in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

masoya..azuciyar Maryam tace hmmmm nima haka zanyi wa yah Omar dina …yarimane yyi musu mgn had’e da cewa su aje su tafi,yasmeen tarada masa akunne ita um um yabarsu ,yaje yyi wanka yacanxa kaya, tukum inyadawo sa tafi..
$suna niyar tafiya yarima yatsidasu,suka dawo,tashi yasmeen tayi dg jikin sa ta bud’e koolas din,lumshe ido tayi ganin wannan tuwon,wani son ammi d kaunarta taji yasake shigarta..
“Kallonsa Maryam tayi ,tace gsky ammi nah tanaji dani,dariyasukayi suka gaida ita had’e da tambayar babyn su,tace yana lfy,nan suka fara firar yadda bath din Maryam xaikasance dazasuyi jibi…shikuwa yarima ciki yawuce dan shiryawa.”
Agogone yyi kara alamar 12:00daidai,alokacin kuma hanan d twins sukashigo parlourn, da ihun murna suka fada jikin yasmeen, salim kuwa hada rai yyi yace kai sarakan surutu kubi mana ita a hankali ba ita d’aya bace ,kada kufadawa babynmu..
Harararsa yasmeen tayi ,azuciyarta tanajin dad’in yadda dangin mijinta ke dokin cikin dke jikinta,ta ce ni karabu da su,zama hanan tayi tace ah ah Anty d gskiyarsa ai,bayan sun gaisa ,itama hanan sai murna take dan dama ammice ta sanar da ita, yayinda su twins sai surutu sukewa yasmeen had’e da tambayarta,wai zata haifi baby yazama kaninsu?”kuma zata basu baby ?”itadai murmushi take sukuwa su Maryam d salim nabasu amsa,ana haka yarima yashigo parlourn d gudu twins sukaje sukayi hugging dinsa suna dariya,sabarsu yyi yana juyi dasu ,yazo yazauna gefen yasmeen suka gaisa d hanan ,tayi masa murnar samun k’aruwar da yayi….
Nan yace mummyn twins ,dama kuwa zanje daa gidanki ,amma tunda kinso shikenan,dan murmushi tayi ta ce oh yaya tunda Anty yasmeen ta zo gidan nan bakasake xuwa gidanaba!murmushi yyi yace zamuje nida ita ko my Princess, yasmeen tayi y’ar dariya yace eh harma kigaji dmu,dariya akayi baki daya….
Yarima yatashi yashiga ,ciki bbu jimawa yadawo da keys din mota yabawa hanan kyauta halak malak dinta,ihun murna tayi kamar wata yarinya tanata jin dad’i had’e da yimasa godiya dan dama tanason acanza mata mota,cikin murna ta nufi part din ammi..
Su Maryam ma suntayata marna,nan suma yabasu kudin da yayimusu alk’awari dan suje suyi shopping din kayan yin bath din..
Bayan duk sun fita ,yasmeen tayita masa godiya da addu ar sake samun bud’i adukiyarsa ,Wanda ba karamin dadi yarima yajiba ..
Rungume yyi ajikinsa ,yana shakar k’amshinta ,anan yake labarta mata yadda bash yashiryu da yadda sukayi da salma har ALLAH yakubutar dasu dg sharrinta..
Hamdala yasmeen tayi tace ALLAH yak’ara tsaremu,yace ameen..sageer ne yyi sallama yashigo parlourn dan dawowar kenan dg Dubai yahado lefe na bikinsa Wanda da tuni anyi(kiddinaping din yarima da akayi yasaka aka daga bikin)shine mama ta sanar dashi yasmeen Nada ciki yazo tayasu murna..
Sallama tyi yarima ya mike suka rungume juna,cikin farin ciki yah sageer yace oh yaya Ashe mun sami baby ?”
Murmushi yarima yyi ,kallon yasmeen yah sageer yyi datake gaisheshi ,ya amsa had’e da cewa maman baby ya baby nah yake? “Tace lfy “yace to ki kulamun dashi pls,itadai sunkuyadda kanta take ,yarimayajashi suka zauna yake tambayarsa saura sati nawa bikin ?”yace2,firarsu suke Wanda duk firar ta babyn daza ahaiface …wayar yah sageer tayi ring in bbu bata lokaci yadaga ganin sweetynshi ce,hans free yasaka wayar dan su yarima suji.
Taslim(wato amaryar sageer)tace my blood Ashe matar yah Ashman cikine da ita, murmushi yyi yace eh wlh ,cikin tayasu murna race gsky naji dadi kace inatasu murna ina gaida babynmu da mominsa….da sauri yasmeen dke murmushi race aiko gamu muna amsawa kuma babynki yace fushi yake dke saikinxo zai amsa gaisuwarki…da sauri taslim tace oh my blood Ashe kuna tare ?” Har naji kunya d’it yakashe kiran..
Murmushi yarima yyi ,Wanda har cikin ransa yanajin Dadi d farincikin ganin yadda danginsa ke nuna farin cikinsu akan gudan jininsa ALLAH dai yanuna musu ranar da yasmeen dinsa zata Haifa masa babyn sa ,ameen…
Kiran sallar azahar yasakasu mikewa suka wuce masjid…
***
Bangaren salma kuwa…
AWESOME WRITER’S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer’s)
YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story &written by mmn fareesa
Wannan page din nakune ,mmn fareesa fans page&awesome fans club kuyi yadda kukeso dashi kuna raina ina mugun jidaku over😍😍
Ina me bawa masoyana hkri aduk inda kuke na rashin jina kwana2inada uxurine nagode, masu zagi kuma na gode😂dan kunragemun xunubi kusani zagi ajinina yake be rageni sai kari ,grps na rufe bbu yadda kuka iya dani saidai zagin nan kadai….
🅿95&96
Bangaren salma kuwa jiki ba kwari, tashige motarta ta nufi gd.
Saidai maganganun da yarima yagaya mata suntsaya mata arai da kuma bash yabata mamaki dukda batasanshi amma Wanda yahadata dashi yasanarda ita dan iskane na karshe.”
Ashe kuma yashiryu ,ita haushinta daya maganganun da yarima yagaya mata agaban bash yak’ara xubda mata kima, lallai Ashe duk abinda mutum keyi ko mekyau ko marar kyau,zaibika ko bayan kabar abun nan..
“Jiki b k’wari ta iso gd ko abinci bataciba ana gama isha ‘I tayi bacci bbu yi salla, dan dama bayitakeba.” rabon datayi tama manta”
da misalin karfe 3:00am salmace sai juye take kan bed idonta arufe ,tayi sharkaf d zufa ,kuma g hawaye na zuba….xuwa can tafara ihu tana cewa wayyoooooooo!
ALLAH nabar lesbian ,bazan sakebaaaaaaaa!
Bude idanunta tayi ta tashi zaune ,sai zare ido take tayi bala’in tsorata, afilili tace oh ni salma meke shirin faruwa dani?sai takama hawaye had’e da cewa dama haka akema masu lasbian azaba d marasa yin sallah oh nashi ga ukkunaaaa!sai waige waige take da gudu ta fito tana ihu hade da kiran mommynta.”
Kicib’us sukayi d mommin da sauri ta fada jikin mommy ta na kuka mecin rai jikinta sai rawa da kirma yake”.
Itakuwa mommy cikin damuwa had’e da tsorata d ganin yadda ya’rta taburkice alokaci guda ,sai jijjigata take tana tambayarta lfy ?meke faruwane?”
Kuka kawai take taje mommy muje daki namiki bayani !ba musu ta bita har bed room ,bayan sun zauna cikin kuka ta sanar da mommy cewa tana lesbian kuma bata sallah…salati mommy ta yi, saikuma tafashe d kuka tace oh ni Habiba na cuci kaina nabatamuku tarbiya ta hanyar sangartaku kuyi yadda kukeso gashi kin lalace wai ko sallama bakyayi..
“” salma wacce kanta ke duke ,ta d’ago tana kuka tace yanxun nayi mafarki anamun azaba akabarina d macizai d kunamu ga duhu d zafi ga wasu irin hallittu nadaban ,kuma ana mun azaba d wuta sbd rashin yin sallah, wlh mommy na tuba nabi ALLAH nabiku..”
Ajiyar zuciya mommy ta yi tace to shikenan tunda kin shiryu kiyita istigifari ALLAHU GAFURUR RAHIM ne amma pls in daddy ki yadawo kada kisanar da shi kinji?tunda baya gari ”
“Tace to”
Mommy ta ce yanxun kije ki kwanta kafin asuba tayi,cikin tsoro tace ah ah mommy muje part din ki ,nan tabita sukaje…
Washe gari saida mommy ta koyawa salma alwalla d yadda ake sallah sbd ta manta.
,,,,acikin kwana biyun salma tayi bala’in yin sanyi ko mgn ba sosai takeyiba ,gashi tashiga islamiya ta matan aure anan anguwarsu burunta yanxun tayi aure bautar ubanjiji,sannan kozata fara aiki..koda daddynta yadawo shikanshi yaga canji atare da ita g islamiya tashiga Wanda yaji dad’in hakan sosai..
“Tun lokacin da salma ta shiryu ta dena amfani da layinta ta rufe dg baya kuma ta bude ta fidda number ta bash ,sannan ta karya layin tacanxa wani,saidai me ?tarasa dalilin dayasa ta cire number bash ta saka abason layinta.kuma take yawon tunasa….

