in

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ CHAPTER 1

SOORAJ*

Tsugune yake akan ƙafafunsa, kansa na kallon ƙasa, yayinda kyawawan idanunsa suke alumshe, jama’a ne cike awajen, sai hayaniya suke, fuskar kowa ɗauke take da farinciki, banda wani mutum ɗaya, shima ɗin baƙin ciki da damuwarsa basu bayyana akan fuskarsa ba, amma tabbas zuciyarsa nacikin matsanancin damuwa.

Sake matse ƴan saffa saffan idanunsa yayi da ƙarfi, jiyake kansa na juyawa, zuciyarsa nayi masa wani irin tuƙuƙi, sosai hayaniyar jama’an dake wajen ke hautsina masa ƙwaƙwalwa, sam shiba mutum bane mai son yawan hayaniya, aduk sanda hayaniya yayi yawa awajen da yake, to ciwon kai ne ke kamasa mai tsanani, yanzu haka shikaɗai yasan abunda yakeji, jiyake kamar ya buɗe bakinsa ya kwarara ihu, koda zaiji sauƙin abun da yakeji.

“ALHAMDULILLAH AURE YA ƊAURU YAU ASABAR AN ƊAURA AUREN SOORAJ MAI NASARA DA AMARYARSA AISHATU KABEER MUNA TAYA ANGO MURNA!!!” abunda wani maroƙi keta faɗa kenan cikin ɗaga murya.

Wannan maganan da maroƙin keyi shiyayi sanadiyar dawo da SOORAJ dake tsugune cikin hayyacinsa, wani yawu mai ɗaci ya haɗiya, lokaci guda idanunsa suka rikiɗe suka zama jajaye, ƙoƙarin tashi tsaye yasomayi. Da sauri wani kyakkywan matashi dake gefensa yariƙe hanunsa, cikin murya ƙasa ƙasa yace “Please SOORAJ karkayi haka mana, acikin jama’a fa muke, kuma kasan tunda mukazo nan idanun jama’a akan mu yake”

Tsuka wanda aka ƙira da Sooraj yayi, tare da fusge hanunsa daga riƙon da wannan ɗin yayi masa, kallonsa yamayar ga Abbansa, karab idanunsu suka sauƙa akan najuna, da sauri Sooraj yayi ƙasa da kansa.

A hankali Tururuwan jama’ar da suka taru a ƙofar gidan Alhaji Kabeer suka soma raguwa, kowa na ƙoƙarin kama gabansa, ganin haka yasa Sooraj miƙewa tsaye yasoma nufar inda motarsa take, ko ɗaga kansa baiyiba balle har wasu daga cikin mutanen da sukayi ragowa su fahimci wani irin yanayi yake ciki. Hanunsa yaɗaura akan murfin motar zai buɗe, yaji muryar MAS’UD ta daki dodon kunnensa.

“Inazakaje?” abunda Mas’ud yatambaya kenan.

Juyowa Sooraj yayi ya watsawa Mas’ud harara, ransa amatuƙar ɓace yake, wani irin haushin Mas’ud ɗin yakeji, gani yake komai daya faru hadda sa hanun Mas’ud ɗin aciki, takaici ne yasake turnuƙe zuciyarsa, sai kawai yasaki tsuka yabuɗe motarsa yashige, Mas’ud na ƙoƙarin zagayawa gefen mai zaman banza yashiga, Sooraj yayiwa motar key, aguje yafigeta haɗe da turbuɗawa Mas’ud dakuma sauran jama’an dake kusa dasu ƙura. Hakan yasa kowa yabisa da kallo, ciki kuwa hadda Abbansa dake can gefe suna ganawa da Baban Amarya.

Sheshsheƙan kuka ne ketashi acikin ɗan madaidaicin ɗakin, wata yarinyace rakuɓe ajikin bango, ta takure kanta waje ɗaya, daga yanda take sauƙe ajiyar zuciya akai akai zai tabbatar maka da cewa kuka taci ta ƙoshi son ranta, idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe haɗe da kai kallonta sama. “YA ALLAH!” abun da ta ambata kenan cikin wata irin raunanniyar murya, dake cikin halin matsanancin naiman taimako, tabbas ta yarda cewa idan Ƴa Mace tarasa Uwa to tarasa babban gata aduniya, Uwa itace komai itace ginshiƙin rayuwa, kamar yanda ruwa keda matuƙar amfani aduniya, haka uwa take awajen kowani ƴa/ɗa, ayanda take da ƙananun shekaru, tunaninta da hankalinta basukai ɗaukar wasu matsalolinba, amma saboda halin rayuwa duk tazama wani iri, rayuwarta duhu ne, rayuwarta ƙunci ne, HASKE take nema akoda yaushe, da fata dakuma burin wani wanda zai taimaka mata.

