in

SOORAJ CHAPTER 2

SOORAJ CHAPTER 2

Ziyada kuwa komawa ɗaki tayi, tayi kwanciarta, harta fara bacci ta tuno cewa wulaƙanta abinci ba kyau, hakan yasa ta fito saɗaf saɗaf kan dinning ɗin ta nufa, abincin yana nan kamar yanda ta ajiye sa, ɗaukan kulan tayi ta fice daga cikin falon, direct wajen maigadi ta nufa nan ta sameshi zaune shida Kamalu driver suna hira, kulan abincin ta basu, duk da basusan menene aciki ba saida sukayi mata godiya, ita kuwa ta juya ta koma ciki. Zama Kamalu driver da maigadi sukayi, suka ci shinkafa da miyan, sam basuji wani abu na’alamar rashin daɗi acikin abincin ba, haka suka ci abincin sukayi nak.

STORY CONTINUES BELOW

*** ***

Washe Gari.

Tun kafun 7 yau ta kammala shirinta bayan tayi wankan tsarki, saboda tun jia da yamma bata ga komaiba, hakan yasa taji ajikinta cewa ta samu tsarki. 7 nayi suka bar gidan.
Zuwanta yayi daidai da zuwan Nasmah, nan suka zauna suka soma taɓa hira kafun Shukra tazo….

*** ***
Bayan sati biyu.

Alhamdulillah. Ayanzu sosai Ziyada take gane karatun da ake koyar musu, duk da cewa turanci har yanzu yana bata wahala, sannan kuma bata iya wani abu sosai daga cikinsa ba, amma duk da haka sosai take gane karatun, saboda kullum idan malami yazo yayi musu lecture yana fita Nasmah zata ƙara fahimtar da ita, yau suke shirye shiryen farayin test don haka daren jia, kusan kwana tayi tana biye karatun Maths ɗin da akayi musu, tun daga zuwanta har kama daga wanda akayi batanan, duk Nasmah tayi ƙoƙari wajen ganin ta koya mata.

Sunyi test ɗinsu lafiya, inda ko wanne ɗalibi dake cikin ajin yake sa ran cinyewa, ita ma Ziyada tayi ƙoƙari ƙwarai, domin kuwa acikin guestions huɗu da akace su amsa, ta samu ta amsa uku, kuma aranta tana sa ran cewa zataci duka ukun. Koda aka raba musu paper’n test ɗinnasu, ta samu six ɗayan da batayi ba kuwa tasamu zero, domin dama shine keda yawan maki har 4 mark yake dashi, duk da haka ma taji daɗi sosai.

Kwana biyunnan gaba ɗaya basu da wani hutu ko acikin school, kullum cikin karatun test suke ga exams ɗinsu dake ta gaba towa, kasancewar exam ɗin third term ne, shi zai kaisu s.s 2, hakanne yasa gaba ɗaya hankalin ɗaliban dake cikin school ɗin atashe yake, domin kuwa matuƙar bakaci exam ɗin ba, to fa repeat ɗinka za ayi babu ruwansu dakai ɗan waye. Ɓangaren Ziyada kuwa abun ya haɗe mata sosai, domin kuwa ta dage tana koyan karatun da akayi baya kafun ta shigo, ga kuma wanda akeyi musu yanzu hakanne yasa gaba ɗaya brain ɗinta ta ɗauki charge, saidai kuma cikin ikon Allah da kuma tsananin nacin da tasanya aranta karatun yana zama akanta. Ayanzu kwata kwata ta daina haɗuwa da Sooraj, bata sanin fitarsa bata kuma sanin dawowarsa, duk da kuwa tsananin son ganinsa da take, amma hakan baya samuwa agareta. Agajiye ta ɗaura kanta akan kafaɗan Shukra wacce take ta faman latsa babbar wayarta. Ɗan kallonta Nasmah tayi tare da cewa.
“Badai kin gaji da karatun ba?”

“Nagaji mana Nasmah, zan bari sainaje gida kawai naci gaba!”

“Amma kinsan fa Monday zamu fara exam ko?” Shukrah tafaɗa tana me maida wayarta cikin jaka.

Murmushi Ziyada tayi tare da cewa “Har kingama shan soyayyan?”

Hararanta Shukrah tayi tare da cewa “Nifa wallahi kunsamin ido, hmm kawai don bakusan daɗin soyayya bane ba shiyasa”

“Daɗi? hmmm ina daɗi acikin wannan abar da kullum sai anbata miki rai? wallahi Shukra inaganin kawai wahalar dakanki kikeyi, s.s one kaɗai fa muke, amma wai ace ke har soyayya kike hmmm Allah ya kyauta!” Nasmah tafaɗi haka tana ɗan taɓe bakinta, ita sam wannan tsarin na soyayya baiyi mata ba, saboda ita atsarinta idan zatayi soyayya tafiso sai taje irin 2 hundred level ɗinnan.

