in

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 2

gareta yana fadin”go ahead zulynah” Jan hannunshi tayi zuwa wajen wani tsadadden*poltrona frau kannedee curved sofa* white colour cos gabadaya colourn wajen white neh,zaunar dashi tayi akan kujera while tamawa kanta masauki akan *silk ifashan rug* tareda tankwashe kafa kaman mai karban karatu sannan tasa hannayenta ta dafa kumatunta dashi, shidai ido kawai ya zuba mata… “Yay Mou dina gudumawar miye zaka bani a aurena??” Wani irin dariya yayi sannan yace”tin yanzu??” Pouting bakinta tayi sannan tace “kawai dai inaji ajikina nakusa aurene shiyasa” Zaro ido yayi yace “like seriously” Gyada kanta tayi tana saukar da kwayar idonta akanshi, murmushi mai sauti yayi sannan yayi gyaran muryan dayasa ta miyarda idonta kanshi Ajiyar zuciya yayi sannan yace”na dauki nauyin kayan dakinki” “Wow yay Mou dina I love it…” “One more thing”yafada,shiru tayi Sai ya cigaba” nida kaina zankaiki dakina babu wani gayya…” Katseshi tayi da fadin “dakinka kuma??” Tareda rike habarta Zaro ido yayi yace”toh in banda abinki ai dakina dakinki neh so dakinki dakina neh ai…” Sosa kanta tayi sannan tayi dariya tace”kuma haka ne fah yay Mou” Dariya dukkansu sukasa kafin tace “sauran abu guda daya” “Toh zulynah miye ne kuma??” Sunkuyarda kanta sannan tace”inason kai zaka zamo waliyyi nah” Wani irin tari neh yasarke shi ai kuwa yafara yi babu kakautawa arikice tayi cikin fridge din wajen tadauko ruwa, tsantsan rudewa mah tamanta dayanda ake budewa,nan kuwa tafara kokuwa da gora dataga babu kanta Sai ta yar da goran tayi wajen water dispenser din wajen,acikin disposable cup ta taro ruwan sannan tazo tafara bashi alokacin kuwa har hawaye yafara wanke mata fuska… Sanda yasamu nutsuwa tukun yadawo da kallon shi kanta , idonshi sunyi mugun Jah,goge mata hawayen fuskanta yayi sannan yatashi tsaye cos yasan in har yacigaba da tsayawa awajen to tabbas saidai afitar da gawanshi… “Sannu yay Mou dina”tafada for the tenth times tana rike hannunshi,gyada kanshi kawai yayi “Muje inbaka magani”tafada tana Jan hannunshi(nace toh yaushe Zulfa tadawo likita bansanibah??) “No zulynah gida Zan koma”yafada ahankali “Harka gaji da ganina neh yay Mou??” Ganin yanda tayi fuskarta yasashi jin tausayin ta,lumshe idonshi yayi sannan yace”ai banki mu dawwama ahaka bah, banjin akwai randa Zan gaji dake arayuwa ta kokuma kin manta matsayin ki azuciyata neh” Girgiza kanta tayi tana murmushi sannan tace”toh karka tafi” Cikin serious face yace”inkinsan zaki tuka min tuwo toh Zan zauna”(kowani abinci ta iya amma banda tuka tuwo…hhh) Nan da nan tafara ja da baya tana fadin”bari na nade maka hoton budurwan ka sai kabi asamaka ita a frame” Murmushi yayi aranshi yana yace”sakaliya kawai” Nade mishi tayi sannan tace”in kazo gobe inason muyi magana” Wani irin dum yaji azuciyar shi amma ya maze yace”ina fatan bah shirme zaki fada min bah” Dariya tayi sannan tace”this time around zakasha mamaki na ” “Allah yasa” yafada tareda ficewa daga dakin… ★★★★★★★★ *Brookfield Center for lifestyle Medicine,8misratah street WUSE 2 Abuja, Nigeria* Kwance take drip ahannunta banda kuka babu abinda takeyi she can’t believe ace yanxu Wannan cikin datake bala’in so yanzu babu shi… Shigowan Umaiza da flask din ruwa neh yasata runtsa idonta ko kadan batason ganin Umaiza din cos gabadaya laifin kanta ta aza… “Anty dazu Alhaji yakira kina bacci,shine nace nakira miki shi ne yanzu kokuma??”Umaiza tafada “Ki Kira min nurse”tafada batareda ta kalleta bah Itama batayi magana bah tafita… Chan saigata tareda nurse sun iso “Sannu madam”nurse tafada ayatsine “Yauwa so nake kiringa Kula dani cos bana bukatar wannan mayyar anan” Afirgice Umaiza ke kallon ta tana mamakin karfin Hali irin na Yusayrah “Bangane mayya bah? mayya ce wannan din??” Nurse din ta tambaya cikin tsoro “Erh mana ita ta yoyemin ciki” Yusayrah tafada batareda shakkan komai bah, zaro ido Umaiza cikin tsananin firgici jin sharrin da yusayrah ke kala mata… “What!!”shine abinda nurse tafada tareda ficewa dagudu,chan saigata tadawo da police guda 3… “Ke kifita daga cikin hospital din nan peacefully kokuma mufitar dake da karfi…” Hawaye taji yasauko mata sannan tace”wlhy ni bah mayya bace, duk familyn mu mah babu mayu…” Kafin ta hankara sunfara ingizata waje nan da nan jama’u suka fara taruwa ana neman ba’asi nan kuwa nurse tafara Koro musu bayani nan da nan aka mata caa akai… Shooting dinta akayi dawaya kotaina while ita banda kuka babu abinda takeyi numfashinta har sama sama yakeyi tsantsan tashin hankali ita ko amafarki bata taba tinanin za’a kirata da mayya bah… Har waje aka raka ta suna mai tir da halinta, gudu gudu sauri sauri tadinga tafiya hartayi nisa amma har lokacin kuka takeyi… Da kafa taka zuwa gidansu dayake daga gidan zuwa asibiti babu wani nisa sosai,maigadi na ganin ta yafara washare baki soboda sosai suke dasawa dashi cos Umaiza bata da matsala kowa nata neh,tanada kirki sosai… Abin mamaki yau mutumiyar tashi ko Kula shi batayi bah tayi shigewarta cikin gida,jikinshi yayi sanyi cos daga gani kuka tayi soboda Jan da fuskarta yayi… Tana shiga cikin gidan tayi zaman dabbas akasa tareda sakin kuka maicin rai,sanda tayi mai isarta sannan ta dauki wayarta tadanna wa Iqbal Kira, bugu daya biyu yadauka… Jin andauka kiran yasata kara fashewa da kuka nan da nan hankalin Iqbal yatashi sosai cos azatonshi wani abu neh yakara samun Yusayrahn shi atsawace yace
“Zakiyi shiru kifadamin abinda yafaru ne kokuwa??” Cikin ajiyar zuciya tace”Anty neh takala min sharri wai ni na shanye mata ciki…” “Alhmdllh”shine abinda Iqbal ya…

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 11 KARSHE

ZULFA CHAPTER 3