in

YARIMA ASHMAN CHAPTER 11

YARIMA ASHMAN CHAPTER 11

Beyi mgn ba sai yasa hannunsa yanuna mata gefensa…wazata gani?”yarimane tsaye yakafeta da firgitattun idanunsa dasukayi zajir yana watsamata kallon tsana..
“” wani kallon tuhuma tajefi bash dashi, “shikuwa mak’e k’afad’a yyi alamar ko ajikinsa”.
Cikin takunsa na k’asaita had’e da isa yanufota…tana ganin haka ta fara ja da baya dan guduwa dan tasan halin yarima in and out..
” wata muguwar damk’a yyi mata ganin zata shige mota ,tana juyowa ya wanke ta da maruka lafiyayyu guda2wanda Saida jinta na wucin gadi yad’auke.”
Wata mummunan shaka yyi mata Wanda atake idanunta suka fara ruwa ta sark’e da tari ba k’akk’autawa ,Wanda shikanshi bash yatsorata daganin irin wannan shak’ar da yarima yyiwa salma.”
Saida yatabbatar ta jigatu yacika ta had’e da hankada ta kanta yabugi marfin motar,tasaki wani uban ihu….
“Cikin kakkausar murya ya nunata da yatsa yace ,natsaneki ,banason ki bana k’aunarki dana aureki gara natabbata bbu aure arayuwata. inaso kisani yasmeen ta fi k’arfinki ,yasmeen yar gatan ubangiji ce baki isa kiyi mata komai ba ,saidai sharrinki yakoma miki!
Wawiya fasik’a ke a tunanin ki na had’a yasmeen da wata y’a mace ?” Kinyi kuskuren da jakar brain d’inki kike tunanin yiwa yasmeen sharrin zina,inaso kisani nayarda da mamata dari bisa d’ari tanada tarbiyayya bakamar keba da Kika zubda darajarki atiti Kika zama kingi.”koda kinci galaba akan wannan mugun gudirin naki to bazan rabu da yasmeen ba mata d’aya tamkar da 1000,bana aikata abu sainayi binkice,dan binkicen ne yasaka nagano yes kina nemanmu da sharri yanxun kuwa nazo hukuntaki,inafatan kin fahimta”.
Zare ido kawai salma keyi dan duk ta ji yafitar mata arai ga zafin maganganunsa na cin fuska ga kuma wai zai hukunta ta ,kuma haushinta guda agaban bash aisai yarainata yaje yana yayata ta.”
Bata gama tunanin ta ba taga yarima na k’ok’arin bude dan bucket d’in dke hannunsa
atsorace tace meye aciki?”wata uwar harara yyi mata yace acid ne zan zubamiki afuska in lalata fuskar da dama bleaching yagama watsawa kixama abintsoro ga lalatattun mata irinki….
Atsorace tace pls wlh natuba kada kamun haka na rok’ek’a wlh nafita arayuwarku…tsaki yarima yyi atsawace yace kadama ki fita indai kincika y’ar halak!amma fa yanxun zan zubamiki na zubawa banxa bbu abinda za’ayi ….kuka tafashe dashi ta duka k’asa tanabashi hkuri…bash ne yazo yajanye yarima dg gefenta ,cikin girmamawa yace y’allab’ai dan ALLAH badan niba karabu da ita tunda da alama tayi nadama intasake yunkurin hakan saikayimata abinda ka gadama,ajiyar zuciya yarima yyi dan dama ba watsamata zaiyiba burgace kawai dan yatsorata “ahankali yace ok nabarta dan ALLAH saidai inaso kisani duk inda Muka hadu Kika nuna kinsanni,saina wulakantaki sakarya wacce ta zubarda da mutuncinta a titi…
Yana fadin hakan fuuuuu yabar gun .
Kallonta bash yyi yace kiyi hkuri kada kiga naci amanarki ah ah na shiryune yanxun ina tsoron ALLAH, kema ALLAH yasa kigane gsky…
” yana kaiwa nan da sauri yabarta anan”
Yana zuwa gun dasukayi parking yasamu yarima acikin motar,nan yabude masa yashigo suka fara tafiya bbu mai mgn acikin su.”
Can yarima yace gsky naji dad’in yadda ka shiryu,kuma na gode sosai da kasanar dani abinda salma kesan aikatawa!
Murmushi bash yyi yace ba komai.
Yarima yace aikin me kake yanxun?
Yace karatu nikeyi ina shekarar karshe sai inama wani tsaron shago inasamun nacin abinci..
Cikin tausayawa yarima ce ok b damuwa gobe kasameni a office dina zan samarmaka wani abun yi mai kwari,godiya bash yashiga yi bbu kakk’autawa tun kan yasan me za’abashi.”