“Dan Ubanki wai maikikeyi acikin ɗakinnan ne? baƙar munafuƙa, Allah dai yayi wadaranki ZIYADA natsani waƴannan halayyartaki, muguwa mai baƙar zuciya, zaki fitone kosai nashigo cikin ɗakin nayi ƙasa ƙasa dake!?” faɗan wata mata dake tsaye abakin ƙofar ɗakin da yarinyar ke ciki, matar tacika fam sai jijjiga ƙugu take.

Jinmuryan Inna Ma’u acikin dodon kunnuwanta baƙaramin tsoritata yayiba, jikinta na rawa tanufi hanyar fita daga ɗakin.

Tana fitowa Inna Ma’u ta bita da wani irin kallo.
“Wallahi natsaneki Ziyada, natsani koda jin sunanki ne, adole nake rayuwa dake acikin gidannan, keda uwarki kun riga da kunzamemin JARABA, ƴan iska masu fararen fuska!” Inna Ma’u tafaɗi haka cike da takaicin Ziyada.

Itadai Yarinyar da ake ƙira da sunan ZIYADA shiru tayi tare da sunne kanta ƙasa, ƙirjinta kuwa jitake kamar zaiyo tsalle yafito waje sarai tasan wacece Inna Ma’u, yanzu zata kuma sake jibganta fiye da wanda tayi mata ɗazu.

“Ungo wannan naira ishirin ɗin kije maza ki ɗauko min niƙa na, kuma wallahi idan kika sake baki dawo da wuri ba, yau saina ƙona wannan ɗan iskan fuskan naki, mai zubin mayu” Inna Ma’u tafaɗi haka tana mai sanya hanunta ta mangare Ziyada harsai dakanta ya bugu da bango, sosai taji zafin bugewa dakuma mangareta da Inna Ma’u tayi, amma babu halin tayi kuka, naira ishirin ɗin ta amsa, cikin yanayinta mai sanyi tanufi hanyar ficewa daga gidan.
Tana ficewa Inna Ma’u tayi ƙwafa haɗe da cewa.
“Wallahi bazaki ƙara min cikakken sati biyu agidannan ba, ko kasheki ne ma gwamma nayi na huta, komai na mayyar uwarki kin kwashe”….

Gudu sosai yake tsalawa akan babban titin, saida yayi tafiya mai nisa kafun yayi parking motar agefen titi, hanunsa yasanya ya bugi steering motar, tare da furzar da iska daga bakinsa, wata drawer dake jikin motar yajawo haɗe da ciro goran ruwa, ɓalle murfin goran yayi haɗe da kafa goran abakinsa, saida yasha ruwan fiye da rabin goran kafun ya ɗauke bakin goran daga kan nasa bakin, numfashi yake fitarwa ahankali, jiyayi ƙirjinsa yayi masa nauyi, ɗaga kansa yayi ya kalli madubin dake cikin motar, da sauri ya kauda kansa gefe, wani irin tsananin tausayin kansa ne ya kamasa, jiyayi zuciyarsa tayi wani irin karyewa, kifa kansa yayi ajikin steering motar, baisan yazaiyi da rayuwarsa ba, baikuma san taya zai fahimtar da iyayensa lalura da damuwarsa ba, akodayaushe su kansu kawai suka sani, koda sau ɗayane basu bashi dama yasanar dasu matsalarsa ba, ako da yaushe basu da wata magana saita Aure, burinsu ɗaya shine yayi aure, baruwansu su basu wani damu da sanin shiɗin yayakeba, ɗago kansa yayi daga jikin steering motar, idanunsa ne suka sakeyin ja, kamar anwatsamusu garin barkono, bayajin cewa zai iya zama da kowace mace aduniyarnan, yanaji ajikinsa cewa shi ba’ayisa don yayi aure ba, rayuwarsa cike take da DUHU baisan wani HASKE ba, “Sai yaushene zasu fahimci hakan?” yatambayi kansa. Shiru yayi naɗan wasu mintuna kafun yatada motarsa, yanzu kam ahankali yake tuƙin motar bakamar ɗazu ba, saidai kuma zuciyarsa cike take da tarin tunani kala kala lallai dolene zaiyi abun da ya saba, duk da yasan hakan ba daidai bane kuma ALLAH Ma bayaso, amma baida wani zaɓi da ya wuce haka…