** ** ** ** ** **
Su yasmeen kuwa sati biyu kenan da gane tanada ciki ,amma kullum gidan nan cike yake da jama a dangi da abokan arziki zuwa tayasu murnar samun wannan ciki.” baba mlm har gd ya aiko da rubutu ajarka yasmeen ta yi ta sha kullum safe da rana,da ya kare asanardashi yyi mata wani insha
ALLAH zata sauka lfy..
Uban gaiyar kuwa wato yarima saida yyi sati d’aya baya zuwa office yana lik’e da princess dinsa kuma mmn babyn sa,saida jama’a suka matsa tukum yakoma office sbdasu son ganinsa ko yataimaka musu.”
Suma su salim d Maryam bayan sun yi bath day dinsu ,ai nan part din yasmeen suka tare ana rainon babyn dasu ….ayanxun haka shire shiren bikin yah sageer ake wadda yau akeyin kamu gobe deenar ,kuma a gobe hjy babba zatazo taga yasmeen tazo biki….
“” yasmeen ce tsaye ,ta kalli agogon hannunta taga 11am saura minti15amma Maryam shiru batadawo tazo ta sanar da ita tazo ayi mata kunshi d kitson biki.”,,
Zama tayi gashi dama tanajin haushi yarima yyi mata wayo tayi bacci yyi tafiyarsa…k’arar bude k’ofar ne yasaka ta kallon me shigowa,maryamce, hararar ta yasmeen tayi tace shine Kika yi zamanki ko?”

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 11

YARIMA ASHMAN CHAPTER 13