in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

Murmushi mama tayi tace wlhy kuwa Omar kagansu nan haka suke matsamin nida amminsu da fitinarsu,amma ai basayi gaban yarima dan sunci gidansu…
Maryam data aje lemo tazuba acup ta mik’a wa yah Omar yasha,kadan ya ajiye gaban sa..
Mama tace kije kisaka ashiryomasa abinci….da sauri yace ah ah mama wlh alhmdllh na gode sosai, murmushi tayi tace hmm kunyadai kakeji Omar.
“Tashi yyi yace natafi ,mama godiya ta masa had’e da cewa yagaishe da Umma,yakalli Maryam tace kije kirakasa mana.,,,,
Fita tayi dan rakasa.
Mama tayi ajiyar zuciya dan har cikin rants tayaba da tarbiyyar Omar fatan ta shine ALLAH yasa alkhairi …
Bangaren su yasmeen kuwa…
AWESOME WRITER’S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer’s )
YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿93&94
Bangaren su yasmeen kuwa, suna can fira kawai suke da yadda zasu yita hidima inta haihu ,su kubra sunci sunsha itada salis da sauran abokanan yarima.
“Suna nan zaune saiga Maryam d yah Omar”.
Murmushi yarima yyi yace oh broth badai tafiya zakayiba?”
Yah Omar yace eh lafiya zanyi sallama nazo miyi,shagwaba yasmeen ta saka ita ah ah bazaitafiba,girgiza kai yah Omar yyi yace hmmm aisaikiyita yi nikinga tafiyata ,cikin shagwaba yasmeen tace wato kasami Maryam ko ?”shine kadaina damuwa dani, dariya yyi yace eh,harararsa yarima yyi yace hmmm munbata dakai ,sudai su kubra dariyarsu suke d haka yah Omar yatafi gd cike da shaukin k’aunar Maryam d’insa.,,,,
Suma su salis basubar gidanba Saida aka kira magrib suka fita tare da yarima yawuce masjids..
Hmmm awannan dare yasmeen tayi baccin farinciki da jindadi Wanda bata tab’ayiba ,cos Daren nadaban ne arayuwarsu taga abinda ake kira gata agun yarima ,motsi kadan yace my Princess mekikeso ?”yah baby nah yake?”zaki sha kaza ko zakici kaza?”kulawa sosai yarima yabawa yasmeen had’e da lallabata kamar kwai…
** ** **
Washe gari byn sun gama shiryawa,Wanda yarima da kansa yyiwa yasmeen wanka da ruwan dumi waibayason ta wahala itada babynsu,koda sukazo yin break kuka yasmeen ta saka masa ita bazataci komaiba sai tea da wainar fulawa”.cikin rarrashi yace my Princess kinga wannan kukun be iyataba bara naje nayiwa ammi mgn tamiki ko?”kuka tafashe dashi… da sauri yajanyota jikinsa ,kansa agefen kafadarta yace menene kike kuka?”fad’amun kinjiko?”ahankali tace ni um um kai nikeso kamun da kanka…zaro ido yyi yace nikuma !aikinsan ban iyaba ko?”cikin kukan kissa tace muje a kitchen saina nuna maka ,yadda zakayi.”tashi yyi ganin tana shirin masa kukan rigimarta da bayaso ,had’a mata tea din yyi mai kauri a cup sannan yasabeta a kafad’a suka nufi kitchen.
Kukun na ciki yana goge goge yana ganinsu yaduk’a yakwashi gaisuwa yabar kitchen din.”
Kujera yarima yajawa yasmeen ta hakimce samanta tana kurban tea d’in ta,nan tace yadebo fulawa da ruwa bbu musu yadebo tashiga nuna masa kaf yadda zayayi kuma yyi ,saidai tun gun yanka albasa yafara shan wuya idanunsa sai hawaye suke,sannan ya yanka tarugu ciki k’anana ,yagama hada komai sauran tuya nan tace ya kunna gas..
“Bayan ya kunna tace ita da pripan zai mata tuyar bbu musu ya aza pripan din kan wutar.”
Tana dg zaune ta na kallonsa ,tanason yin dariya amma ta to she bakinta,ganin yyi wuri wuri dashi basabonba sai zufa yakeyi ,manja yazuba bayan yyi zafi yazuba kullun fulawar,nan tafara soyuwa ,sai ihu yasmeen keyi ita yyi sauri yagama taci babyn sa yunwa yakeji aisaita rud’asa gun juya wainar yasaka lallausan hannunsa aiko yad’askane atake hannun yyi jajir dama ga zunga yana masa dan ya yanka attarugu be wanke hannunba da albasa…
Yasmeen kuwa dukewa tayi tanata dariyarta ta mugunta dan sak abinda yyi mata a farkon zuwanta gidan yafado mata,wato guga da chakol da yadda taita d’askane hannuwanta aigashi nan shima yaji yadda akeji…kallonsa tayi taga yabata fararen kananun kayan dke jikinsa d fulawa had’e da manja..
“Murmushi tayi ,azuciyarta tace oh yanxun in kuyangin nan suka gansafa?”
Kallonsa tayi tace my Prince ka gamane?”
Cikin sauri bawan ALLAH yace ah ah sauran kad’an ko inkawo miki wacce nafara gamawa?”turo baki gaba tayi tace nidai um um,murmushi yyi yace to maman baby yi hkri saura kadan,ida shanye tea dinta tayi sannan taje ta rungume sa tabaya tana kukan shagwaba,ida kwashewa yyi yakashe gas din had’e da juyota gabansa ,hannunsa guda rike d plate din wainar yace muje ko?
“Make kafad’a tayi tace nika wanke hannunka tukum,bbu musu ya aje yawanke hannunsa Ta’s Wanda yyi jaaa duk yadaskane g xingar dayake masa,kallon kitchen din yasmeen tayi taga duk yarima ya hargitsasa..
Hannunta yaja suka nufi parlour sai wannan lallabata yake, yazauna had’e da azata saman cinyarsa yarika bata yana lallabata, itakuwa saici take tana lumshe ido dan ta yi dadi sosai..
” gani tayi yaki ci,”ahankali tace yaya kaci mana girgiza kai yyi yace ah ah banma taba cintaba tunda nike,ai ihu yasmeen ta saka fafur bata yardaba,shikuwa bawan ALLAH yace to kidaina kukan zancu ai,akan dole yazauna sukaci ..
Suna nan saiga ,su Maryam d salim ammi ta aikosu da basket ,dke dauke d farfesun kaji ,da tuwon samanvita miyar danyar kubewa,sun sha mamakin ganin yarima haka,juyawa sukayi ganinsu haka musammun da yasmeen ke zaune saman cinyarsa suna firarsu ta

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 11

YARIMA ASHMAN CHAPTER 13