in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 14 KARSHE

YARIMA ASHMAN CHAPTER 14 KARSHE

Shekaru goma sha Tara dasuka wuce…
Alh ismai’l ne wato mahaifin yarima alokacin yana magajin gari bezama Sarki ba,yana rik’e da hannun yarima Wanda alokacin yana dan 14years .
Bayan sun fito dg mota ,yyinda dogarawa nagun motar suna jiransu.
Cikin asibitin suka shiga suna tafiya suna fira a hanya ,office din wani Dr suka nufa abokin abban yarima ne yazo suyi wata shawara gameda rashin lafiyar dayake fama da ita….suna shiga office din suka sami jaririya kwance kan gadon da’ake duba marasa lfy”,ai da sauri yarima yanufi gunta yana murmushi yad’auketa had’e da kissing nata…. Abban sa kuwa cikin mamakinsa yake kallonsa har yazauna suka gaisa da Dr din ,suka cigaba da mgn yyinda yarima hankalinsa naga babyn wato yasmeen (alokacin tana jaririya)Abbansa yakallesa yace oh my son bazako zo Ku gaisaba?” dg zuwa said’aukar y’ar mutane kadafa ka kadamusu y’a…murmushi Dr yyi yace oh wannan baby ,yanxun mahaifinta yaje yakarbo allura za’ayimata ta BCG dayake sabuwar haihuwace shine yabarta nan yaje yakarbo allura yadawo in anmata yakaita gun mamanta tana can bin layin ganin likita..yarima ne yakatsesa da cewa pls uncle kubani ita natafi d ita gidammu,murmushi abbansa d Dr sukayi kafin suyi mgn ,baban yasmeen yashigo d sallama abakinsa.”
bayan sun amsa yagaida abban yarima cikin girmamawa kasan cewar yasan shine magajin gari…Dr yadubi yarima dketa ma yasmeen wasa yace to ga abbanta nan saika tambayesa inzai baka ita..da sauri yarima yakallesa yana murmushi yagaidashi,ya amsa cike d kulawa had’e da cewa Ashe yasmeen ta sami wani yayan bacin yayanta Omar?”kai duke yarima yace pls kabani ita natafi da ita gidanmu gun ammina!murmushi yyi had’e da dafa kafadarsa yace kayi hkru kaga jaririyace batafi wata2 ba in anyayeta zan kamaka ita har gdnku kaji ….mika masa ita yarima yyi had’e da cewa to kayi alkawari ko?”abbansane yace oh haka kake dama?”aiyace zaikama ita bashikenan ba muje gd …shiru yyi abban yasmeen dai baiyi mgn ba yamik’awa Dr ita dan ayi mata allura ,shikuwa abban yarima hannu yaba mahaifin yasmeen sukayi sallama had’e da sakamasa kud’i wai na yasmeen ne da yak’i karb’asaida Dr yasa baki tukum yakarb’a yyi godiya… shikuwa yarima saida yaje yasake kallon yasmeen tukum yataho had’e da cewa abbanta saika kamun ita,murmushi yyi yace insha ALLAH yasmeen batada miji sai kai…..nan abbansa yace ALLAH yasa sukayi sallama suka tafi….
Ajiyar zuciya yarima yyi a fili yace oh ALLAHU Akbar wato ubangiji ya amsa ,tabbas tunda naga photo na abbanki nasan duk inda nasan shi nasansa,yafad’a had’e da kallon yasmeen…
Cikin rashin fahimta tace oh sai surutu kke kai d’aya kayimun bayani dan infahimta ni yanxun ban gane ina kadosaba?”murmushi yyi yace my Princess wlh kuna kama da yarinyarnan sak kamanninkine tun kina jaririya! Turo baki tayi tace hmmm ni kasanni ne da ina jaririya ne?”ahankali yalabarta mata sadda yaganta a asibiti..murmushi tayi tace oh ikon ALLAH Ashe yan ameen sun karba….kafin yace wani abu ammi ta shigo dakin, tana ganinsa tayi salati had’e da cewa wato kana nan bazaka barta ta hutaba ko ?”to maza ka tashi katafi kafin ran…yasmeen ta katseta da cewa ayya ammi muna sallama ne shiyasa…da sauri yarima yace eh wlh,baki bude ammi ke kallinsu dak’k’uwa tayimusu had’e da kora yarima ,sannan tagyrawa yaran kwanciya had’e cewa yasmeen yanxun zata turo jakkadiya tazo ta kwanadasu ,bata jira amsartaba ta fita…
Yasmeen kuwa kwanciya tayi tana tuna labarin da yarima yabata ,azuciyarta tace oh dama Ashe tun tana jinjirarta yarima ke k’aunarta ,wani irin son mijinta da k’aunarsa suka sake dabaibayeta ako ina nan jikinta ,lallai ta yarda aurensu had’in ALLAH ne gashi har sun fara da haihuwa d’aya yara2 oh to wama yasan iyakar zuriarsu?”sai ALLAH da wannan tunanin bacci yyi gaba da ita.,,,,,
*** **** ****
Washe gari misalin karfe 7:am yasmeen ta farka da adduar tashi dg bacci abakinta ,bude idonta tayi taga jakkadiya nawa macen wanka ,inna atika nayiwa namijin shafa…mamaki take yaushe inna atika ta zo?”muryar ta taji tana cewa yasmeen kintashi?” nan tace eh inna ina kwana?”bayan sun gaisa tace to tashi muje namiki wanka kinji,bbu musu ta tashi ta cire kaya ,nan akace tabasu nono za’a kaisu fada gun maimartaba yagansu…
Bayan ta shayar dasune,suka shige toilet inna atika tayimata wanka sosai ta gasheta ,yasmeen kuwa yaji dad’in jikinta saidaifa taji zafin ruwan zafin hakadai ta fito ta shirya ,sannan tayi break fast mai rai da lafiya..
