in

SOYAYYAH CHAPTER 1

SOYAYYAH CHAPTER 1

Alhaji Muhammad Ibrahim Agadez, Unguwar Yahaya gusau, KANO, KANO STATE.
‘Yar k’aramar yarinyace ta fito da gudu, sanye take da pink coloured riga iya gwiwarta, sai black coloured skin tight,jelar gashin ta yasha gyara an mata packing da pink coloured ribboms, duka_duka bazata wuce 12 years ba.
Kyakkyawar yarinyace fara k’al, face nata har wani ja yake saboda fari, da gashi kwance luf_lufa goshin ta hakan ba k’aramin kyau ya k’ara mata ba, tanada cikan gashi ga tsayi kamar balarabiya, bak’i ne sid’ik ga santsi kaman na baby, tana da dogayen eyelashes da suke kallon k’asa, da manyan idanu wanda inta zare su saita baka tsoro , kwayoyin idon nata sky blue coloured ne kamar na baturiya, tanada dogon hanci wanda ya k’arawa siririyar fuskarta kyau, bakin ta d’an k’arami ne wanda inka kalla saika zata spoon bazai shiga ba, colour d’in lips nata light red ne. Safwah kenan, yarinya maiji da hutu, kyau, gata uwa uba shagwab’a.
Tana d’auke da k’atuwan pink coloured teddy bear, k’araso wa tayi gurin wata farar Dattijuwa dake zaune akan sofa tana karanta daily trust.
Cike da shagwab’a tace ” Granny what say’s the time please? ” D’agowa Dattijuwar tayi ta kalli diamond wrist watch d’in dake d’aure a tsintsiyar hannun ta tace ” quarter pass 2 baby “. ‘
Tana jin haka ta kwasa da gudu tayi waje, girgiza kai wannan Dattijuwar tayi tace ” yanzu haka da kuka zaki dawo “. Parking space ta nufa ta nemi guri ta zauna a kan wasu iron chairs masu matuk’ar kyau da akayi decorating gurin da su, ga wasu red and yellow flowers masu dad’in k’amshi da suka k’awata gurin.
Bata dad’e da zama ba wata bak’ar Prado jeep ta shigo, da sauri ta mik’e tana tsalle tana ” oyoyo, oyoyo “, ana gama parking driver ya zagayo da sauri ya bud’e right side sannan ya zagaya ya bud’e left side.
Ahankali suka fito da legs d’insu then complete body nasu. Duba na nakai kan last guy d’in daya Fito daga motar, kyakkyawan saurayi ne fari tas, yana da suma wacce ta

kwanta luf_luf akansa black coloured, tana walk’iya dan ba k’arya kallo d’aya zakai mata kasan tasha gyara, sai saje kwance akan farar fatar sa kamar balarabe wanda da ace yana da gemu da sun had’e, gashin giransa a cike yake bak’ik’k’irin yayi curve kamar cinku, ga eyelashes masu santsi zara_zara, yana da idanu dara_dara masu tafiya da zuciyar ‘yan mata, idanun nasa suna nan madai daita da kwayoyin idon nasa black , yana da dogon hanci wanda ya k‘ara k’awata ‘yarfuskar sa da d’an madai daicin bakin sa pink colour, yana da dimples a both cheeks nasa dan ko smile yayi sai sun lotsa, dogo ne shi yanada faffad’an k’irji, duk da cewan shid’in siriri ne amma ba can be, yanada
six packs wanda ya k’ara fito da mazan takarsa. Guy d’innan dai Kat ne dan anacewa mutum tara yake bai cika goma ba, to nidai zance wannan ya cika saidai ko a halayyarsa asamu akasi. Suwayd kenan, Mr arrogant yaro maiji da zamani, kud’i, kyau uwa uba ilimi. Kallona na mayar kan guy d‘in dake middle d’insu, kyakkyawa ne shi sai dai kallo d’aya zakai masa kasan yafi Suwayd fara’a, dogone shima yanada saje a fuskar sa kamar balarabe
, suman kansa yasha gyara kaman na shahid kapoor and a fizge yana kama da Suwayd. Sayyid kenan, Mr cool, kind and breathtaking. Ahankali nakai dubana kan d’ayan shima

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

DAN MACE CHAPTER 5

SOYAYYAH CHAPTER 2