in

SOYAYYAH CHAPTER 11

Zee na kwance akan makeken royal bed nata, kallo d’aya zaka mata ka hango
matsananciyan damuwa tattare da ita dan yadda tayi bak’i ta rame.
K’asan tiles natan kam du tissues ne da akai staining da blood, ahankula ta mik’a hannu ta
waro tissue d’in again.
Tare bakin ta tayi dashi tana janye wa kuwa du ta b’ace da wani bak’in jini mai matuk’ar
firgitarwa.

Lokacin da ta kalla she just can’t help ta fashe da wata masifaffiyar kuka.
She is damn scared and worry cause wa’adin da Daddy ya d’iba mata na gab da cika, bata
son Ammar bata son Amiz ga kanta ya kulle ta rasa mafita.
Wayanta ta d’auko wanting to call the jerk amma tunowa da tayi no Matter what bare
d’auka ba sai kawai ta ajiye wayan side, ta soma catching up breath nata dake barazanan
barin ta, she is in so much pain, yadda zuciyan ta ke mata zugi da rad’ad’i is just
unbearable.
Within the week kullum gaban ta fad’i yake wanda bata san meke shirin faruwa da ita ba,
wayan ta sake jawo wa ahankali, jin yadda jini yake fita ta ears d’in ta tayi saurin jayo tissue
ta cire wanda ta toshe kunnen tai replacing da sababbin da ta cire, again wani ta ciro jin
yadda bakin ta ya cika ta sake zubar wa kan tissue d’in ta yasar a gefe.
Gaba d’aya ta gama cire rai da rayuwa dan situation nata kullum k’ara worsting take.
Dakyar ta jawo wayan ko gani sosai batayi dan yadda idanun sukayi luhu _luhu saboda
kuka, kukan da take har affecting idon tata tayi.
Turning on data nata tayi ta shiga WhatsApp wanting to post her last and final story ever,
idanun ta ne suka kai kan group ta school tasu ganin yadda massages ke rushing shigowa
aciki, haka kawai taji tana son viewing.
Ahankali ta soma bin hiran tana karantawa gaban ta na tsanan ta fad’i, the more take k’asa
the most heart beat nata ke beating so fast wane zatayi bursting k’irjinta ta fito.
A firgice ta mik’e not believing exactly what she is seeing, hannayen ta na tsananin rawa ta
cigaba da bin massages d’in.
Wata rikitacciyan k’ara ta kwalla yayin da wani abu kaman mashi ya soki zuciyan ta, watsi
da expensive perfumes nata dake kan mirror tayi, ta shiga buga hannayen ta jikin mirror’n
ta ya tarwatse.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

ZULFA CHAPTER 1

GIDAN UNCLE COMPLETE