in

SOORAJ CHAPTER 2

SOORAJ CHAPTER 2

Tare suka shigo ajin ita da Nasmah, Nasmah ne ta ciro littafin Maths ɗinta, ahankali ta shiga yiwa Ziyada bayani dalla dalla da Hausa yanda zata fahimta, abun mamaki kuma sai gashi ta ɗan gane wasu abubuwan, tana kammala koya mata Maths ɗin ta ɗauko Biology shima ta koya mata, aikuwa harma tafi gane Biology’n akan Maths ɗin, kasancewar shi baida lissafi, bakamar Maths ba, har subject ɗin da akayi musu na ƙarshe kafun break wato Agric science saida Nasmah ta koyawa Ziyada, Alhamdulillah kuma ta fahimta sosai, akuma ɗan lokaci ƙanƙani wata ƴar shaƙuwa ta shigo tsakaninsu da Nasmah, duk abun da sukeyi Shukrah na jinsu, amma ƙala bata ce musu ba, saima wata fakekiyar wayarta data ciro ta soma latsawa. Suna kammala karatun aka dawo break.

Sosai suke shan karatu basu suka samu kansu ba sai ƙarfe 1 na rana nan ma sallah aka fito dasu. Nasmah ne ta jata suka nufi masallacin dake cikin school ɗin, Nasmah saida ta jirata tayi alwala sannan itama tayi, atare suka shiga cikin masallacin nan suka iske Shukrah tana sallah, gefe suma suka samu suka tada nasu sallan, suna idarwa Nasmah ta sake kama hanun Ziyada suka fito daga cikin masallacin. Aji suka koma kowa yaciro abincinsa yafara ci, ita dai da bata da wani abinci sai snacks shi ta ciro ta ɗanci kaɗan, Nasmah ce tayi mata tayi’n soyayyen doya da naman kaza wanda tazo da shi, amma sam taƙi ci babu yanda Nasmah batayiba akan taci amma taƙi dolenta ta haƙura.

5:00 pm daidai shine lokacin tashinsu akowacce rana, yauma biyar na cika dai dai aka kaɗa ƙararrawan tashi. Tare da Nasmah suka fito tana fitowa ta hango Kamalu driver tsaye ajikin mota, sallama tayiwa Nasmah da Shukrah sannan tanufi inda yake tsaye.
Tana shiga yaja motar suka bar haraban makarantar.

Tana shiga cikin falon, daddaɗan ƙamshin turare ya daki hancinta, ko ina na falon a gyare yake tsab. Ƙofar ɗakinsa ta kalla, sannan ta wuce ɗakinta. Tana shiga ta soma cire kayan uniform ɗinta, ban ɗaki ta shiga ta yi wanka, yanzu babu abun da bata iya amfani dashi ba na cikin banɗakin.

Tana fitowa awanka ta sanya kaya haɗe da faɗawa kan gado, ajiyar zuciya tashiga sauƙewa akai akai, wani irin gajiya haɗi da bacci takeji, basaban ba, idanunta ne suka sauƙa akan wani ƙaton akwati dake aje cikin ɗakin. Tashi tayi ta nufi inda akwatin yake tana buɗewa taga kayane shaƙe acikin akwatin, kama daga kan dogin riguna riga da sket ƴan kanti, da kuma dogin wanduna, murmushi tayi haɗe da lumshe idanunta, batasan da wani baki zata gode masa ba, amma tabbas Ya Zama MADUBI acikin rayuwarta, da sannu itama zata haskaka ta zama kamar wata TAURARUWA. Komawa tayi ta kwanta cike da ɗokin sababbin kayan da tayi masu yawa. Jin anata ƙiraye ƙirayen sallan Magriba ne yasa tatashi ta shiga toilet ta ɗauro alwala bata tashi akan sallayan ba saida ta yi sallan Isha, tana gama naɗe sallayan da tayi sallah akai, ta faɗa kan gado, wani irin baccine ke fusganta, tana kwanciya kuwa bacci ya ɗauketa ko lufayan dake jikinta bata cire ba.

Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa abun yaci tura, kwance yake akan makeken Royal bed ɗinsa wanda yaji lallausan bedsheet. Idanunsa dake alumshe ya buɗe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa dake wani irin sara masa kamar zai faɗo ƙasa haka yakeji. Gaba ɗaya duniyar bata yi mashi daɗi, ƙuna yakeji acikin zuciyarsa abubuwa da yawa ne suka haɗe masa, hanunsa na dama ya sanya akan cikinsa wanda ke ɗauke da manya manyan 6 packs, ahankali ya ke murza fatan cikinsa, idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jajur dasu. Cigaba yayi da murza fatar cikinsa da ɗan ƙarfi haɗe da cije laɓɓansa. “Sai yaushe ne zai zama mutum me cikakken lafiya? sai yaushene zai san cewa shima Namiji ne? yaushe ne damuwarsa zata gushe? yaushe ne zaiyi bacci acikin farinciki da nishaɗi? yaushene zaiji abun da yake buri da fatan ji watarana? Abun tambayar aransa shine yaushe ne yazama haka? yaushe ne kuma zaici wannan jarabawar tasa mai wahala?” waƴannan tambayoyin su yakeyiwa kansa akullum, sau tari yakan cire rai amma yasan Allah na sane dashi idan yana darai watarana zai dace, amma kuma yaushene wannan ranan zata zo? shine abun da baisani ba, tashi yayi ya zauna still hanunsa nakan fatar cikinsa yana murzawa. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon, gaban window ɗinsa ya nufa, tsayawa yayi ajikin window’n haɗe da sanya hanu ya yaye labulen window’n, buɗe glass ɗin window’n yayi take wata iska mai daɗi ta bugi fuskarsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, ɗaga kansa yayi yana kallon sararin samaniya, farin wata ne ya haske ko ina da ina. Ahankali ya kejin nutsuwa na sauƙar masa, sosai yakejin daɗin ni’imar dake hurawa, yajima tsaye ajikin window’n kafun ya dawo cikin ɗakin. Kwanciya yayi akan gado yayinda ƙafafunsa ke ƙasa, ahaka wani bacci ya ɗaukesa, dagani kasan bajin daɗin baccin yake ba.

** **

Tun 7 ta kammala duk wani shirinta, saboda ta fahimci ba aso azo late a makarantar, duk yanda ta buga sammako wajen fita, amma bata iske shi afalo ba, saidai ta iske daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, haka tashiga mota Kamalu driver yaja motar suka tafi batare da tayi tozali dashi ba.

Kamalu driver na tsaida motar ta ɗauki jakanta haɗe da soma ƙoƙarin buɗe murfin motar. “Ga wannan Oga yace abaki” Kamalu driver ya tsaidata tahanyar faɗan haka, yana mai ciro kuɗi acikin aljihunsa.

Kallon kuɗin tayi sannan ta kalli Kamalu driver. “Ni kuma mai zanyi dasu to?” ta tambaya cike da mamaki.

“Haka dai yace abaki, hala ko kuɗin taran ki ne” Kamalu driver yafaɗi haka yana me ƙara miƙo mata kuɗin.

Cikin sanyin jiki tasa hannu ta amshi kuɗin, sannan tafice daga cikin motar aranta tana mai cewa da zaran takoma gida zata tambayeshi, hala ko wani abu ya keso tasayomasa da kuɗin.

Yau ta riga Shukra da Nasmah zuwa saboda haka ita kaɗai ta zauna tayi jigum, ba wani jimawa sosai sai gasu sunzo atare, ga mamakinta yau fuskar Shukra asake take babu tsumewa kamar na jiya, Nasmah na ganinta ta saki murmushi haɗe da ƙarasowa ta zauna akusa da ita. “Yau munyi late kin rigamu zuwa” Inji cewar Nasmah dake ƙoƙarin sauƙe jakarta dake kafaɗarta.

Ta buɗe baki zatayiwa Nasmah magana kenan malami ya shigo ajin. Sai bayan yafita ne suka ɗanyi taɗi da Nasmah.. Yau dai sosai Nasmah tasake jawota jikinta ko ina zasu tare suke zuwa kuma Shukra na biye dasu saidai bata cika yawan magana ba. Hatta sallah yau atare sukayi su duka ukun. Ko da suka idar da sallan ma tare sukaci abinci wanda Shukrah ce tazo musu da jallop rice wacce taji ɗanyen kifi.

Yauma agajiye ta dawo daga school ɗin tana idar da sallah ta soma bacci.

