in

SOORAJ CHAPTER 4

SOORAJ CHAPTER 4

Ahankali ya zuro da ƙafafunsa ƙasa, tare da rumtse idanunsa wanda suka kaɗa sukai ja tamkar waƴanda aka watsawa garin barkono, hannayensa ya sanya ya dafe kansa dake barazanan tarwatsewa, wani iri yakeji acikin kansa tamkar ana doka masa gudu ma, cikin ƙarfin halin daya aro ya dasawa kansa ya miƙe tsaye tare da soma binbango yana neman hanyar da zai sadasa da toilet, zuwa yanzu ko gani sosai baya iyawa, wani irin duhu ne ke neman mamaye ganinsa, sunan Allah Yashiga ambata acikin ransa yana me tafiya ahankali, ƙafafunsa ne sukayi masa nauyi, haka yakeji tamkar an ɗaure masa su da kaca, aninayen dake jere reras agaban rigarsa ya soma cirewa, tare da sanya hannunsa ya kunna shower take ruwa yasoma zuba ajikinsa, duka hannayensa ya sanya ya dafe bango tare da rumtse kyawawan idanunsa, yayinda ruwa ke dukan naked skin ɗinsa, still ambaton Allah Yaketayi acikin ransa, ahankali yakejin nutsuwar daya rasa na dawo masa, yayinda yaji gaba ɗaya jikinsa yayi weak, zuciyarsa kuwa har yanzu fast fast haka take bugawa, sake lumshe idanunsa yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa, ko ka ɗan bayason tuno mafarkin da yayi wanda tunda yake bai taɓayin makamancin irin saba, bayan hannunsa yasa yaɗan naushi bango tare da kashe shower’n, wani white towel ya ɗaura akan waist ɗinsa tare da ɗaukan wani ɗan ƙaramin towel yashiga goge jiƙaƙƙiyar suman kansa, koda ya fito daga toilet ɗin, zama yayi akan dressing mirror tare da ɗaukan body lotion ya shiga shafawa jikinsa, yana gamawa ya feshe jikinsa da wani irin body spray me daɗin ƙamshi, black pencil crazy jeans and white t-shirt ya sanya, kasancewar anyi ruwa sannan akwai sanyi sosai agarin yasanya shi ɗaura black leda jacket akan rigan, wayoyinsa ƙiran Samsung galaxy S20 da kuma iphone 11 pro max ya zura acikin aljihun jacket ɗin nasa, wasu irin combat shoe yasanya masu kyau da tsada, ahankali ya ƙarasa gaban mirror tare da ɗaukan facing cap white colour ya sanya akansa, baƙaramin kyau shigan yayi masa ba, yayinda sajen dake kwance akan fuskarsa keta shinning. Farfumed ya fesa ajikinsa kana ya nufi hanyar fita daga ɗakin, ahankali yake sauƙowa daga kan haɗaɗɗen matattakalan da zai sadasa da wani katafaren falo wanda yagaji da haɗuwa, yana ƙarasowa cikin falon yanufi wajen wani haɗaɗen fridge wanda yake na glass, gaba ɗaya kana iya hango duk wani abu dake ciki, buɗe fridge ɗin yayi tare da zaro gwangwanin malt, ɓalle murfin yayi tare da kai bakinsa jikin gwangwanin, 8 minute kacal ya shanye gaba ɗaya malt ɗin, tare da wurga gwangwanin cikin dustbin. Cikin takun dake nuna tsantsar aji da kuma nuna cikakken zarransa na ɗa namiji, ya fito daga cikin ƙawataccen hotel ɗin, wanda anan yake da zama tunda yazo Singapore, hotel ne mai kyaun gaske don yana ɗaya daga cikin manyan hotels ɗin da akeji dasu a ƙasar Singapore, tafiya yake da ƙafafunsa yayinda yashiga cikin ƴan ƙasar yasaje dasu sak, kasancewar kalan fatarsu iri ɗayane danasa yasanya bazaka iya banbanceshi da suba, babu wani ɗaya acikinsu da zaice ya ɗarasa hasken fata, wani ƙaton club yanufa inda maza masu aji ke zuwa, kowa dake cikin club ɗin harkan gabansa yake babu ruwan kowa da kowa, wasu suna shaƙatawane da ƴan matansu yayinda wasu keshan wine, wasu kuwa rawa kawai sukeyi, kan wata kujera da take ita kaɗai ya zauna tare da zaro wayansa don yanaso yayi vedio call da Mas’oud, ɗaya daga cikin masu aiki a club ɗinne ya tambayashi tsakanin Alcohol da wine wanne yake da buƙata. kansa ya girgiza tare da cewa ya basa drinks kawai, hakan kuwa akayi inda ma aikacin ya cika masa gabansa da drinks kala kala, nan ya maida hankalinsa ga wayarsa tare da dannawa Mas’oud ƙira.
Nigeria

