in

SOORAJ CHAPTER 2

SOORAJ CHAPTER 2

STORY CONTINUES BELOW

Cikin sauri sauri ta zura kayan uniform ɗinta, safa’nta ta sanya tare da ɗaukan school bag ɗinta, duk da batasan ƙarfe nawa bane yanzun, amma tabbas da dukkan alama yanda taga rana ta bayyana raɗau tasan tayi latti, fitowa falon tayi tana mai ƙoƙarin cusa wani littafi dake hanunta acikin jaka, sam bata lura dashi ba kasancewar bata kawo ma aranta cewa zata ganshi ba.

“Ina zakije?” muryarsa ya doki dodon kunnenta, cak ta tsaya daga tafiyar da takeyi, tare da dawo da kallonta zuwa inda taji sautin muryar ta fito.
Zaune yake akan dinning table yasha kyau cikin riga da wando na suit amma baisanya suit ɗin ba, sai dai tana aje agefensa, parking shirt ne ajikinsa Navy blue colour wanda ta ƙara masa kyau. Cup ɗin tea ne ahanunsa yana sha da kaɗan kaɗan.

Bazata iya jure kallonshi ba, saboda sosai yake mata kwarjini. “Dama zanje makaranta ne!” tabashi amsa cikin muryarta mai sanyi.

Shiru yayi kamar bazai amsa mata ba, sai kuma ya ɗago kansa yaɗan kalleta. “Zokici abinci!” yace da ita ataƙaice.

Duk da tasan cewa tayi latti, amma bazata taɓa iya faɗa masa hakan ba, batasan tayaya zata iya fara zama tare dashi ba, amma ya zatayi? Ƙarasawa gaban dinning ɗin tayi tare daɗan durƙusawa. “Ina kwana!” tace dashi cikin sassanyar murya.

Kansa kawai ya kaɗa mata batare da ya amsa ba, aɗaɗare ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun dake dinning table ɗin. Food flask da kuma plate ɗin dake gabanshi ya turo mata, kana ya cigaba dashan tea ɗinsa, wayarsa ya ɗauka yasoma latsawa. Buɗe food flask ɗin tayi ta ɗan ɗibi abincin kaɗan, gaba ɗaya ta kasa sakewa taci abincin, jin kanta take atakure, duk abun da takeyi yana lure da ida ta gefen idanunshi, miƙewa tsaye yayi tare da ɗaukan suit ɗinsa ya sanya.

Saida ya ɗanyi tafiya kaɗan sannan ya tsaya, batare da ya juyo ya kalleta ba yace.
“Yau bazakije school ba kizauna agida” Baijira abun da zata ce ba yayi gaba abunsa.

Bata ɗauke idanu akanshi ba har saida yafice daga cikin falon.

“Yau bazakije school ba ki zauna agida”
Tamaimaita abun daya faɗa cikin ɗan nazari, kenan yana nufin tazauna agida kada taje makaranta? Babu mai amsa mata, hakan yasa ta ci gaba da tsakalan abincin. Bata wani ci abincin sosaiba tatashi ta koma ɗaki, uniform ɗinta ta cire sannan ta dawo falo ta zauna, ƙurawa tv idanu tayi tana kallon yanda ake koyar da girki.

***

Shikuwa yana fita daga falon direct wajen lafiyayyar motarsa ƙirar Range Rover Blue colour ya nufa, yana shiga Kamalu driver yaja suka fice daga cikin gidan. Yau meeting suke dashi a Transcop hilton saboda haka direct can suka wuce. Tun ƙarfe 9 da suka shiga meeting ɗin basu suka fito ba sai 11 daganan yawuce office.