Adede k’ofar gidansu yarima ya ajesa,shikuma yyi yar tafiya kadan yatsaya yyi sallar la’asar sannan yayo gd…
*********
Yasmeen kuwa tana tashi dh baccin ta duba taga bbu yarima ,cikin jin haushi tace wato wayo yyimunko?”hmm zaidawone ai,tashi tayi ta yo wanka had’e da yin alwarla tayi sallah sannan ta shirya cikin purple din super exclusive Riga da zani tayi daurin daya fito da ita tayi kyau…
Harta zauna taji tanason shan furar ammi,amma me?”tasan wannan masifaffar tsohuwar tana sashen.
“Tashi tayi dan jitake inbatasha furarba ,kamar bazata iya baccin dareba”.
Aiko tana zuwa ko tasameta hakimce akan kujera tayiwa tb k’uri kamar tanajin abinake cewa ,ammi na gefe kuyangi 2na matsa mata k’afa,sallama tayi cikin d’ar d’ar ,ammi ta amsa fuska asake nan yasmeen ta gaidasu ,wadda hjy babba ciki ciki ta amsa.ammi tace yayadai yasmeen kinyi shiru?” ahankali tace dama ammi zansha furane…tsaki hjy babba tayi tace oh to a can b’angarenku bbu ne saikin zo nan?”hmm gsky yarinyar nan da alama kingama dasu yodama jikar mlm,koda alhj tsoho yace wannan abar zai aurawa yarima nasan sai mlm yashiga yafito sun gama da…..ammice tace haba hjy dan ALLAH kidena hakan sbd cin fuska ne bbu dadi….
“Baki bude hjy babba tace banga laifinkiba angama dkene.”
Ammi ta tsaida kuyanga guda dasuke shirin fita dg parlourn,tace ta dakko gidauniyar fura a frige.,,
“Yasmeen kuwa ko ajikinta da surutun hjy babba dan tasan dg gobe insha ALLAH zata tafi tabar musu gidan”.
Karb’ar furar tayi ,ta aje gabanta tafara sha….jin sallamar yarima yasaka ta tafasa shan furar,dan yaje part din su bata can.
,,,,had’e rai yarima yyi had’e da yin kicin kicin da fuska sakamakon ganin hjy babba a parlourn, zama yyi yagaidasu ..tsaki hjy babba tayi tace ka rik’e abunka ,shiru yyi be tankataba,yakalli yasmeen yace my Princess ashe kina nan naduba bakyanan?
Turo baki tayi had’e da harararsa.
Murmushi yyi yace ninefa Prince dinki!tace eh d’in bakaine kayimun wayoba kayi tafiyarkaba …azuciyarsa yace hmmm bakisan fitata alkhairi bace ba,amma afili sai yace fitarce tazama dole shiyasa my honey kiyi hkuri kinji tawan?”
Itadai ammi tana kallonsu,cike d burgewa da sha’awa dan tasan so ba karya bane ,ta fuskanci soyayya kamar haka gun me martaba Saida hjy babba ta tasota gaba waits mallake mata d’a ,Saida ya auri hjy rahama sannan ta barta tahuta shine yanxun kuma zata koma kan yarima..
Yarima yakalli yasmeen yace my honey zansha furar”make kafada tayi tace um um nidaya ammi tabamawa.dan murmushin gefen baki yyi had’e da matsawa kusada yasmeen yace nikuma nace sainasha b…maganar hjy babba ce tahana yarima kin ida maganarsa jiyyi tace oh ni halima wannan zamani bbu kunya ba tsoron ALLAH agabanmu da gyatumarka kuke wannan abu lallai bakuda kunya kuma yarinyar nan ta cuceni tabata maka tarbiyya tun….magana yarima keshirin yi ,ammi tayi masa alamar ah ah,afusace Yakama hannun yasmeen suna fita,yyinda ammi tasaka abisu da furar part din su.
“” Ahanya yarima yakalli yasmeen yace dg yanxun kada kisake zuwa part din ammi sai wannan masifaffar tsohuwar ta tafi kinji my honey nah?yar dariya yasmeen tayi tace nifa yaya yanxun nadena damuwa tunda kai baka canxamunba dan wani yacanxamun banajin komai..adedenan suka shige parlourn.
Suka tararda fura harta rugasu isowa kan carpet duka zauna yasmeen na tsakkiyar cinyoyinsa suna sha sna firarsu,knocking sukaji,yarima yace yesssss!aka shigo salis ne .
