abinci??”yafada cikin hade fuska cos baiji dadi kwarewan ta bah “Am sorry”tafada cikin sanyin murya Ganin yanda ta marairaice fuska yasashi rungumeta tsam ajikinshi”karki sake” Taji yafada”InshaAllah”tafada tana breaking hug dinsu. “Sannu” Ammi da Fakihah suka fada Gyada kanta kurun tayi cos sosai take jin kunyar Ammi. Iyanxu kam har Siyah tafara share hawaye aboye Sai kuma tayi danasanin zuwanta cos wanda tazo domin sa mah bai wani kulata bah,kila ma ya manta daita azaune(nace sannu😓). Hamdala Ammi tayi tareda tashi sannan tace” nikam nashige ciki,saika nuna mata dakinta”. “Ohk Ammi”yafada cikin girmamawa,daman suma sungama saikawai suka tashi aka bar Siyah da Fakih. Riko hannunta yayi cikeda tausayin ta sannan yace”namiki Alkawari wlhy Sai yayana ya aureki(🙆🙆 akwai matsala fah…hmm) Cikeda murna

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 4