*(Sunan labarinnan SOORAJ shima ƙirƙiransa nayi kamar yanda na ƙirƙiri sauran, kamar yanda kukasani labarina ina ginashine akan mutum biyu, to wannan labarin ma hakanne, domin akan SOORAJ da kuma ZIYADA na ginashi, kamar yanda nagina SHU’UMIN NAMIJI akan ZAID da ZAHRAH, nakan tsayawa nayi komaina akan daidai, ina iyaka ƙoƙarina wajen ganin nabaku nishaɗi, nasamu ƙalubale sosai akan Labarin dana gama wato SHU’UMIN NAMIJI duk da nasan matakin nasara yana tarene da ƙalubale, amma wasu sunta faɗamin maganganu son ransu so please kuna kiyayewa, bakowacce magana yakamata ace wasunku na furtawa ba, karku manta magana mai daɗi sadaka ce.Agaban wani tankamemen gate yayi parking motarsa, fitowa yayi daga cikin motar ya nufi ƴar ƙaraman ƙofar dake jikin gate ɗin, ahankali yatura ƙofar yashiga, Manu mai gadi naganinsa ya kwaso aguje cike da girmamawa yace.
“Ranka ya daɗe barka da zuwa, Ango, Ango kasha ƙamshi….”

Kallon da yayiwa Manu mai gadine yasa yaja bakinsa yayi shiru, batare daya ƙarasa maganar dayakeyi ba.

Direct wani dogon gini dake tsakiyan compound ɗin gidan yanufa.

Wata ƴar dattijuwar mata ce ke zaune acikin katafaren falon, kayane zube agabanta tare da wasu manyan akwatuna masu kyau da tsada.
Da sallama ɗauke abakinsa yashigo cikin falon, amsa masa sallaman matar tayi fuskarta babu yabo ba fallasa. Baidamu da yanayin yanda yaga fuskarta ba, don yasan dalilin daya sanya tayi kicin kicin da fuska damace batason bashi, kuma amma duk da haka baijin zaiƙi furta abundake cikin ranshi.

“Barka da gida Ummu”
Sooraj yafaɗi haka bayan yayiwa kansa mazauni akan lallausan carpet ɗin da ya mamaye ƙasan falon.

“Yauwa sannu” Ummu tafaɗa tana mai ƙoƙarin tattare kayan dake gabanta. Shirune yashiga tsakaninsu, dama shi haka yake idan yayi magana saiyaja wasu mintuna baisake cewa wani abu ba, bakuma don baida abun cewa ba, a’a haka ya sabarwa kansa. Ummu kuwa afakaice ta ɗan saci kallonsa, yanda taga fuskarsa ya tabbatar mata da cewa akwai magana abakinsa, itakuwa bazata so taji komai daga bakinsa ba. Miƙewa tayi daga zaunen da take, wayarta taɗauka kana ta nufi hanyar da zai sadata da ɗakinta.

Ganin da yayi cewa idan yabari tatafi yarasa damansa ne, yasanyashi gyara zama haɗe da cewa. “Ummu dama inaso….”

“Banason kacemin komai, ya isa haka, munriga da mungaji da halinka SOORAJ, wallahi kaji na rantsema awannan karon kasaki matar da muka aura ma, ranka saiyayi mummunan ɓaci, zakuma kaga fushinmu irin wanda baka taɓa gani ba!” Ummu takatseshi ta hanyar faɗan haka cikin ɓacin rai.

Jajayen idanunsa yaɗago ya watsawa Ummun, itakuwa ko waiwayosa batayiba ta wuce ɗakinta.

Wani irin tsannin baƙinciki ne yasake kawo masa ziyara, babban abun takaicin shine yanda akaƙi basa dama, jiyayi kansa na sarawa kamar zai rabe gida biyu, tashi yayi ya fice daga cikin falon, ko iya kallon gabansa bayayi haka yakoma motarsa, kafa kansa yayi ajikin steering motar, yana fidda numfashi mai zafi, “Wannan wace irin rayuwace yakeyi? sai yaushene zai samu sauƙi daga raɗaɗin da yakeji?” tambayar dayaketa yiwa kansa kenan acikin zuciyarsa. Ya kusan mintuna 10 a wajen, kafun ya iya tada motarsa yabar unguwartasu gaba ɗaya, kaitsaye gidansa ya nufa.