“Bayan sun gaisa,cikin tsokana salis yace to lailah d majnun,inkuna tare na luramanta wa d kowa kkeyi”.
Yarima ya hararesa had’e da matse yasmeen gam datake shirin guduwa sbd salis,yace pls mlm yi tafiyarka banason takura lokacin iyalinane wannan.
Dariya salis yyi yace pls yasmeen kitaimakamin wlh kubra tak’i saurarena wlh,yafada fuska kalar tausayi.
” Ahankali yasmeen tace ka kiratane?”
“Yace eh yafi akirga amma bata peaking”.
Cikin rada yasmeen tace wa yarima yaya pls bara naxo kaji ,ok yace had’e da saketa ta shige bed room dinta tanajin yarima na tsokanar salis..
Tana zuwa takira kubra ,kogaisawa basuyiba tace haba friend meye? haka wulakanci bbu kyau shine yaya salis yakiraki kikaki dagawa?
Ahankali kubra tace ke jamasa aji nayi ,nimafa yyimun ,tsaki yasmeen tayi tace to bari nasanar dashi hakan..d sauri tace ah ah yi hkuri pls zan daga kiransa ALLAH inmayimasa kwatancen gidanku.
Yar dariya yasmeen tayi tace oh anaso ana kaiwa kasuwa ,nan sukayi sallama, yasmeen ta je tasanar da salis cewa yakirata zata d’aga ,abinda yasa bata d’agaba ,bata daga bak’uwar number..
Cikin jin dadi salis yyi godiya had’e da hararar yarima ,yace to kaji kaimeyimun dariya,adaidai nan kubra ta d’aga kiran dan dama yasmeen na cewa yakira yyi calling d’inta,cikin xakuwa yace hellow baby yafad’a had’e da ficewarsa ,su yarima namasa dariya..
Kallon yasmeen yarima yyi yace baby muje nayi wanka bbu musu ta bisa tahada masa atare suka shige ta cud’asa sunata wassaninsu ,har aka kira magrib ,alwalla sukayi sannan duka fito ,yawuce masjeed,itakuma tayi tata agd…
Bedawoba sai da aka yi isha’i tukum yasamu yasmeen kwance tsakkiyar bed din sa dg ita sa yar have vest iya cibi da Dan mini siket..tana chat d friends d’inta….
Koda yaga hankalinta baya gunsa sai yahaye Samanta yakarbe wayar ,ihu tasaka itasaita karba,aiko yafara yimata cakulkuli sai dariya abinsu suke itama ta mirgina tadawo kansa ta ruk’a yimasa cakulkulin suna dariya dg nan salon yacanxa duka Lula wata duniyar…
Washe gari bayan sun gama kimtsawa,state duka fito dan gaisheda su ammi ya wuce office ita kuma skul dan yanxun itama da guards zata ruka zuwa skul din Wanda yajamusu kunne sosai akan su kula masa da ita..
Koda sukaje bbu kowa apart din ,parlourn Sarki suka wuce ,aiko nan suka sami hjy babba,ammi,mama,da lubna sai alhj tsoho zaune yana Jan casbaha.
Yana ganin su yyi murmushi, yace to Ku k’arasomana.
Sallama sukayi had’e da…
Share pls
AWESOME WRITER’S ASSO..🏮
(palace of excitation and pleasant writer’s)
YARIMA ASHMAN
🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
🅿83&84
“” Sallama sukayi had’e da samun guri suka zauna.
bayan sun gama gaisawa alhj tsoho yyi ajiyar zuciya yace yasmeen!
Ta d’ago kanta had’e da amsawa ,yace kiyi hkuri kinji?” da abinda yafaru kidauka kamar bai faruba ,domin duk Wanda aka bawa hkuri to anxalinceshi.”
“Ahankali tace babu komai ya wuce wlh,alh tsoho yace ALHMDLLH to ALLAH yyi muku albarka ,gaba d’aya akace ameen.
Kallon lubna yyi yace ke kuma marar mutunci nadawo gareki, kifita harkar yarinyar nan tun kafin iyayanki suyimiki baki…kibata hkuri yanxun!kinji kobakiji ba?” Yafad’a atsawace ,da sauri lubna tace naji,ta kalli yasmeen tace kiyi hkuri dan ALLAH da abinda yafaru “yasmeen tace ya wuce ,nan lubna ta rok’i Sarki d ammi gafara sukace sun yafe amma duk radda tasake shiga harkar yasmeen hmmm…
” nan alh tsoho yasallami kowa “yyinda hjy babba sai cika take tana batsewa,yakalleta yace halimaaaaaaa!
Halima !Halima!!

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 10

YARIMA ASHMAN CHAPTER 12