in

SOORAJ CHAPTER 2

SOORAJ CHAPTER 2

Wanka tayi sannan ta ɗauki doguwar rigan material blue wanda yakawo mata tasanya, ɗinkin rigan irin rapper gown ɗinnan ne, sannan tana da ɗan guntun hanu, kallon kanta tayi acikin madubi, tare da kallon rigan azahiri, mamakin inda yasamo rigan take, domin kuwa tasan baya ɗaya daga cikin kayanta nacan gidan, gaba ɗaya ma kayan daya kawo mata sabbi ne, kuma duk daga ɗinkin materials sai wasu atamfa guda biyu wanda aka musu ɗinkin riga da sket. Jihabin data gani haɗe da rigan material ɗin ta ɗauka tasanya ajikinta, kasancewar white skin gareta saigashi kayan sunyi mata kyau sosai. Afalo ta iskesu duka suna zaune, cike da ladabi ta rusuna ta gaishe da Ummu, amsa mata gaisuwan nata Ummu tayi tanaɗan dubanta. 1

Akan sofa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, Mas’oud ne ya turo mata plate ɗin soyayyen chips gabanta tare da kofin tea.

Bata wani iyacin abincin sosaiba, tea ɗinnema ta ɗansha da yawa. Mas’oud ma sama sama yaci abincin, Ummu kam adole takecin abincin, hakan ma saboda umarnin da Alh.Mansur ya bata ne, da yace “Idan tasan bataci abinci ba karta sake tazo asibitin, idan bahaka ba kuwa zata gamu da fushinsa.” banda haka babu abun dazai sanya tasanya wani abu na abinci acikinta.

Yauma dai aɗakin jiya suka zauna, gaba ɗaya zuciyoyinsu babu daɗi. Sai ƙarfe uku sannan Dr.Mohd yayi musu jagora zuwa ɗakin da Sooraj ɗin yake.

kamar jiya haka Ummu tayita aikin ƙwalla, Ziyada ma idanunta sunyi tab da hawaye, ɗan matsawa kusa dashi tayi tare da kafesa da idanunta, gani takeyi kamar zai buɗe idanunsa, gani take kamar bacci yake idan katasheshi zai tashi, gani take kamar duk abun da suke yana jinsu, dubanta takai kan ƴan yatsun ƙafarsa, ƙurawa babbar yatsar ƙafansa ta dama idanu tayi, gani tayi kamar yatsar nasa tana motsawa, gefen hijab ɗinta ta sanya ta share ƙwallan dake cikin idanunta, wanda suka sa take ganin komai dishi dishi, sake kallon yatsar ƙafannasa tayi, sai kuma taga bata motsi, da alama gizone idanunta keyi mata.

Kallon Alh.Mansur Dr.Mohd yayi tare da nuna Ziyada yace.

“Matarsa ce?”

“A’a ƙanwarsace” Alh.Mansur yabashi amsa shima yana mai kallon Ziyada wanda idanunta ke cike da ƙwalla.

Kai Dr.Mohd ya jinjina tare da cewa “Inaganin ka ɗauki Hajiya ku koma gida kawai, ita sai kubarta anan, naga kamar yarinyar bata da hayaniya zamanta awajensa bazai kawo wata matsala ba, amma idan Hajiya ce zata zauna kasan dole saita ƙara ta da hankalinta”

Cike da gamtsuwa da kalaman Dr.Mohd, Alh.Mansur ya jinjina kansa. “Tabbas maganarka haka take doctor, yanzu kuwa zamu tafi insha Allah”

Da ƙyar da dabara Abba yasanya Ummu agaba yana rarrashinta sukabar cikin asibitin, tare da Mas’oud wanda shine ke tuƙasu.

Ziyada ita kaɗai akabari acikin ɗakin daga ita sai SOORAJ wanda bashida maraba da gawa. Akan kujeran dake gefen gadon ta zauna, tare da kifa kanta ajikin gadon. Tananan zaune har aka ƙira sallan Magriba, Sallah tayi sannan ta dawo ta zauna. Kallon kyakkyawar fuskarsa tayi, zara zaran eye lashes ɗinsa ne suka kwanta aƙasan idanunsa, sukayi luf dasu gwanin burgewa, gani tayi gumi nata fesowa akan goshinsa, mamakine ya kamata domin kuwa sanyin AC har yaso yin yawa acikin ɗakin. ɗan kwalinta ta ɗauka tashiga goge masa gumin. Atunaninta ko sanyin AC’n ne yayi masa kaɗan hakan yasa taɗan ranƙwafo da kanta zuwa daidai fuskarsa, ahankali tashiga hura masa iskan bakinta akan fuskarsa. hannunta takai kan nasa hanun tashiga goga masa taushin tafin hanunta akan fatarsa, tanayin hakane cikin wani irin yanayi mai ɗauke da nutsuwa. Aƙalla taɗauki kusan sama da mintuna goma tana yi masa haka. Jin ana ƙiraye ƙirayen sallan isha ne yasata miƙewa daga zaunen da take, ta juya kenan kamar amafarki haka taji ya damƙi hanunta.Kamar amafarki haka taji sauƙan hanunsa acikin nata.