Ziyada kuwa dake zaune agaban tv, duk wani abu da ake koyarwa na girki taɗaukeshi tsab akanta, hatta abun da tagani jiya a kitchine wani mai kamar kofi,(Blender) yau taga yanda ake amfani dashi, ashe abun markaɗe ne ita bata sani ba, suna gama koyar da girkin, suka sako wani film shine abun daya ƙara ɗauke mata hankali. Ba itane ta tashi agaban tv’n ba harsai bayan sallan Azahar. Kitchine ta shiga cike da karambaninta yau taci alwashin sai tayi girki. Ruwa ta zuba atukunya cike da karambani ta kunna gas, duk abun da taga sunyi acikin tv’n ta riƙeshi yana kanta, ruwan na tafasa ta wanke shinkafa ta zuba, fridge ɗin dake cikin kitchine ɗin ta buɗe ta ɗibi kayan miya, saida ta wankesu sannan ta ɗauko irin abun da taga sunyi markaɗe aciki gaba ɗaya kayan miyan ta juye acikin blender tare da ɗaukanshi can ca ɗak takaishi gaban socket, kamar yanda taga sunyi haka itama tayi ta jona sa ajikin socket, ƙaran da taji yayi kaɗai saida ya kusa fasa mata ƙirji, don baka ɗan ba ta tsorata, can gefe ta koma tana ganin ya markaɗu ta siɗaɗo da ƙyar ta iya kashe socket ɗin, duba shinkafarta tayi taga ta nuna, haka ta sauƙe shinkafar batare da ta kashe gas ɗin ba, da sauri sauri ta juye markaɗen acikin wata tukunya sannan tasanya mangyaɗa akan markaɗen don ita agarinsu haka suke miyansu. Baƙaramin jimawa tayi ba kafun ta samu miyan ya soyu mata, hmmm nan akeyinta sam batasan me zata sanyawa miyan don kashe mata tsami ba, haka ta zuba kayan haɗi ta rufe miyar, mintuna kaɗan ta kashe gas ɗin lokacin miyar tayi, komawa ɗakinta tayi tayi wanka, wata doguwar riga blue colour ta sanya mai kyau, rigan irin arebian gown ɗinnan ce, sosai ta amshi jikinta, zuciyarta fara tas ta nufi kitchine ɗin, daɗi takeji yau zataci abincinta, bata taɓa mantawa awasu lokuta da dama a ƙauye idan tayi girki babanta yaci yakan yaba girkin sosai, sannan ita kanta Inna Ma’u idan tanacin girkin har santi take, hakanne ma yasa aka sallama mata gaba ɗaya girkin gidan. Food flask ta ɗauka ta juye shinkafan aciki, sannan ta ɗauki plate ta zuba nata, miyan ma juyeshi tayi acikin wata kula gaba ɗaya kulolin takaisu kan dinning table ta ajiye..

Akan sofa ta zauna tare da ɗan ƙwashe ƙafafunta, cikin ɗari ɗari takai loman farko na abincin bakinta, saboda atunaninta miyan tayi tsami sosai, sai dai kuma koda taci abincin, ga mamakinta sai taji miyar batayi wani tsami sosai ba, hasalima mutum zai iyaci hankalinsa kwance. Sosai taci abincin tana kammalawa ta je kitchine ta wanke plate ɗin. Dawowa falon tayi ta zauna, tana zama tajiyo ƙarar horn ɗin motarshi, tashi tayi da sauri ta tafi jikin window ta ɗan leƙashi, yatsun hanunta tashiga murzawa aranta tana cewa.

“Allah yasa ya yarda yaci abincinnata”Tsaye take ajikin window tana mai jiran shigowanshi, amma kuma sai dai ga mamakinta har anshare sama da mintuna 10 baishigo cikin falon ba, sake gyara tsayuwanta tayi, tare da soma murza ƴan yatsun hanunta. Buɗe ƙofar falon yayi ya shigo, yana mai ƙoƙarin cire suit ɗin dake jikinshi, idanunsa ne suka sauƙa akanta, amma saiyayi saurin kawar da kanshi gefe, tare da ƙarasawa cikin falon, aje suit ɗinnasa yayi akan kujera tare da cire agogon dake ɗaure atsintsiyar hanunshi, gaban fridge yaje tare da buɗewa ya ɗauko goran ruwa, ɓalle murfin yayi tare da kaiwa bakinsa, saida ya tabbatar da cewa babu komai acikin goran, sannan yayi wurgi da goran cikin dustbin, dawowa cikin falon yayi ya ɗauki suit ɗinshi kana ya nufi hanyar bedroom ɗinsa, gaba ɗaya ma yi yayi kamar baisan da zamanta acikin falon ba, tana ganin shigewarsa cikin ɗaki. Ta saki wani gauron numfashi, sam bazata iya yi masa magana ba, kwarjininsa ya wuce gaba ɗaya tunaninta, sumu sumu haka ta wuce tayi ɗakinta.