“Hmm kwata kwata bazaki gane ba Nasmah, amma kema watarana nasan zakiji abun da nakeji!” Shukrah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin tashi tsaye daga zaunen da take.

“Ba abun da zan gane!” Nasmah tafaɗi haka cike da jin haushi.

Murmushi Ziyada tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, haka nan tunaninsa ya faɗo mata arai, jitayi gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kallonta Shukrah tayi tare da cewa. “Muje ki rakani kinji share wannan abar” Still murmushi kawai tayi sannan tabi Shukrah suka tafi, Nasmah ma binsu tayi tace bazata zauna ita kaɗai ba, direct ɓangaren da ake koyar da girke girke dake cikin makarantar suka nufa, ƴan department ne dayawa awajen kowa yana baje basirarsa, gani tayi Nasmah tashiga itama ansoma bugawa da ita, tsayawa tayi daga gefe tana kallonsu, dukkan abun da sukeyi tana haddace shi akanta, sunjima awajen kafun suka koma class.

Koda ta koma gida gaba ɗaya bata wani samu sukuniba karatu ta dinga yi, har wayewar gari ta shirya tatafi makaranta, acikin ƴan kwanakinnan wani abu da ta fara fuskanta shine sauyawar da jikinta yasomayi, hips ɗinta ne taga sun ƙara faɗi, yayinda ƴan saffa saffan breast ɗinta suka ɗan ƙara girma, skin ɗinta ta sauya tayi wani fresh, ga kyawun da fuskarta take ƙarawa ako da yaushe, ita kanta sau da dama idan ta kalli kanta takanyi mamakin yanda kamanninta ke ƙara sauyawa. Tun ɗazu su Nasmah suka fita break suka barta, kasancewar bata ƙarasa note ɗinta da wuri ba, miƙewa tsaye tayi bayan ta kammala note ɗin, maida littafinta tayi cikin jaka tare da ficewa daga cikin ajin.

Wata haɗaɗɗiyar mota ƙirar benz ce ta kunno kai cikin makarantar. Adai dai kusa da parking space ɗin makarantar yayi parking motar, buɗe murfin motar yayi tare da zuro ƙafafunsa waje, cikin yanayinsa na nutsuwa yafito daga cikin motar, haɗaɗɗen saurayine mai kyau da gayu, ba fari irin tas ɗinnan bane, amma yana da nasa irin salon hasken, direct idan ka ganshi zaka ƙirasa da mai kyau, kasancewar babu laifi shima yana da nashi kyau’n, irin Handsome guy ɗinnan ne mai son ado da gayu, dogone amma basosai ba sannan yana da ɗan faffaɗan jiki, yana da wani kwantaccen sajen da yaƙarawa fuskarsa kyau, sanye yake da riga da wando na jeans masu kyau, yayinda ya rufe gashin kansa da facing cap blue colour. Cikin isa yake takunsa yana mai ɗan kaɗa key ɗin motarsa dake riƙe a hanunsa, direct office ɗin principal ya nufa. Ta baya baya take tafiya tana dariya yayinda Nasmah ke biyota da ɗan sauri sauri, ɗan juyawa tayi sam bata ankara ba, saiji tayi ta bugu da mutum yayinda kanta ya daki ƙirjin mutumin da ta buge, da sauri ta juyo tare da sanya hanu ta dafe goshinta cikin yanayi naɗan jin zafi tace. “Auchhh!!” Shima hanu yasanya ya dafe ƙirjinsa, daidai saitin inda kanta ya buga.

Ɗan zame hanunta tayi daga kan fuskarta, idanunsune ya sarƙe cikin na juna, ɗan matsawa baya tayi tare da sake kallonsa.
“Kayi haƙuri dan Allah bankula bane!” tace dashi cikin murya mai sanyi. 1

Murmushin daya bayyana dimples ɗinsa yayi mata tare da cewa. “Babu damuwa!” shima cikin sanyi yayi maganar, yana mai ɗan ƙara faɗaɗa murmushin dake kan fuskarsa. Raɓawa tayi taɗan gefensa ta wuce, Shukrah da Nasmah suka bita abaya. Kafeta da sexy eyes ɗinsa yayi har saida yaga shigarta class sannan ya ɗauke idanunsa, sannan ya juya ya nufi inda zashi. 2

Har ta zauna akan sit ɗinta tana dafe da goshinta, don taji zafin buguwar da tayi baɗan kaɗan ba.