Da sauri ta waiwaya zuwa gareshi, amma sai taga ko motsi baiyi ba, hasalima idanuwansa akulle suke da’alama bai dawo cikin hayyacinsa ba. Ahankali ta koma ta zauna tare da kafe sa da ido, zara zaran eye lashes ɗinsa da suka kwanta luf luf take kallo, ahankali tayi ƙasa da idanunta tana kallon ɗan ƙaramin pink lips ɗinsa wanda suka ɗan bushe. Idanunta ta sake mayarwa kan lallausan sajen dake kwance akan fuskarsa, baƙaƙen hairs ne kwance luf akan fatarsa, komai nasa me kyaune kuma gwanin burgewa. Kanta ta mayar jikin gadon tare da lumshe idanunta. Wani irin tausayinshi takeji, daga wani ɓangare na zuciarta kuwa tunanin Farouk ne yazo yayi tsaye. Bazata iya faɗin me takeji game da shi ba, amma tabbas akansa tanajin wasu baƙin al’amura suna ziyartan ta. Zare hanunta dake cikin nasa hanun tayi tare da miƙewa tsaye, toilet tashiga ta ɗauro alwalan sallan isha’i.

Tajima tana zaune akan sallayan. Wasu siraran hawayene suka silalo daga cikin idanunta, kallonta takai zuwa garesa, wasu sabin hawayene suka sake fitowa daga cikin idanunta, hakanan batasan me yasa ba aduk sanda ta ɗaura idanunta akansa takanji zuciarta ta karye, tasan da cewa ita mai raunice tun tuni, amma akansa raunin da takeji na dabanne. Tajima zaune akan sallayan har kusan 9 pm sannan ta tashi ta koma bakin gadon ta zauna. Kanta ta ɗaura adaidai saitin kanshi tare da lumshe idanunta. Mintuna goma tsakani bacci ya ɗauketa batare da ta shiryawa hakan ba.

Ahankali breath ɗinta ke fita, yayinda hucinsa ke sauƙa adaidai saitin kunnensa, ahankali yasoma buɗe idanunsa har ya waresu gaba ɗaya, akan zanen pop’n dake cikin ɗakin ya tsayar da idanunsa, sosai idanun nasa suka sauya kala daga farare zuwa kalan ja, sannan lokaci guda suka ƙanƙance sai tarin eye lashes dake samansu wanda yayi wara wara, wani irin ciwo yakejin kansa nayi masa, yayinda yakejin wani zogi na musamman adai dai chest ɗinsa. Lumshe gajiyayyun idanunsa yayi tare da sauƙe wata gajiyayyar ajiyar zucia. Ahankali ya ɗan yunƙura tare da ɗan jingina bayanshi ajikin pillow, saida ya ɗan cije pink lips ɗinsa sakamakon wani irin zogi dayaji ƙirjinsa nayi, hanunsa yakai kan wani ɗan madanni dake gefen gadonnasa ya ɗan danna da ƙarfi har saida yayi ƙara. 3 minute tsakani saiga wata Nurse tashigo cikin ɗakin da gaggawa. Ganinsa azaune yasa tashiga tambayarsa jikinnasa. Da kai kawai ya iya amasa mata, ganin haka yasa tafita da hanzari don ƙiran Dr.Moh’d.

Baƙaramin daɗi Dr. Moh’d yaji ba sakamakon jin cewa wai Sooraj ya farfaɗo, da ƙwarin guiwarsa haka ya nufo ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance.

Checking ɗinsa yayi sosai sannan ya tambayesa ko akwai wani abu dake damunsa. Kai kawai Sooraj ya iya girgizawa, sannan yayi masa nuni da chest ɗinsa daidai inda aka ɗaure da bandage. Alaman nanne kawai ke masa zafi.
Wasu magungunan kashe zogi Dr. Moh’d ya basa ya sha, sannan yace masa yaɗan kwanta zuwa da safe. Har Dr.Mohd yagama abun da zaiyi yafita Ziyada na bacci bata sani ba. Shiru haka Sooraj ya koma ya kwanta tare da lumshe idanunsa, tunanine cunkushe acikin ransa, _ƘADDARA_ itace abun dake ɗawainiya da rayuwarsa, sau da yawa yakansamun kansa acikin ƙuncin rayuwa, sai dai dole ayanzu zai daure don yaga yayi faɗa da zuciyar da take ƙoƙarin hanasa ɗaukar ƙaddaransa.

STORY CONTINUES BELOW

6:00 am dai dai Ziyada ta buɗe idanunta, awahalce tayi miƙa saboda wani irin ciwo da taji duka jikinta nayi mata, gaba ɗaya duk wani gaɓa dake jikinta yayi tsami. Kallonta tamayar ga Sooraj wanda yake kwance luf acikin gadon idanunsa a rufe da’alama bacci yake, kallon small lips ɗinsa tayi tare da ɗan murza idanunta, A hankali ta buɗe ƙofar toilet ta shiga, gaban sink ta tsaya tare da ɗauro alwala, koda ta fito sallaya ta shumfuɗa tare da tada Sallah, koda ta sallame sallan bata tashi akan sallayan ba, sai dai lokaci zuwa lokaci tana kae dubanta zuwa gareshi.