“” bayan ta idan ne taduba wayarta taga miss call 126na yarima ne 3na yah Omar 3na umma ,umman takira suka gaisa ta tambayeta lafiya dai take ko?”tace eh nan tayita mata nasiha akan taruk’a nuna kawaici akan yaran,sannan banda musu d kowa sannan sukayi sallama nan takira yah Omar shima sukasha fira sannan sukayi sallama..””
Bata aje wayarba yarima yashigo d’akin da sallama fuska asake tashi tayi ta fad’a jikinsa tana kukan kissa da shagwaba”ahankali yace mmn baby lfy me aka miki?”fad’amun kinji tawan,cikin shagwaba tace ba inna atika ce tamun wanka da ruwa masu zafiba !had’e rai yyi yace oh dama wait dole wankan sao anmike?”nifa gsky banaso ayita kalleminke bbu kaya gsky !Amma zancewa ammi arik’a bari ruwan yaf’an sha iska tukum ayimiki kinji?”ahankali tace to yaya, zama sukayi suka gaisa yatambayeta kotana bukatar wani abu ?”tace ah ah ,yaran yatambaya tace suna gun maimartaba afada ,ahankali yace my Princess nakira naji shiru baki d’agaba lfy dai?”tace lfy lau yaya ina wanka alokacin…. Jakkadiya ce ta shigo da yaran Maryam d salim nabiye da ita wai sunxo suyi wasa da fira da yaransu…shidai yarima murmushi yyi ya karbesu yahad’a d yasmeen yacigaba damusu pics ,sai fara’a yake bakin nan yaki rufuwa,yyinda Maryam d salim keta lissafa budurin daza’ayi na suna ,saiga Anty hanan d twins dinta sun shigo..
Bayan sun gaisa ta musu barka ta karbi yaran twins d’inta kuwa sai murna suke suna surutu wai sunyi kanne dasu zasu tafi gidansu ….wayar yarima tayi ringing yad’aga ganin salis ne murmushi yyi yace ok had’e da datse kiran,yakalli yasmeen yace bars naje da yaran nan ga abokaina can part dinmu su gansu sai na maidosu!tace to nan hanan ta miko masa su ya karba adaidainan kubra ta shigo dakin, tana ihun murna tayi ya’ya koda taga yarima saitayi shiru dan tare da salis suke ya wuce can part dinsu yace ta nufo nan yasmeen tana nan,cikin kunya tagaidashi hade da masa barka murmushi yyi yace babies d’inki sunyi fushi dke sunxo duniya tun jiya sai yau kikazo ganinsu,ware ido kubra tayi tace all yaya ai yanxun bata baciba ina nan har ayi suna tare dasu ,murmushi yyi yace dakin kyauta ,nan yafice ta fada kan bed din suka rungume juna da yasmeen suna farin ciki ,nan suka cigaba da fira dasu hanan d Maryam da salim suna nan kuma saiga salma ta shigo bash ne yakawota yawuce part dinsu yarima dan yakirasa yace sunacan…
Bangaren su yarima kuwa ,suna can fira ta Barker shiga salis dan wasu dg cikin abokan bayan sun ga yaran tafiya sukayi,sukabarsu suda salis .
Salis yakalli yarima yace kai mutumin bbu sauki kowa yaga yaran nan yasan nakane sbd kamarku ,musammun nmjin ,kana bada himma gsky yafad’a hadeda yin dariyar shakiyanci…murmushi yarima yyi yace to yasan ranka ai indai wannan fanninne bana wasa da harka ,kai aigashi duk jarabar taka matar taka bbu ciki ko?”hararansa yyi yace hmm to bars kaji tana da ciki 2month dandai mu namu ba mai laulayi bane ,dan ranar da najefa kwallona araga aranar Muka sami Rabin baby…
Cikin tsokana yarima yace hmmm kayi kokari dan duk yadda nike ganin inada fitina to wlh gara ni dakai ,kodayake ai gudunka tarukayi saida my Princess ta tsorata ta dazaka mata kishiya sannan taba da kai bori yahau,murmushi salis yyi yace eh naji ai dan tanasona ne shiyasa tayi kishina Ashe haka akayi?”yarima yace eh mana hade da labartamasa komai …
Suna haka su mukhtar da wani kamal abokansu sukazo ganin babies bbu jimawa bash yashigo shima ,nan sukayi ta fira basu maida babies dinba saida ammi ta kirasa tukum yamaidosu sbd jamaa nason ganinsu yan barka…
Yinin ranar yarima be fita ba yana gd shida abokansa suna tayasa murna ,abinci kuwa dg hotel akayi Oder, ana bawa jamaa,shima yarima Maryam ta kaimusu nasu shida tauwagar abokansa.
Hakafa aka cigaba da zaman jego gidan cike d mutane a kullum kubra kuwa saida tayi kwana anan sannan ta koma gdnta 2 washe gari tasake dawowa nan aka cigaba shire shiren suna dan su Maryam har anko akayi kuma a hotel za’ayi taron sunan ..
Ayaune aka kawo kayan yaji na babies d na uwarsu hmmm fadin yawan kayan ko tsadarsu bata lokaci ne ga harda gold dana babyn mace dana yasmeen ,dan Tsabar murna yasmeen bar kukan Dadi tayi yau ALLAH yashare mata hawayenta ta haihu kuma alokaci guda 2ta Haifa ta huta da gorin wasu dg dangin miji …
Yau Yakama Daren suna akuma yau d safe hjy babba ta sauka …
mmn fareesa ce✍🏻✍🏻AWESOME WRITER’S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer’s)
YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
Wannan page din nakine Aisha Aliyu kiyi yadda kikeso dashi ina mugun jidake irin sosai din nan😍😍
🅿113&114
“Yau Yakama Daren suna akuma yau da safe hjy babba ta sauka agidan sbd tun farkon haihuwar taso xuwa alhj tsoho yahana yace sai Daren suna washe garin suna ta dawo..