Dariya Shukrah tayi tare da cewa “Wai miye hakan kike dafe da goshi sai kace wanda kika bugi dutse?”

“Ai inajin da dutse da shiɗin basu da maraba!” Ziyada tafaɗi haka tana mai ɗan mulmula goshinta.
Dariya su Nasmah suka sanya. “Dole zakiji zafi mana, daganinsa ai zaki san ma’abocin yin gym” Shukrah ta faɗi haka tana mai ƙoƙarin murzawa Ziyada goshinta. Malami ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka nutsu, tare da maida hankalinsu kansa. Kwana biyunnan duk ba atashinsu da wuri yau har 5:30 sannan aka tashesu.
**
Tana shiga cikin ɗakinta ta soma rage kayan jikinta, banɗaki ta shiga tayo wanka. Riga da sket ƴan kanti ta sanya sannan taɗan yafa wani ɗan ƙaramin ɗan kwali akanta. Direct kitchine ta wuce, duk wasu ƴan ƙananan girki yanzu babu abun da bata iyaba. Indomie ta dafa bawai don tanaso ba saidon yunwan dake damun cikinta. Gaba ɗaya kwanukan da suka ɗan yi ƙura a kitchine ɗin ta kwashe ta kai gaban sink wankesu tayi tas, sannan tayi mopping kitchine ɗin. Acikin kitchine ɗin ta zauna taci abincinta, tana gamawa ta wanke plate ɗin data ɓata. Zame ɗan kwalinta tayi ta ƙarasa gaban sink, hanu tasa ta tari ruwa ta wanke fuskarta, tana maiƙoƙarin ɗaura ɗan kwalin tanufi hanyar fita daga kitchine ɗin, harta jefe ƙafarta na hagu acikin falon, da wani irin ƙarfi taji an jawota cikin kitchine ɗin tare da sanya hanu aka rufe mata baki gam.Numfashinta ne yasoma ƙoƙarin ƙwacewa, saboda tsabar tsananin tsoron da ta samu kanta aciki, ƙasa tayi da idanunta, tana me kallon hanun da aka rufe mata bakinta dashi,

hanun namiji ta gani, wanda ke ɗauke da kwantattun gargasa da sukayi luf akan farar fatarsa, jikinta ne ya ɗauki tsuma, wani irin tsoro mai ƙarfi ya ziyarceta, wani ɗan corridor dake cikin kitchine ɗin ya shiga da ita, ɗan sassauta riƙon da yayi mata yayi, ba tare da ya sake mata bakinta ba, ya juyo da ita suka zama suna fuskantar juna, idanunta ta zaro waje tana me sake kallonsa. Sake mata bakinta yayi, tare da ɗaura hanunsa akan laɓɓansa cikin ƙasa ƙasa da murya yace.
“Shiii!! kada kimin ihu, ina da baƙi a falo ki zauna anan kada ki fito” yana gama faɗan haka ya saketa, tare da juyawa ya nufi hanyar fita daga cikin kitchine ɗin, bakinta a wangale haka ta bisa da kallo har ya fice, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da jingina bayanta da jikin bango, har acikin zuciyarta tayi bala’in tsorata, duk atunaninta wanine daban yazo saceta, hanunta ta ɗaura adaidai kan chest ɗinta dake ta bugawa da ƙarfi, aƙalla takusan mintuna 9 ahaka, kafun tasamu ta iya daidaita nutsuwarta, kan wani plastic chair dake cikin kitchine ɗin ta zauna, tare da kifa kanta akan cinyoyinta. 3

Shikuwa Sooraj yana barin kitchine ɗin, komawa cikin falo yayi, wajen abokan business ɗinsa, da suka kawo masa Ziyara, yana zaunene amma gaba ɗaya hankalinsa naga ƙofar kitchine, sam bayaso tayi gangancin fitowa, ba tsoronsa ganinta da zasuyiba, tsoronsa shine wani irin bahagon kallo za suyi masa? tabbas ba lallai suyi mishi kyakkyawan zato ba, shikuwa ko kaɗan bayason ayi masa irin wannan kallon. Sunjima suna tattaunawa akan business ɗinsu, kafun daga bisani sukayi masa sallama, har bakin motarsu ya rakasu, shima daga rakiyarsu bai dawo cikin gidanba, motarsa ya shiga ya fice daga gidan gaba ɗaya. 1

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 3