in

SOORAJ CHAPTER 5

SOORAJ CHAPTER 5

CHAPTER 5 KARSHE

Idanunsa ne suka kad’a sukai ja, lokaci guda gargasan dake kwance ajikinsa suka mimmik’e, idanunsa ya rumtse, yana mejin wani irin abu da ya taho ya tokare mak’oshinsa.
Cikin yanayi na tsoro ta shiga girgiza kanta, da k’arfi ta fusge hannunta dake cikin nasa, hawayene suka shiga gangarowa daga kan fuskarta, cikin sauri ta juya da niyar barin wajen, idanunta ne suka sauk’a akansa, inda yake zaune cikin motarsa yana kallonsu, wani irin bugawa k’irjinta yayi, take wani irin mummunan fad’uwar gaba ya rusketa, wasu sabbin hawayene suka kwaranyo daga cikin idanunta, zuwa kan fuskarta. +

Wani k’awataccen murmushi Pharouk yasake, tare da d’an satan kallon SOORAJ wanda ke zaune acikin motarsa, inda ya d’auke kae yayi kamar ma baigansuba, murmushin mugunta Pharouk yayi, yana mejin wani irin sanyi na ratsa zuciarsa, komai da gangan yayi, don kawai ya k’untata zuciyar SOORAJ d’in, yanasane da Zuwan SOORAJ d’in shiyasama ya rik’o hannayenta, duk da cewa sha’awar da yakeyi mata nada yawa, amma kuma awani b’angare na zuciyarsa yanajin soyayyarta, hannunsa yakai da niyar sake tab’a hijab d’inta, saidai yayi rashin sa’a don kuwa tuni tasoma tafiya, hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa inda ya k’urawa bayanta ido, tsoro fargaba sune abun da suka cika zuciyarta, cikin yanayin sanyin da jikinta yayi ta k’araso jikin motar, cikin tsoro ta bud’e murfin motar, Sassanyan k’amshin turarensa da ya bugi hancinta ne yasanya tsikar jikinta mimmik’ewa, cikin rashin kuzari ta shiga cikin motar, kafunma tayi yunk’urin daidaita zamanta yafigi motar da wani irin speed, kan Pharouk dake tsaye yayi da motar, ihu Zieyaderh tasanya tare da rumtse idanunta, don taga dagaske kan Pharouk d’in ya nufa, saida yakawo gaf da Pharouk d’in sannan ya taka wani irin birki Wanda yasanya harsaida kanta ya bugu da gaban motar, Ido cikin ido suke kallon juna shida Pharouk d’in, wani irin kallo Wanda ke k’unshe da zallan gargadi SOORAJ ya watsawa Pharouk, tare saying wani irin reverse, murza steering mota yayi, cikin wani irin speed yanufi hanyar fita daga cikin makarantar yayinda ya bud’awa Pharouk k’ura, daga kan jikinsa harzuwa kan fuskarsa, da gudu masu gadin gate d’in makarantar suka mammatsa gefe, sakamakon ganin yanda motar tayo kansu. 2

Da k’arfi Pharouk ya rumtse idanunsa, yana mejin wani irin bak’in ciki na ratsa zuciyarsa, kallon jikinsa yayi, gaba d’aya kayan jikinnasa sun b’aci da k’ura, ransa ne ya b’aci, saidai kuma tunawa dayayi cewa ya isar da sak’on da yakeso na bak’in ciki azuciyar SOORAJ, yasanyashi jin sanyi a ransa, haka yashiga motarsa yabar makarantar, zuciarsa na k’issima masa abubuwa da yawa. 1

Sosai ta tsorata da irin gudun da yake shararawa akan babban titin, cikin rufewar ido yake tuk’i, gaba d’aya jikinsa rawa yake, matsanancin b’acin rai ne kwance akan kyakkyawar fuskarsa, sosai zuciyarsa ke tafasa, wani irin d’aci yakeji amak’oshinsa, idanunsane suka sake kadawa sukai ja, yayinda jijiyoyin dake kansa suka mimmik’e inda suka fito sukayi rud’u rud’u.

Sam bayako iya ganin gabansa da kyau, dayawan motoci ke kauce masa ahanya, don kuwa kowa yaga irin tuk’in da yakeyi yasan bana lafiya ba.

Wani irin mahaukacin horn yake dannawa kamar zai dage unguwar bak’i d’aya, da wani irin hanzari maigadi ya wangale masa gate d’in gidan, dan shi kansa ya tsorata da irin yanda maigidannasa ke danna horn kamar zai tashi sama.

Dagudu yatura hancin motar ciki, wani mahaukacin parking yayi, inda ko second d’aya bai k’ara acikin motar ba ya bud’e murfin motar ya fice, wasu sabbin hawayene suka silalo daga cikin idanunta, sosai tahango matsanancin fushi akan fuskarsa , jikinta amatuk’ar sanayaye ta bud’e murfin motar ta fito.

