in

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 2

ZULFA CHAPTER 2

Miye yake nufi da hakan, kodai yayi zuciya ne dazai tafi batareda yabar min aika bah…” Cikin sanyin tabar wajen batareda ta Kula maganganun su bah…+ “Umma ina kwana” Mourad yafada “Lafiya lau Mourad din Zulynshi” Umma ta amsa mai “Daman Zan fada miki abu neh?” Tattara hankalinta tayi zuwa gareshi sannan tace”ina jinka” Cikeda jin kunya ya zayyano mata abinda yafaru daga farko har karshe,harda yen kwallan shi Umma kuwa mamaki ne yakamata jin babu abinda ya chanza amaganan lallai Sai yau tagama yarda da soyayyan da take hashashen Mourad yana mawa yarta, katse Umma yayi da cewa “Umma DanAllah kitayani rokonta tayi hakuri wlhy *nayi nadama* bazan sake bah sharrin shaidan ne” Numfasawa Umma tayi sannan tace” gaskiya abinda kukayi bai dace bah amma tinda kagane kura kuranka komai ya wuce, Allah yaraba mu da son zuciya” “Ameen Umma, ina zulynah take??” “Ta tafi makaranta yanzu nan, nazata mah kun hadu ahanya ne cos tana fita ko 10minutes bata yi bah ka iso” “Ya Salam, gashi nan da 20minute flight dina zai daga, gashi ba halin inyi shifting dinshi soboda emergency nake dashi”yafada kaman zaiyi kuka “Allah sarki”Umma tafada “Umma kidan taimaka min da littafi zan ajiye mata sako” tashi umma tayi sannan tashige ciki domin dauko paper… *5:20pm* Agajiye take taka matakala yen aiki sai gaishe ta sukeyi amma soboda damuwan da take dashi ko amsa musu batayi bah Dakin Umma ta nufa inda tasameta tana waya da alaman daga Nigeria ne, zaman jira tayi agefen ta… “Yar umma har an dawo kenan?” Umma ta tambaya bayan ta gama wayan ” Erh ummana , nasameki lafiya?” “Lafiya lau ga abinci nagama, zakici yanxu ne ko zaki fara wanka?” “Erh umma zan fara wanka
tukunna soboda gabadaya nagaji dayawa” “Yauwa yar umma,inkin gama mah akwai aikanki awaje na saiki xo ki karba” Murmushine ya subuce mata dukda bata san aikan miye bah amma tabbas zuciyarta yayi mata sanyi kuma tayi farinciki da hakan cikin dariya tace “umma na aikan miye neh?” Umma ma murmushi tayi sannan tace” ki bari saikin zo zaki gani” “Barina yi sauri nagama sainazo nagani tinda ummana taki fada min” tafada hade da barin dakin dasauri daman kuma an shige mata da jakanta cikin gida… Sanye take cikin Silk Floral Wrap Dress na companyn zimmermann black with peach touch colour kafanta kuwa sanye yake cikin black cashmere cadie slippers sai sauri take bugawa… Haryanzu murmushin dayake kwance akan fuskarta bai bace bah,cewa tayi”Umma gani nagama kibani aikan” Umma dake zaune ta ce ” yana daki na akan dressing mirror kije ki dauka” “Ohk” tafada hade da nufa dakin umma, idanunta suna sauka akan papern taja wata iriyar ajiyar zuciya, murmushin kan fuskarta na daduwa ahankali tayi tataki zuwa wajen sannan tadauka, ahankali takai papern kan hancin ta ai kamshin dataji ne yasata lumshe idanu hade da fashewa da dariya kaman wata mahaukaciya akan gadon umma tayi super aikuwa tadinga rolawa ga haryanxu tana dariya, daidaita kanta tayi sannan tazauna dakyau hade da bude papern ahankali,da kyakyawan rubutun shi tayi harba ita fah tana jin anace wa rubutun likitoci jagwal neh amma banda na Mourad dinta…
Ahankali tafara karantawa kaman haka “Life is all about the next step… Everyone makes mistake but life is all about a second chance… I request

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 11 KARSHE

ZULFA CHAPTER 3