*** ***
Yau kimanin sati guda kenan tana zuwa makaranta, Alhamdulillah yanzu kam tana ɗan fahimtan wasu abubuwa musamman da Nasmah ta dage da koya mata, acikin waƴannan kwanaki tayi sabo da Nasmah sosai, duk da cewa Shukra na shiga sha’aninta yanzu amma sunfi sabo da Nasmah, aduk tsawon kwanakinnan bata taɓa ganinsa ba koda sau ɗaya ne, saidai idan ta fito falo tana samun tsaraban ƙamshinsa dayake barmata akowacce rana.Kamar dai yanda kowa ya sani saturday ranar hutuce ga yawancin ɗaliban makarantar boko. To haka ranar yau ta kasance saturday wato (Asabar). Zaune take aƙasa ta tanƙwashe ƙafafunta, jakar makarantarta ne agabanta, sai kuma wani littafin English ɗin dake riƙe a hanunta, lecture’n da akayi musu jiya take dubawa, so take karatun ya zauna akanta sosai, don taji malamin nacewa wani sati zai basu Assignment. Tunda tayi sallah ta ke riƙe da littafi, gaba ɗaya hankali da nutsuwarta naga littafinta so take ta iya duk wani abu da aka koya musu, a yanda ta ba da himma ne yasa ta fahimci wasu abubuwa da dama, wato shi karatu ɗan naci ne idan kanace masa da yardan Allah Zaka iya, sannan zaka gane komai sannu ahankali, yarda da wannan da tayi ne yasa abubuwa da yawa dake cikin karatun da take suka zauna akanta. Yunwar da ta soma ƙwaƙulan cikinta ne yasa ta aje littafin haɗe da jingina bayanta da jikin gado, ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci, kasancewar daren jiya bata wani samu isashshen bacci ba, domin kuwa jiya ba tayi bacci da wuri ba, har sai wajen ƙarfe 12:30 na dare sannan ta kwanta, karatu tayi sosai, sannan gashi kuma yau tayi tashin sassafe sakamakon wani irin zazzaɓi dake ta sanɗanta tun jiya da rana, amma dayake zazzaɓin baiyi ƙarfi ajikinta ba hakan yasa bata jikkata ba.
***
Duk da cewa yau Asabar amma bayajin zai iya zaman gida, shi kansa yasan yana da buƙatar hutu amma kuma yasan ko ya zauna agida hutun nasa bazai samu yanda yakeso ba. Fitowarsa awanka kenan yana ɗaure da towel a ƙugunsa, sannan kuma ga wani ɗan ƙaramin towel still dake riƙe a hanunsa, yana tsane ruwan dake kansa. Yana gamawa ya ɗauko handryer, da shi yayi amfani wajen busar da gashin kansa, mayinsa mai ƙamshi ya shafa, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar dake kansa, mayukan gashi har kala uku ya shafawa kansa, take gashin kannasa ya ƙara bayyana sheƙi da kuma walwali. Dogon wandon jeans wanda ke ɗauke da zane irin na kayan sojoji ya sanya, wandon irin mai yawan aljihunnan ne sannan ƙasan wandon atsuke yake da rubber, wata farar t-shirt ya sanya ajikinsa, take kyawunsa ya sake bayyana sosai kayan suka amshi jikinshi, kasancewarsa namiji mai murɗaɗɗiyar surar jiki, gun ƴar ƙaramar drawer’n da yake aje drugs ɗinsa ya nufa, wani magani dake cikin sachet ya ciro, tare da ɓallan guda biyu ya watsa abakinsa, sannan yakora da ruwan swan. Hanunsa riƙe da goran swan ɗin ya nufi falo. +

Yana shiga cikin falon ya soma bin ko ina dake cikin falon da kallo, ko alaman datti babu acikin falon, hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas gyara falon akayi, duk da cewa dama babu wani datti acikin falon, amma dai kallo ɗaya zakayi kasan an gyara falon.

Kitchine ya wuce ya tafasa ruwan zafi acikin heater cup, yana gamawa ya juye a flask. Zama yayi akan dinning tare da haɗa tea ɗinsa. Sanya kofin tea ɗin yayi agaba ya kasa koda ɗauka ne yakai bakinsa, sai jujjuya spoon ɗin dake hanunsa yake acikin cup ɗin, yanayin yanda ya nutsu yayi shiru shine abun da zai baka tabbacin cewa tunani yakeyi. Tabbas kuwa tunanin yake, maganganun da mahaifinshi yayi mishi masu tsauri su suke damunshi, bai ɗauka fushin da mahaifannashi keyi dashi har yakai haka ba, bai taɓa tunanin suma zasuƙi fahimtarshi ba, maganan da Abbanshi yayi mishi akan cewa wai ya nemo matar aure ya aura, acikin ƴan ƙanƙanin lokaci idan ba haka ba kuma kada ya sake ƙiran wayanshi shine abun dake damunsa, tabbas hukuncin da Abbansa yayi mishi yayi tsauri da yawa, koda wasa baitaɓa tunanin zasu sake kawo mishi maganar aure nan kusa ba, ya ɗauka zasu fahimceshi a wuce wannan stage ɗin, ashe abun ba haka yake ba. Wayarsa dake gefensa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira, jikinsa a sanyaye ya ɗaga ƙiran tare da kara wayar akan kunnensa. 2

STORY CONTINUES BELOW

Mas’oud dake zaune acikin motarsa yace
“Gaye na shigo Abuja fa yanzu”

Cike da ɗan mamaki Sooraj yace

“Da gaske?”