STORY CONTINUES BELOW

Koda yashiga falon kaitsaye bedroom ya wuce, yana shiga ya bugo k’ofar da k’arfi, cikin yanayinta me d’auke da sanyi tashigo cikin falon, ganin bata gansa acikin falon bane yasanyata zubewa akan sofa, idanunta wanda har yanzu ke tsiyayar hawaye ta lumshe.

Akan gado ya zauna tare da sanya duka hannuwansa biu ya dafe kansa da yakejin kamar zai tarwatse, sosai zuciyarsa keyi masa zafi, rumtse idanunsa ya kuma yi da k’arfi, sakamakon tuna wa da yanda yaga hannuwansu sarke cikin na juna,
Jikinsa ne ya d’auki rawa sosai cikin tsananin b’acin rai yayi wurgi da bedside lamb din dake gefen gadon, wani mak’ak’i ne kedamun zuciyarsa, baitaba jin zafi irin haka ba, baisan wannan bak’on Al’amarin ba, saboda haka bazai iya jurewa ba, wani irin tari ne ya sarke mak’oshinsa, sosai yake tarin ba k’akk’autawa, cikin yanayin gajiyawa daya dan soma shiga, ya d’auki wani farin handkerchief, inda yashiga goge jinin dake fita ta bakinsa, saboda tsabar tsananin b’acin rai har wani d’aci yakeji a mak’oshinsa.
Ahankali taturo kofar dakin tashigo, idanunta ne suka sauk’a akansa, cikin firgici ta zazzaro idanunta waje, sosai jinin da tagani abakinsa ya razana ta, d’ago kansa yayi inda idanunsa suka sa’uka acikin nata, afusace ya tashi daga zaunen da yake, ya nufota, yana k’arasowa ya damk’i hannunta, ransa amatuk’ar bace ya bugi k’ofar d’akin, har saida ta bud’e, da k’arfi ya hankad’ata waje tare da jawo kofar d’akin ya rufe, kana ya murzawa kofar key, wani irin bugewa kanta yayi da jikin kujera asakamakon wurgota da yayi, kuka ta sake mai sauti, inda lokaci guda jikinta ya d’auki rawa, bata tab’a ganinsa acikin irin wannan yanayin ba, sosai yanayin idanunsa suka tsorata ta, kanta ta cusa atsakankanun cinyoyinta, kuka take sosai tare da matse jikinta waje daya.

Cikin yanayin b’acin ran dayake ciki ya bud’e k’ofar bath room ya shige, sosai zuciyarsa ke tafasa hakanne yasanyashi kunna shower, tare da tsayawa ruwa na dukan
jikinsa, ak’alla ya d’auki kusan sama da mintuna talatin yana tsaye ruwa na dukan jikinsa, har yanzu zuciyarsa tafasa take, daya kulle idanunsa su kawai yake gani, yanajin kamar ana caccaka masa wuka akan kahon zuciyarsa, da k’yar ya iya kashe shower’n, farin bathrube ya sanya ajikinsa, haka ya fito daga cikin toilet d’in zuciyarsa duk ba dad’i, ko tsayawa goge jikinsa baiyi ba, ya zura wani dogon trouser ha’e da wata farar long sleeve marar nauyi, zama yayi akan bedside tare da sanya hannuwansa ya dafe kansa dake masa ciwo, Sam bayajin dadin jikinsa,, rumtse idanunsa yayi da k’arfi, ahankali sautin kukanta ke shiga cikin kunnuwansa, labb’ansa yadan ciza da k’arfi,
sam bayason kukanta, jin kukanta daidai yake da d’iga masa narkakkiyar dalma akan fatar jikinsa, zai iya jure komai amma banda kukanta, hannayensa yasanya ya toshe gaba d’aya kunnuwansa, mekenan? Me hakan yake nufi? ganinta da Pharouk yasanyashi jin wani irin rad’ad’i acikin zuciya da gaba d’aya ilahirin jikinsa, yanajin wani irin abu me d’aci ya toshe masa mak’oshi, idan har hakan dayaji akanta shine abun da ake Kira KISHI, to tabbas yana matsanancin kishinta, Inda KISHI kuma akwai SO, duk da cewa baisan menene SO ba, haka baisan tayaya zai misalta abun da ya keji a zuciyarsa ba, ajiyar zuciya ya sauke, tare da jingina bayansa da jikin bango, Ya yarda yana mata wani irin TSANANIN SO, baisan yaushe kuma da yaya hakan ya kasance ba, amma tabbas yayarda cewa yana cikin magagin Soyayya. 2

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 4

RAINA KAMA CHAPTER 1