in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 4

YARIMA ASHMAN CHAPTER 4

Jiki ba kwari suka nufi cikin kotun .
Yarima yakalli umma yace mama kije ganinan xuwa,to tace ta shiga cikin kotun.
Shikuwa yarima gun mota ya wuce yadauko rigarsu ta lauyoyi yasaka aisanaga ,haibarsa da kamalarsa had’e da kwarjinsa sunsake bayyanah.
“A cikin kotun kuwa kowa ya hallara alkali da barrister’s kawai ake jira.”
Kawu bala kuwa inbacin harara bbu abinda yake aikawa da Umma dan tunani yakefa kada allura ta tona galma.
Alk’aline yashigo kowa ya mik’e tsaye bayan ya zauna kowa yazauna.
Megabatarda da kara yagabatar had’e da tambayar lauyoyin masu kariya su fito.
“Cikin takun kasaita yarima yashigo sai kallonsa ake ” wani mugun kallon tsana da k’iyayya Kawu bala da alh jamilu suka aikama sa,sarai yagansu amma sai yanuna be gansuba dan tunda yashigo idanshi ke Kansu musammun alh jamilu dan besan balaba amma ganinsu tare yasa yagane balane.
Nan shima barrister saminu yazo yabaiyana agun.
Alkali da abukaci ganin umma gabanta,bbu musu ta fito alk’ali yyi mata tambayoyi akan abinda take kara nan ta sanar da shi kamar yadda yarima yafad’a mata.
Sannan aka bukaci Kawu bala yafito ,cikin fad’uwar gaba da muxurai bala yafito nan alkali yyi masa tambayoyi yana amsawa cikin inda inda.shikanshi alk’alin yalura bbu gsky atare da bala.
“Yarima kuwa sai murmushi ykeyi yana cewa good”.
Bayan alkali yagama yiwa bala tambaya ,yabukaci ganin alhj jamilu.
Bayan ya fito alk’ali yakallesa yace Kaine Wanda bala yabawa auren diyar k’aninsa ? Alh jamilu yace eh!
Alk’aliyace kuntab’a magana da yarinyar kunsan juna?yace ah ah ,alk’ali yace yaje ya xauna.
Bayan yyi yan rubuce rubuce yace lauyoyin masu kariya ko kunada tambayoyin dazakuyi?
” da sauri yarima yad’an rusuna yace akwai yahmai girma mai shari’a ,alk’ali yace kotu tabaka dama barrister.
Nan yarima yace inason ganin bala agaban kotu.
Nan Kawu bala yafito kamar zaiyi xawo sbd yadda yatsorata ainun lol..
Yarima yakallesa yace inason kagabartawa da kotu sunanka da matsayinka agun yarinyarda zaka aurawa alh jamilu bacin kasan yarinyar bata sons….upjection my lord barrister saminu yakatse yarima had’e da cewa, yah mai girma mai sharia yakamata lauyan mai kariya yasan abinda zai rik’a tambaya sbd koba komai ai yarinyar diyar k’aninsa sace kuma yana da iko akanta tunda mahaifinta baya Raye…alk’ali yace k’orafi be karb’uba barrister ,dole ya amsa wannan tambayar.
Wani murmushin mugunta yarima yyiwa barrister saminu.
“Kawu bala cikin in,ina yasanar da kotu sunansa da matsayinsa gun yasmeen.”
Yarima yace bayan rasuwar k’aninka wane taimako ko kulawa kabawa wannan bewar ALLAH da y’ayanta?eh…nah ..ban ..banida haline shiya sa.
Yarima yace sadda alhj jamilu yazo Neman auranta gunka kayi shawara da mahaifiyar yarinyar kafin ka amince?ah ah banyiba.
Yarima yace good ,to amatsayinka na Wanda besan cinsu,shansu,iliminsu ,tufafinsu,farat d’aya sai kace dole sai yarinyar tamaka biyayya ta auri Wanda bata so….da sauri barrister saminu yace up jection my lord yakamata lauyan me kariya yadena jifar Wanda ake tambaya da laifi kokuma ko kuma d’ora masa laifin dabai aikata ,koba komai ai sai inyanada halin taimaka musu zai tammaka musu..
Al’kali yace barrister akiyaye.”kwafa yarima yyi yabukaci ganin alh jamilu nan yafito, yarima yabuk’aci yyiwa kotu bayani wanene shi? Nan yagabatar da kansa ,yarima yakallesa yace Kaine Wanda bala yabawa auren diyar k’aninsa? Yace eh yace to yanxun kun hadu da yarinyar kunyi mgn yace ah ah.yarima yakalli alk’ali yace yamai girma mai shari’a da waddannan hujjoji nike so wannan kotu me adalci tabiwa Mariya da yarta hakkinsu gun hana Wannan auren da bala kawunta yabawa Wanda bataso ,yin auren zai iyasa Rayuwar yarinyar tagaiyara,yanxun haka Tana karatune dan taimakon kanta kasancewarta marainiya ,inason kotu tahana bala koda yawan xuwan dayakeyi gidan Mariya sbd yana daga mata hankali ita da yaranta na gode yamai girma mai shari’a..

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 3

YARIMA ASHMAN CHAPTER 5