in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12

Yasmeen data lura tsantsar kishin dake cikin idon yah Omar”ahankali tace oh salim saikace ba yayarkaba kamar k’anwarka!tafad’a yayinda take amsa sallamar yah Omar tana kallon yanayin fuskarsa. ”
Yarima kuwa tashi yyi suka rungume junada yah Omar sannan suka gaisa ,Wanda yah Omar idonsa k’yam akan Maryam,dan yafahimci salim k’aninta ne bbu tazara atsakanunsu,cikin doki yah Omar bayan sun gama gaisawa yacewa yarima yah Ashman yah babynmu?”
Murmushi yarima yyi yace baby yana lfy yanama gaidaka….
“dariya akayi gaba d’aya, salim dke kusada Maryam yagaida yah Omar ita kuwa Maryam tsintar kanta tayi da jin kunyar yaganta bbu d’an kwali da sauri ta duka ta d’auki d’an kwalinta ta rufe kanta dke da kitso shuku yyi kyau yazubo mata dan tanada gashi…niyar tafiya takeyi, da sauri yasmeen tace oh Maryam bazaki gaisheda da yaya Omar dinaba kenan?”
Juyowa tayi sum sum kanta akasa ,yayinda yarima yakalli salim yace oya jeka kawoma yayanku drinks bbu musu yatafi,Maryam kuwa kasa kallon yah Omar tayi dan jikinta yana bata ita yake kallo…ahankali tace ina wuni?”
Yar dariya yyi kafin yyi mgn ,ammi ta shigo parlourn da kuyangi biyu a bayanta suna d’aukeda plate2 d’aya shake yake da awara taji kwai ga wani bowl agefe da yaji ciki,d’aya kuma tsirena yasha kuli ga tumatar da cabbage samansa ..
“Yasmeen da k’amshin yadaki hancinta ,ta lumshe ido tuni yawunta yatsinke” ammi tayi umarnin su ajiye gaban su yasmeen ,kallon yah Omar tayi cike da kulawa tace oh bakin turai Kaine yaushe kadawo??”
Murmushi yyi yace yau ammi, yaduka yagaisheta,byn sun gama gaisawa take tambayarsa umma yace tana lfy..
Kallon yarima ammi tayi ganin yana k’okarin feeding d’in yasmeen tace oh son pls kabimun ita ahankali”murmushi yyi yace to ammi nah nan ta fita,yayinda salim ya,aje musu drinks shima yabi bayan ammi…
Maryam wacce tayi shiru kanta aduke,ganin su 4yarage a parlourn tayi saurin d’ago kanta tsab idanunta cikin idanun yah Omar…. wani yarrrrrrrrrrrrrr!”taji ta saurin rufe fuskarta da tafikan hannunta…..
“Kallonsu yasmeen yyi yaga hankalinsu naga abincin dasuke ci.”
Murya k’asa kasa yace to tunda bazaki gaidaniba dawo nan,yanuna mata gefensa ,Nina gaida ke…
Cikin jin kunya tadawo gefensa,murmushi yyi yace my baby girl ina wuni ?ykk?”
Wani yanayi na jindadi Maryam ta tsintsi kanta wai itace ake kira da wannan sunan ,burinta shine tasamu irin kula da soyayyar dasu yarima da yasmeen sukeyiwa junansu Ashe zata samu oh a….katseta yyi yace bazakimun mgn ba?”
“Ahankali tace lfy lau alhmdllh”.
Murmushi yyi yace amma ni miyasa baza’a kalleniba ?kina kallon wani gu daban kina mgn ” pls kalleni!kallonsa tayi tasakarma sanyayyen murmushi shima yyi mata ,ahankali yace yanxun kije kicire yuni foam kidawo sai musake gaisawa ko baby nah? ”
Mak’e kafad’arta tayi alamar ah ah
Lumshe ido yyi dan yana bala’in son mace mai shagwaba,cikinrarrashi yace oh baby kinaso mubata?”
“da sauri ta ce ah ah”
Yace to jeki canxo kayan ,bbu musu ta tashi ,jiki amace dan duk kalaman yah Omar sun kashe mata jiki..
Yana juyowa yakalli su yasmeen saiyaga itada yarima suna mgn kasa kasa suna dariya…
Matsawa yyi gunsu yace oh wannan dariyar da kukeyi dawa kuke ne?”
Sake ke cewa da dariyar sukayi,yarima yace da duk Wanda yatsargu da kansa….Sosa k’eya yyi yace oh iyayan baby kunacin abu bbu tayi to sainaci nima ai ammin bataku bace ku kadai,yafad’a had’e da daukar awarar guda yakai bakinsa,wani lumshe ido yyi yana jin dad’in ta dan yasacinta..
Shikuwa yarima da yaune yafaracinta shima dan yasmeen ta fara yimasa rigima yasakashi yaci aiko yaji da dadi yacigaba da ci..