Yasmeen ce zaune ,ana Mata lalle da Kitso nasuna ,masha ALLAH wannan lalle yyi kyau over ,yyinda kuyanginta ke gefenta suna rik’e da babies d’in..
Lubna dke zaune kan kujera ta kalli yasmeen tace mmn babies ankawo kayan printing d’in?” Yasmeen tace eh “nan tace ok bara agama miki sai amun,sannan Maryam….bata rufe bakiba saiga Maryam d’in da salim sun shigo,kallonsu kubra tayi tace oh ikon ALLAH kaidai kazama na mata ko ina Maryam tayi kana manne…murmushi Maryam tayi tace ALLAH Sarki my salim bacci kawai ke rabamu dashi gsky Anty lubna kinsaka masa ido..yar dariya yasmeen tayi tace hmmm inkinyi aure ai dole yahakura…sallamar hjy babba ta katsemusu fira ,sai yan harare harare take tasamu guri ta zauna nan suka gaisheta ta amsa hade da cewa amiko mata baby boy din nbu musu akabatashi taita kallo nan lubna tace hjy badoshi kidauki macen…wani mugun kallo tayiwa lubna tace ke wacece ne dazaki gayamun San ranki?” Yasmeen azuciyarta tace oh lubna kintab’o jaraba”da sauri maryam tace yi hkuri hjy mstar abokin yah ashmance kuma batasankiba…tsaki tayi tace to dg yau aita sanni ,itadai kubra bata k’ara mgn ba …ana cikin hakan yarima yyi sallama cikin takunsa na k’asaita yasha askin suna da guaran fuska yyi masifar kyau wani lallausan boyel ne milk ajikinsa sabo fir sai kamshi yake dalagansa kaga angon jego,kai tsaye gun yasmeen yanufa kuma cikin sa’a angama mata ,fuskarsa asake be amsa gaisuwar da kuyangin kemasaba yadai daga musu hannu ya tsugun na gefen yasmeen hade da rike mata hannu d’aya yace wow my Princess kunshin nan yamun kyau gsky,murmushi tayi tace ALLAH nawan?”yace eh mana amma zanbasu kyauta ta mu…..salatin d hjy babba ta yi ne
yasashi yin shiru dan sai yanxun yasan tazo shibema lura da ita ba azuciyarsa yace to ga fitinanna kawai,jiyayi tace gsky bakuda kunya kota miyan bacci ,ace agabanmu kuma tana jego kake tab’ata to wlh zansaka da anyi suna amaidata gd yo wannan ai kafin tayi 40kasakeyi mata wani cikin ta fada hade da tashi tsaye ….yyinda kubra tayi shiru tana mamakin mita da jarabar wannan tsohu wa tana shiga inda ba huruminta…

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 13

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 1