in

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 2

tareda lakutan hancin ta yana fadin”nayi kewarki sosai Zulynah” Jan hannunshi tayi tareda fadin” inada abinda nake son nuna maka” “yau kuma?” “Erh mana…” Cikin gidan suka koma sannan suka aura sama wani part din dake chan karshe suka nufa, ma’aikaciyar wajen tagaishe su tareda bude musu kofa… Gabaki daya wajen duhu ne ko hannunka baka gani balle azo kan abubuwan da suke cikin wajen, cikin wajen suka karasa shiga while shi yana mamakin ina ne wajen… Rufe kofan da akayi ne yasa haske gaurayawa cikin dakin “Wow” shine abinda Mourad yafada lokacin da idonshi yahango mishi *gallery arts (paintings)* din wajen cikin wajen Wanda sunfi dubu, garun wajen ma abin kallo ne cos duk paintings dinta neh amakale awajen … Cikin mamaki yake fadin” zulynah yaushe kikayi wa’inan ayyukan da ban sanda su bah” Murmushi tayi sannan tace”tin randa gidan nan yazamo mallakina nafara kenan 4yrs back” “You mean acikin 4yrs kikayi duka wannan?” Yatambaye ta still da mamaki akan fuskarshi Janshi tayi tace”Erh mana, zo na nuna maka wasu kuma” “Still?” “Erh mana” Wani katon frame tacire daga jikin garu wanda sanda yataya ta,nan kofa ya bayyana, bude kofar tayi shima duhu neh sannan tace”rufe idonka” Dariya yayi yace”yanxu kuma??” “Please”ta fada cikin shagwaba “Ohk” yafada “Karufe kuwa??” “Erh” “Sure??” “Yeah” Kunna Wuta tayi sannan tace “open your eyes” Ahankali yake bude idonshi har yasauke shi cak akan wani katon framework dinta, rufe idonshi yayi yasake budewa fess kuma akan wannan hoton… Takawa yakeyi har ya isa gaban framework din zuciyar shi cike da mamaki cos wannan shine biggest surprise din rayuwarshi SAKAMAKOn ganin hoton shi ajikin frame din tsaye agefen ruwa na beach dagashi Sai gajeren wando, towel zagaye da wuyar shi ga six packs dinshi nan abin sha’awa kirjinsu kuwa gashi ne kwance kai bama zallan kirjin shi bah gabadaya jikinshi,gashin kanshi kuwa kaman na mata sanadiyar ruwan da ya zuba akai, hannunshi kuwa rikeda*RUWA*drink dayafi kowani drink tsada aduniya cos goran shi ma da Diamond akayi shi murfin goran kuma da Gold akayi shi ,juyawa yayi gareta inda Sai faman blushing takeyi ahankali tace “You like it??” Maimakon ya amsa saiyace” yaushe Kika taba gani na ahaka?” Soboda shi yasan rabonshi da irin wa’inan wanjen tin kafin ya hadu da Zulfa ,kuma a saninshi bata taba ganinshi babu riga bah amma how comes tazana sak shi cos hatta tattoo dinshi na yen gayun dayayi mai suffar Z a Samar kirjin shi akwai kuma babu abinda ta rage… Murmushi mai sauti tasake sannan tace” na taba ganinka babu kaya sau daya ranar dana zo gidan ka shiyasa nayi imagining dinka a irin wannan wajen kuma nasan *Ruwa* neh drink dinda kake sha… “So blessed and talented” shine abinda yafada azuciyar shi kafin ya tsinkayo muryan ta tana fadin “Kodai bai maka kyau bane??” “Yayi min kyau sosai kuma I love it kaman yanda nakeson wanda tazana” Dariyar jin dadi tayi sannan tace nasan zaka so shi shiyasa nayi kuma guda biyu nayi, wannan zaka tafi dashi dayan kuma adakina yake… Cikin mamaki yake kallon ta ga wani farincikin dayake ji yana ratsa shi “Ke ina hoton ki??”ta tsinkayo muryan shi yana tambayan ta “Banyi bah”tafada tana karasawa wajen hoton tareda shafawa,shidai ido kawai ya zuba mata “Duk lokacin dana kyalla ido na akan wannan wlhy wani irin farinciki na daban nakejin kaina ” tafada tana saka fuskarta akan hoton “Nima kizo kiza na min budurwa na wanda zanna gani ina farinciki” Cakk ta tsaya sanadiyar jin abinda yafada,wani abu taji ya tsaya mata amakoshinta,ga zafinda kirjinta ya dauka lokaci daya,muryanshi ta sakeji yace “Ko bakison na kasance cikin farinciki neh??” “Ka kaita studio Azana ta” tafada cikin dauriya “Yanxu zulynah gaki nan amma Sai na bata kudina?”yafada cikin sanyin murya Jin yanda yayi magana yasata fadin”toh ina take nazana” Murmushi yayi yace” wani irin ina