“Bakayarda ba?” murayar dake cikin wayar Sooraj ne ta bayyana raɗau acikin falon, da sauri Sooraj dake zaune akan dinning ya kalli ƙofar falon.

Mas’oud yagani yana murmushi.

Murmushin da iya kansa leɓe Sooraj yayi tare da kashe wayarsa.
“Kai ɗan rainin hankaline Mas’oud” Sooraj yafaɗi haka yana me kallon Mas’oud dake takowa zuwa garesa.

“Ni ne ɗan rainin hankali, ko kuma nida kai ne dukanmu ƴan rainin hankali?” Mas’oud ya faɗi haka yana mai ƙoƙarin jawo wata kujera dake fuskantar wacce Sooraj ke kai ya zauna.

Still ɗan guntun murmushinsa yayi, haɗe da ɗaukan kofin tea ɗinsa ya ɗanyi sipping kaɗan.

“Sauƙar yaushe?”
ya tambayi Mas’oud.

“Banwuce 30 minute da sauƙa ba” Mas’oud yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin ɗaukan wani cup zai haɗawa kanshi tea, duk da cewa bawani damuwa da tea din yayiba kawai don yanajin yunwa ne ya sanya zai sha.

Ɗan sipping tea ɗin kaɗan yayi, tare da kallon Sooraj da yaketa aikin juya tea da spoon ɗin dake hanunsa, ya ɗan karanci damuwa akan fuskar Sooraj ɗin, amma da yake yasan kwanan zancen sai kawai ya share haɗe da cewa..
“Ya maganan waƴannan kayanne? kasanfa yanzu babu kaya aƙasa”

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe haɗe da cewa “Next week zanje USA zan taho dasu”

Kai Mas’oud ya jinjina cike da gamsuwa sannan yace.
“Amma baka karɓi ribanka na wannan month ɗin bafa”

Shiru yayi baice komai ba, aƙalla yaɗauki kusan 4 minute bai tankawa Mas’oud ba, ganin haka yasa Mas’oud yin murmushi kawai ya cigaba da shan tea ɗinsa.

Ganin bazai iya shan tea din bane yasanya shi miƙewa tsaye, yana ƙoƙarin barin wajen Mas’oud yace.
“Inason muyi magana dakai”

Komawa yayi ya zauna tare da ɗaukan wayarsa ya soma latsawa “Inaji!” yace ataƙaice.

“Aure nakeso nayi” Mas’oud yafaɗi haka yana wata ƴar dariya.

Ajiye wayan Sooraj yayi tare da dawo da duk wani attention ɗinsa ga Mas’oud.

“Aure kuma?” ya tambaya da ɗan mamaki.

“Eh Aure mana, gaskia Raj na gaji, shekaru 29 fa ba wasa ba, ko so kake na zauna sha’awa ta kasheni, bansamu na kawar da ita ba?” Mas’oud yafaɗi haka yana mai kafe Sooraj din da ido.

Sunkuyar da kai ƙasa Sooraj yayi tare da cije laɓɓansa, wani irin abu mai ƙuna yaji acikin ƙirjinsa, ahankali ya ɗago kansa ya kalli Mas’oud ɗin cikin wata irin murya kamar mai koyon magana yace “Sha’awa!”

“Banason na faɗa halaka Raj, amma seriously ina da buƙatar mace akusa dani, ina da buƙatar zama cikakken mutum nima, inaga kawai zan tura su Baba gidansu Aisha su tambayomin izinin aurenta kawai, inaga hakan shine mafita, amma kai maikagani?” Mas’oud ya tambayi Sooraj.

Wata murmushi yayi wanda shi kaɗai yasan mene meaning ɗin murmushin, leɓensa na ƙasa ya sake ɗan ciza tare da fesar da iska ta bakinsa. “Allah Ya sanya Alkhairi!” Sooraj yafaɗa ataƙaice.

“Ameen” Mas’oud ya amsa yana maison karantar yanayin da Sooraj ɗin ke ciki, saidai kuma sam ya kasa gano wani irin yanayi Sooraj ɗin ke ciki, domin kuwa Sooraj murɗaɗɗen mutum ne da wahala gane gabansa da bayansa.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 3