Kasancewar Yau asabar babu makaranta hakan yasa bata tashi da wuri ba sai wajen 9, kasancewar yanzu sam bata aikin gidan Oummu ta ɗebi wadatattun ma’aikata wanda sukeyin girki da komai, fitowanta a wanka kenan zama tayi agaban mirror tare da shafa mai ajikinta, sama sama ta shafa powder akan fuskarta tare da ɗan goga man baki abakinta, wata doguwar riga na black lace ta sanya, sosai rigan tayi mata kyau, tsayawa tayi tana me kallon kanta a madubi, ita kanta tasan tayi wata ƴar rama wanda bakowane zai gane hakan ba har sai in wanda ya lura, tana ƙoƙarin ɗaura ɗankwali ne aka turo ƙofar ɗakin nata, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta cikin yanayi na girmamawa tace “Barka da safiya Oummu!” +

STORY CONTINUES BELOW

“Yauwa barka, fatan kintashi lafiya!” Oummu ta tambayeta cikin kulawa.

“Lafiya ta amsa tana me ƙoƙarin sunkuyar da kanta ƙasa.
“Masha Allah, to maza zo muje yau kina da babban baƙo yana falon Abbanku, nasan da ace kinsan da zuwansa to tabbas da tun 7 zaki tashi” Oummu tafaɗa tana me ƙoƙarin kamo hannunta. Jitayi gabanta ya faɗi, tsorone ya kamata don gaba ɗaya tunaninta ya bata cewa Pharouk ne ya kuma dawowa. Haka tabi Oummu jikinta asanyaye, suna sauƙa daga kan steps ɗin Oummu ta miƙo mata wani tray wanda samansa ke ɗauke da kayan fruits. “Ungo ki kai masa tun ɗazu ke yake jira yace yana sauri zai koma”
Jikinta na rawa haka ta amshi tray ɗin ta fice daga cikin falon, ƙirjinta na dukan uku uku haka ta nufi ɓangaren da zai sadata da falon Abba. Ahankali taturo ƙofar falon bakinta ɗauke da sallama ta kutsa kanta ciki, tarwal idanunta suka sauƙa akansa, koda wasa bata taɓa tunanin ganinsa awannan lokacin ba, muryarta narawa tace “Baba!!” murmushi Malam Garba yayi tare da yi mata alama da hannunsa akan taƙaraso, da sauri ta ƙaraso cikin falon tare da ƙarasowa gabansa ta aje tray ɗin, idanunta ne suka kawo ƙwalla cikin muryarta dake rawa tace “Baba sannu da zuwa!”
“Yauwa Zieyaderh sannu ya makarantar?”
“Alhamdulillah!” tafaɗa asanyaye tana me kallon mahaifinnata.
Ganin haka yasanyashi sakin murmushi tare da sanya hannu ya dafa kanta, cikin kulawa yace “Kina mamakin ganina ko Ziyaderh? karkiyi mamaki ni mahaifinki ne kuma ina ƙaunarki amatsayinki na tilon ƴata, haƙiƙa nasan banzama mai kyautawa agareki ba, duk irin abun da nayi miki banyi miki shi ason raina ba, nakuma ɗauki hakan amatsayin ƙaddara da babu wanda ya isa ya guje mata, kiyi haƙuri ki yafemin Zieyaderh haƙiƙa na cutar da rayuwarki na bari kinyi rayuwa cikin wahala da rashin gata, nasan ban kyauta miki ba amatsayina na mahaifi agareki….” Kuka tasanya me sauti tare da kifa kanta akan ƙafafunsa kana ta sanya hannayenta duka biyu ta rungume kafafun nasa, wani irin kuka takeyi mai ban tausayi yayinda agefe guda kuwa wani irin nutsuwa ke shiga zuciyarta.