7:00 am dae dae acikin asibitin tayiwa su Alhaji Ma’arouf da Mas’oud. Koda Dr.Moh’d yabasu kyakkyawan labarin farfaɗowan Sooraj baƙaramin farinciki sukayi ba, har suna rige rigen shiga ɗakin da Sooraj ɗin yake.

Da farinciki ɗauke afuskokinsu duka suka shigo cikin ɗakin, cike da ladabi Ziyada ta gaidasu, kowa fuskarsa ɗauke da annuri ya amsa mata, Ummu kam tuni tayi kan Sooraj, hawayene suka cika idanunta tab, hannunta ta ɗaura akan fuskarsa murya araunane tace. “SOORAJ!” jin muryan Ummunsa acikin kunnuwansa yasanyashi buɗe idanunsa ahankali domin dama ba bacci yakeba kwana yayi idanunsa biyu batare da ya runtsaba. Kuka ne ya ƙwacewa Ummu domin kuwa wani ƙaunar ɗannatane ya sake shiga zuciyarta, sosai takejin tausayinsa duk da ya kasance me laifine agaresu, Hanunsa Abba yakama cike da ƙarfin guiwa haɗe da farinciki yace.

“Alhamdulillah! Yajikin naka, meke maka ciwo yanzu?”

Ɗan yunƙurawa yayi zai tashi Mas’oud yataimaka masa wajen sanya masa pillow a bayansa. Breath me ɗumi yafitar sannan ya kalli Abba cikin wata irin murya yace “Banajin komai Abba, kawai inaso na koma gidane, nagaji da zaman nan!” yaƙare maganar yana ɗan ɓata fuska.

Farincikine yasake cika zuciyarsu jin cewa bayajin komai. Murmushi Abba yayi tare da dafa kafaɗan sa yace.
“Ka kwantar da hankalinka, zannema maka sallama awajen Dr.”

Ɗan ya mutsa fuska yayi tare da kawar da kansa gefe, idanunsu ne suka sauƙa acikin na juna, dai dai lokacinne kuma ƙwallan da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan ƙuncinta, da sauri yajanye idanunsa tare da ɗan cizan lips ɗinsa. Ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon ya somayi, Mas’oud yace “Ina kuma zaka?”

“Wanka!” Sooraj yabashi amsa ataƙaice. Bathroom ɗin dake cikin ɗakin ya shiga, long pencil jeans ɗin dake jikinsa ya cire tare da tsayawa agaban shower ruwa na dukan jikinsa, Sai da ya soma jin sanyi na ratsa cikin jikinsa sannan yakashe shower’n, dai dai lokacinne kuma aka soma knocking ƙofar toilet ɗin, yana buɗewa Mas’oud ya miƙo masa wani Blue pencil crazy jeans, tare da sabon brush da maclean, karɓa kawai yayi yakoma cikin bathroom ɗin, saida yasanya trouser’n kafun yayi brush, ruwa ya sanya yasake wanke fuskarsa. Sannan yafito daga cikin toilet ɗin. Zama yayi akan gado, lokacin har Ummu tagama haɗa masa tea. Miƙa masa cup ɗin tayi, amaimakon ya karɓa sai ya ɓata fuska tare da kawar da kansa gefe, alaman bazai shaba.

“Kayi haƙuri kasha kaji, Dr. Moh’d yace akwai maganin da zakasha kuma dole saika ci abinci!” Abba yafaɗi haka cikin rarrashi.

Karɓan cup ɗin yayi tare da kaiwa bakinsa, da kaɗan kaɗan yake sipping tea ɗin, hakanan yakejin bakinsa babu wani ɗanɗano, bai wuce rabin cup yasha ba ya aje kofin, dai dai lokacin Dr.Moh’d ya dawo hanunsa ɗauke da magunguna.

Ita dai Ziyada tana daga zaune akan sallaya tana ganin ikon Allah, mamakin yanda ake shagwaɓasa kamar ƙaramin yaro take, daga cikin zuciarta kuwa wani irin sanyin daɗi takeji na ganin ya buɗe idanunsa har ma ya tashi, Mas’oud ne ya dawo gefenta tare da jawo wata farar kujera ya zauna akai, plate ɗin dake hanunsa ya miƙa mata, abincine aciki Chips and onion soup wanda yaji ƙwai, karɓa kawai tayi ta ajiye batare da takai koda loma ɗaya bakinta ba.

“Ziyadah!” Mas’oud yaƙira sunanta cikin ƙasa ƙasa da murya.

Bata amsa masa ba sai dai ɗago kanta da tayi ta kalleshi.

STORY CONTINUES BELOW

“Kukan na menene?” yatambayeta yana me ɗan satan kallonta.
Hanu tasanya ta shafi gefen kumatunta, sai alokacin ta tuna da cewa hawaye sun sauƙo daga idanunta kuma bata share ba, hannunta tasanya ta goge hawayen tare da yin ƙasa da kanta, tasoma wasa da yatsunta.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 3