take bayan you are so talented, kin iya imagination mai kyau, suffarta kawai Zan fada miki saiki mun ita” Wani guri yaga tanufa tareda daukan abubuwan da zatayi zanen dasu harda katuwar drawing board duk ranta ya jagule… Wani bakin kyalle ta dauko ta kulle idonta bayan ta ajiye komai Cikin mamaki yace”miye kuma na wani rufe ido” Batareda tasan abinda tafada bah tace”soboda bana kaunar ganinta” “Kinsan wacece kuwa??”ya tambaya “Koma wacece ban bukatan ganinta” Dariya mara sauti yadinga yi jin yanda take amsawa gefe daya kuma farinciki neh fal sbd kishinshi dayagani atareda ita… “Kayi sauri ka fadin yanda suffarta take” takatse shi, nan yadinga kwararo bayani amma kishin dake cinta yakasa bari tagane suffarta yake karantowa,cikin abinda baifi minti 10 bah takarasa zanen… *Bude idonki din mana”yafada bayan tagama “So nakeyi ya bushe na nade maka” “Ai inkin bude mah zaki nade” “Ai cemaka nayi banason ganinta ko ana dole neh?” Tafada tareda fashewa da kukan da batasan dalilin shi bah ,juya bayanta tayi tareda cire kyallen sannan tayi cikin toilet tareda slamming din kofa… Kukanta bakaramin wargaza mishi tunani yakeyi bah,ahankali yakarasa kofar toilet din sannan yace”zulynah ki bude kofa Zan fada miki abu” “No ka tattara hoton katafi wajen masoyiyarka wanda inka gani kake farinciki”tafada cikin kuka “Yah Salam!!!” Yafada yanasa kanshi ajikin kofan toilet din cikin dauriya yace “Zo kiganta kosau daya zulynah” “Nifa nace ban kaunar ganinta” tana wargaza abubuwan cikin toilet din , tana jin zuciyar ta kaman ta yasar Da karfi yace”Ke ce F…..Witch*+ Da karfi yace”Ke ce fah”cakk kukanta yatsaya tana son tabbatar da abinda yafada, muryan shi tasake jin yace
“Wlhy kece” wani irin wawan bude kofa tayi wanda yasashi kusan faduwa kasa, cakk ta tsaya tana kallon hoton wanda bakowa bane aciki face ita kuma da shigar jikinta, tambayar kanta tafara yi wai shin ina tunanin ta dahar aka suffanta ta bata gane bah Daidaita tsayuwar shi yayi sannan yace”wlhy dana fadi da kema saina fadar dake” Juyowa tayi gareshi tana mai harde hannayeta biyu a kirji sannan ta turo baki kafin tace”miyesa baka ce nice bah??” Shima harde hannunshi yayi kaman yanda tayi sannan yace”toh miye amfanin fada din??”,nidai a nade min hoton budurwa ta nakama gabana, kar kishi yasa a yagamin don anga beautiful girl mai mulkan zuciya ta” Giran ta daya ta dage sannan tace “kaji min mutumin nan ance maka samarika na basu fita kyau bane da har zanyi kishi da wannan mummunan” Kalman mummunan da tafada bakaramin taba mai kirji yayi amma kalman samarika yafi tsaya mishi arai,afili yace “bangane samarika bah??” Cikeda rashin damuwa tace” erh mana daya ina mugun sonshi dayan kuma…” tasamu bakinta da yin shiru kuma atake wani kunya ya turnuketa,sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsarta… Har ya karaso gabanta bata sani bah sai jin hannunshi tayi yana dago habarta cikin danne duk abinda yake cikin ranshi yake Adduan Allah yasa karta karasa kalman dazai tarwatsa zuciyar shi awajen amma Sai yace” dayar fah??” Samun kanta tayi da girgiza kanta tareda fadin”hey cool down wasa nakeyi fah” Ajiyar zuciya mai karfi yasake tareda sake habarta sannan ya dafa saitin zuciyar shi yana dan runtsa ido… Ganin abinda yakeyi ne yasata zaro ido tace”yay Mou dina miye faru” Ganin yanda tazaro ido neh yasashi fashewa da dariya yana nuna ta da yatsa hade da yin baya … Kallon kanta takeyi daga sama tana neman abinda yake mawa dariya din ,ganin babu komai yasata matsawa gab dashi hade da buge kirjin shi tace “You scared the hell out of me and kana min dariya” rike hannunta yayi cos ayayin da take bugawa wani vibration yakeji awajen, controlling din dariyan shi yayi sannan yace”am sorry zulynah”, Sai asannan ta tsaya tana fadin “daman fah Zan tambaye ka abu neh” Tattara hankalinshi yayi

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 11 KARSHE

ZULFA CHAPTER 3