“Nibakamin komai ba Baba, kaine zaka yafemin, duk da cewa bansamu ƙauna daga gareka ba, amma baka koyar dani tarbiyan banza ba, na saɓa tarbiyana na gudu na barka batare da neman izininka ba, kayi haƙuri Baba kayafemin!!” Tafaɗa tana kuka sosai. Idanunsa ne suka cika tab da ƙwalla ahankali ya ɗago kafaɗunta cikin son ya rarrasheta yace “Nayafemiki Zieyaderh, najima da yafemiki Allah yayi miki albarka, kema kuma inaso kiyafemin haƙƙin ki dake kaina wanda bansauƙe miki shi ba!”
Hawayen dake gudana akan fuskarta ta share tare da yin murmushi cikin jin daɗin ganinta gata gashi tace “Najima da yafe maka Baba!”
Murmushin jin daɗi shima yayi tare da shafa kanta cikin soyayya irin ta ɗa da uba yace “Allah Yamiki albarka!” da “Ameen” ta amsa tana murmushin jin daɗi, kamar ba itace tagama kuka yanzu ba, tray ɗin da ta shigo dashi ta miƙo mai tare da cewa “Baba kasha fruit” Murmushi yayi tare da girgiza mata kansa cikin halin dattako irin nashi yace “A’a Zieyaderh naƙoshi, bakiga har abinci sun kawomin ba!” yafaɗa yana meyi mata nuni da kulolin dake jere saman table. Cikin jin daɗi Zieyaderh tashiga bubbuɗe kulolin wanda aka shaƙe cikinsu da abinci na alfarma. “Baba to ai bakaci ba!” tafaɗa aɗan shagwaɓe tana kallonsa. Murmushi yayi tare da cewa “Dawo kizauna kusa dani” cikin jin daɗin sabuwar kulawan da tasamu daga mahaifinnata ta dawo ta zauna akusa da ƙafafunsa.
“Zieyaderh” yaƙira sunanta cikin kulawa.
“Na’am” ta amsa masa tana me dubansa.

Gyara zamansa yayi tare da cewa “Nasan ko ada can baya ke me hankali ce da nutsuwa, sannan kuma ke yarinyace me biyayya, bansan ko akwai soyayya atsakaninki da wanda ake ƙoƙarin haɗaki aure dashi ba, amma haƙiƙa na amince da karamci da kuma mutumci irin na waƴannan mutanen, saidai kuma duk da haka bazan yi gaggawan yin gaban kaina ba, duk da cewa na amince musu batare danaji ta bakin ki ba, sannan sun kawo sadaki suna me neman asanya musu lokacin aure amma banyi musu na’am ba nadaice su bani nan da kwana huɗu, bazan hanaki abun da kikeso ba Zieyaderh, bakuma zan tilastaki yin abun da bakya so ba, idan har bakyason aurennan karkiji ɗar ko shakka ki sanar dani, nikuma zan maida musu da sadakin su zan kuma basu haƙuri”
Shiru tayi tare da sunne kanta ƙasa, wasa da hannayenta tashiga yi cikin sanyin daya zame mata sabo tace “Na’amince musu Baba!”
Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa cike da tausayin ƴartasa yace “Allah yamiki albarka Zieyaderh, tashi kije idan yaso sai ki sanar da Ummantaku ni zan wuce!” “To” tace dashi asanyaye kana ta miƙe tsaye tana cewa “Baba kaɗanci abincin ko kaɗanne dan Allah!” murmushi kawai yayi harta fice bai sake ceda da ita komai ba. Zieyaderh kuwa tana fita daga cikin falon aɗan corridor ɗin dake barandar falon ta tsaya, bayanta ta jingina da jikin bango tare da sanya hannu ta sharce hawayen daya silalo kan ƙuncinta, kanta ta girgiza tare da ɗan cije laɓɓanta, ita kaɗai tasan meke zuciyarta,wanda bazata kuma iya furtawa kowa ba, gefen mayafinta tasanya ta goge idanunta sosai sannan ta nufi ɓangaren Oummu. Afalo ta samu Oummu hakan yasa ta ɗan rusuna tare da gaya mata saƙon Baban nata, murmushi Oummu tayi tare da miƙewa tsaye mayafinta ta ɗauka kana tafice daga falon, Zieyaderh kuwa kitchine ta wuce inda ta haɗawa kanta tea, domin ayanda take batajin wani abu bayan tea zai iya samun gurbin zama acikinta.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 3

SOORAJ CHAPTER 5