Koda ya isa bedroom ɗinsa kayan dake jikinsa ya cire tare da shigewa cikin bathroom, wanka yayi tare da ɗauro alwala kana yafito, dogon wando na jeans yasanya tare da wata farar T-shirt, kallon agogo yayi yaga da sauran time kafun aƙira sallan Azahar, kwanciya yayi akan makeken gadonsa tare da lumshe gajiyayyun idanunsa…..

***
Idan hankalin Ziyada yayi dubu to atashe yake, domin kuwa tana zuwa injin niƙan tasamu ba’a niƙawa Inna Ma’u niƙan garin kunun tsamiyanta na gobe ba, hawayene suka cika idanunta, yayinda tashiga haɗa mai injin da Allah akan yaniƙa mata sauri take, da ƙyardai tasamu ya yarda ya niƙa mata. Tunda ta shawo kwanan ƙofar gidannasu take hango wata yagalgalalliyar mota, wanda taji tsufa harta gode Allah, cikin yanayinta na sanyi taƙaraso ƙofar gidannasu.

Wani dattijone wanda aƙalla shekarunsa zasukai 60 tsaye ajikin wata ragwaɓaɓɓiyar mota dagani motar taci wahala, mutumin irin baƙaƙen tsofinnan ne, sannan kuma ko wani gashi najikinsa yatashi daga baƙi yakoma fari, kai tsaye zaku iya ƙiransa da tsohon najadu, domin daganin idanunsa zakasan cewa baƙaramin ɗan duniya bane, yanayin yanda yake kallon Ziyada kamar wani tsohon maye ne yasanya tayi ƙasa da kanta, tashige cikin gida, Murmushi Tsohon yayi haɗe da jijjiga kansa, wani irin daɗi yaji aransa alokacin dayaga Ziyada’n.

“La’anatu sai yanzu kikaga daman dawowa? halin asaran dai shine bazaki fasa ba?” Inna Ma’u ta tambayeta.

“Kiyi haƙuri Inna Ma’u, wallahi ba ayi miki niƙan da wuri bane, shine kuma…..”

“Da Allah rufemin baki shine kuma me? waye baisan fetsarancinki ba, shashasha kawai, yanzu da kika ebo ƙafa kika shigo cikin gida, shin bakiga Tsoho ɗan dashe natsaye a waje yana jiranki bane?”

Wani irin bugawa ƙirjin Ziyada yakumayi, a tsorace tace
“Tsoho ɗan dashe kuma?”

“Ƙwarai kuwa, zakije kisamesane ko kuwa saina ɓaɓɓallaki yanzu anan wajen!” Inna Ma’u tafaɗi haka a hasale.

Jikin Ziyada ne yasoma ɓari amma bata da wani zaɓi daya wuce zuwa tasamu tsohon najadun dake tsaye a waje yana zaman jiranta.

Tana fitowa daga gida Tsoho ɗan dashe yasaki dariya irinta tsofaffin ƴan duniya. Kallonsa yamayar kan ƙirjinta, saida ya haɗiyi wani yawu, “Ƙaraso mana Amaryata” yafaɗa yana washe wawagegen bakinsa.

Kallon tsananin tsana Ziyada tabisa dashi haɗe da soma ƙare masa kallo, idanunta ta sauƙe akan jajayen haƙoransa dayaketa washewa, gaba ɗaya bakinsa cike yake da tsakin goro, komai nasa dagajaja ba kyaun gani, duk da itama acikin dauɗa da ƙazanta take, sannan kuma bata da wani suturun kirki, amma duk da hakan ƙazancin Tsoho ɗan dashe daban take dana kowa, duk garin babu wanda baisan wanene Tsoho ɗan dashe ba, tsohone da bai riƙe mutumcin kansa ba, bashida wani aiki sai lalata yaran jama’a, matansa huɗu, kuma acikin garinnasu sosai akeji dashi, kasancewar yana da shanaye dakuma dabbobi, saboda tsabar duniyanci irin nasa har mota yake dashi, irin ko ohon motocinnan, nanma ƙaryan raine kawai irin nasa, ko iya tuƙata baiyiba, akwai wani ɗan ƙullinsa Ɗan liti shike tuƙasa yakaisa duk inda zashi, yanzuma tare suke.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GADAR ZARE CHAPTER 2

SOORAJ CHAPTER 2