Sake daukar guda yah Omar yyi,kukan shagwaba yasmeen tasaka had’e da aza kanta a kafadar yarima tace yaya kaga yah Omar ko?”zaicinyemun kaya in so yake yasaka Maryam ta masa mana…
dariya yarima yyi yace gsky broth zamu bata da kai ,kaida kazo tayamu rainon cikin da jinya saikuma karika Sata tanamun rigima gsky kabari…
Hmmmm ALLAH yah Ashman kashagwaba yarinyar nan da yawa ,yo tayita rigimarta mana sai me?
Sannan naji kince Maryam kai tsaye ko ?”bbu sayi kin kyauta kenan?”
Hararar wasa yarima yyi masa yace lallai kadama kaja inmammari Maryam din,aibazata sabuba zanma gayamata ko bayan aurenku dole tacigaba da kiran my Princess d Anty..
Kafin yah Omar yyi mgn su kubra da salis sun shigo parlourn ,nanfa fira ta kaure da hayaniya duk sun cika ma ammi kunne datake bed room, fitowa tayi suka gaisheta ,cikin dan murmushi tace to iyayen babyn dke ciki ,kukoma part din Ku kuyi murnarku a can….dariya sukayi ,kubra tace ai ammi wani abu ma sai an haihu ,tace to ALLAH yasaketa lfy ,baki daya sukace ameen.
Tashi sukayi ,adede nan Maryam ta shigo cikin gown ta las green tayi masifar kyau dan ba laifi duka gidan mata tafisu kyau dg ita sai hanan.
Salim yana mak’ale da ita sun jero,inkika gansu bazakice kaninta bane,wani killer smile yah Omar yasakamarta azuciyarsa yace oh wannan yaro duk inda zata yana manne like da ita…
Su yarima kuwa fita sukayi zuwa part din su ,shikuwa yah Omar tsaya wa yyi harsu Maryam suka k’araso yakalleta yace my baby girl kinyi kyau…cikin jin kunya ta dukar da kanta,salim yaturo baki yace ni yah Omar banyi kyauba?”
Murmushi yyi yace oh sorry k’aninmu kaima kayi kyau wollah,dariya yyi yace yes ,amma gsky zaku dace dakaida twins sister na,nikuma kaga k’aramine banida budurwaaaaa!!
dariya sosai yaya Omar yyi dan yalura salim akwaisa d barkwanci,ita kuwa Maryam jin kunyar maganarsa tayi,ahankali yah Omar yace my baby girl miyasa baza kimishi budurwaba ?”
Turo baki tayi cikin shagwaba ta ce ,aiyarone”kuma bayason mata ko sunce suna sonsa…
Murmushi yyi yace ok muje to kimun rakkiya zan wuce gd ko?”
Cikin shagwaba had’e da yarinta tace to muje ka gaishe da mama nah ko my salim ?”tafada tana kallon salim..
,,,salim kuawa cewa yyi eh gsky bara naje nafara sanar da ita,yana fadin hakan yajuya yatafi..
Shikuwa yah Omar “Ahankali yakalli Maryam yace my baby girl pls kibari zanxo saimu gaisa kinga k’anannun kayane ajikina yanxun kinji?”
Kukan shagwaba ta saka masa ita ah ah suje kosu bata…
Shiru yyi yakafeta da idonsa yana kallonta ganin yadda shagwabar ta mata kyau…
Murya kasa kasa yace to muje ko,amma sai kinmun dariya!
Kallonsa tayi ,had’e dayin dariyar,shima ita yyi yace ILOVE U my baby girl …
Lumshe ido tayi ,suka jera suna tafiya,ahankali yace ko bakya sona ne ?”
Rufe fuskarta tayi,hakan yasakashi yagane tana sonsa ,har cikin parlourn hyj rahama suka shiga ,samunta sukayi zaune kan kujera salim yyi matashi da cinyarta yanata tabararsa,sallama yah Omar yyi kansa aduke ,yaduka har k’asa yakwashi gaisuwa …
Cikin sakin fuska mama ta amsa had’e da cewa Omar kazauna mana kan kujera kasaki jikinka ai nan gidankune ,yasu umman ?”
Murmushi yyi yace lfy lau alhmdllh.
Kallon Maryam tayi tace oh kinyi wani tsaye kije kikamasa ruwa mana..
Cikin shagwaba tace to mama salim yatadamun cinya manah..
Girgiza kai tayi tace oh ko ina kuke baza by dena shiriritarkuba ko?”
Sai asannan yah Omar yyi mgn yace oh mama dama haka suke wannan shagwabar, suna hawa cinya Manya dasu..

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 11

YARIMA ASHMAN CHAPTER 13