Kwance yake acikin jakuzzie ɗinsa, wanda yasha haɗaɗɗen ruwan wanka, daga kan ƙafafunsa zuwa ƙirjinsa, gaba ɗaya lume suke acikin ruwa, kansa da hannayensa ne kawai suke waje, yayinda kyawawan idanunsa suke alumshe, kana ya ɗan jingina bayan kanshi da jikin jakuzzie’n, gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya tare dashi, sam kwana biyunnan baya cikin wata gamsashshiyar nutsuwa, tunani da damuwa sune abun da suka sakoshi gaba, akullum kuma ako wacce rana jin kansa yake tamkar wani baƙon halitta, ya sani acikin rayuwarshi akwai tawaya sosai, amma kuma baison ya zamanto mai rauni saboda hakan, baiso yazama ɗaya daga cikin irin mutanennan da basa iya riƙe damuwarsu, shikansa ya sani da ace lafiyarshi ƙalau, to da bazai taɓa iya kai wannan lokaci mai tsawo haka, batare da mace akusa dashi ba, “Menene matsalarsa? mecece damuwarsa? meyasa baya iya zama da mace?” yasan duk waƴannan abubuwan iyayensa suna da buƙatar sani, “Amma mai yasa basa tambayarsa?” wannan tambayar shi ne abun da yake tambayar kanshi akullum, baikamata don ya kasance Namiji su sakar masa ragamar rayuwarsa ba, duk da cewa ya girma amma tabbas yana da buƙatar kulawan Iyaye atare dashi.
Wani numfashi yaja tare da fesarwa alokaci guda, wani irin tausayin kanshi yakeji, sosai yake tausayawa al’amuranshi, baisan taya zai dubi wata mace yace yana sonta ba, haka kuma baisan wace macece zata iya zama ta jure lalurar shi ba, bazai taɓa yaudaran kanshi ba, saboda yasan babu wata mace da zata iya jure zama dashi ayanda yake, musamman ma idan tasan ƙatuwar matsalan dake tare dashi, yasani shi me raunine ako da yaushe, safe, dare, rana, babu wani lokaci da zaizo masa yana cikin farinciki da walwala, sau da dama yakanji kamar yayita kuka, ko da zai samu salaman rage ƙuncin dake cikin zuciyarshi, saidai hakan baya samuwa ayanzu, sakamakon zuciyarsa da tayi tauri, haƙoransa yasa ya ɗan ciji laɓɓansa da ƙarfi, shi kaɗai yasan me yake ji, haka kuma shi kaɗai yasan kalan ƙunci da yake ciki, sama da shekara 10 kenan da haske ya gujewa rayuwarsa, azahiri acikin haske yake rayuwa, amma kuma idan aka duba bayansa duhune dulum mai wuyar kalluwa. Cikin rashin kuzari haka yayi wanka, tare da ɗauro towel akan waist ɗinsa ya fito daga cikin toilet ɗin.
Zama yayi akan gado tare da ɗauko mayinsa ya soma shafawa, yana kammalawa ya feshe jikinsa da body spray mai daɗin ƙamshi. 3 guater jeans and white t-shirt ya sanya, laptop ɗinsa mai ɗauke da tambarin apple asaman murfin ya ɗauka, tare da ficewa daga cikin ɗakin. Aje laptop ɗin yayi akan rug tare da buɗe fridge ya ɗauko goran pepsi mai matuƙar sanyi. Zama yayi akan rug ɗin, tare da tanƙwashe ƙafafunsa, buɗe laptop ɗinshi yayi ya soma gudanar da aikinsa kamar yanda ya sabayi akowacce rana.
**

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 3