in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 8

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 8

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 8

Ikhlas na shigowa ta iske Sultan a falo yayi shiru yana tunani, gaisawa sukayi kafin yace mata Badiyyar na daki, tana shiga dakin taga Badiyya kwance sai sauke ajiyar zuciya take, tana saka hannu tana share hawayen dake zubo mata, alamar tsananin damuwa kwance kan fuskarta. Ikhlas zama tayi jusa da ita “Badiyya,” ta kira sunanta cikeda damuwa. Badiyya tajita amma ta mata banza, dan kuwa she needed to be alone, gaba daya ta rasa me ke nata dadi, Momynta kadai takeda bukatar gani yanzu, wanda kuma ta mata nisa na har abada. Ikhlas hannunta ta riko, dan ganin yanayin Badiyyar ya nuna mata tabbas tana cikin damuwa “Badiyya, dan Allah ki mani magana, naga Sultan a falo looking glum amd sombre, kema gaki kina kuka, wai meke faruwa ne? Kuma ni cemani yayi baki
lafiya,” Ikhlas ta fada cikeda damuwa, dan kuwa gaba daya ganinsu a haka yasa something bad gnawed at her, dan ita tayi tunanin Ahmad ne ya kara zuwa. Badiyya a hankali ta bude idanunta, wanda sukayi jajir saboda azabar zazzabi ga damuwa data mata yawa, “Ikhlas, Banda lafiya ne,” tana fadar haka ta rungume Ikhlas tana kuka. Ita kuma Ikhlas ganin dukansu suna cikin damuwa, dan da ace rashin lafiyace normal da duk bazasu damu haka ba, amma kawai sai ta share. Hannu takai kan goshin Badiyya tajishi rau, cikeda tashin hankali ta dago ta kalli Badiyya “Badiyya lafiyarki kalau kuwa? Ji fah yanda jikinki yayi zafi, amma bazaki iya fadawa Sultan ba shine zakizo ki rufe jikinki hada saka wani uban blanket ko? Yayi maki kyau. Yanzu tashi kije kiyi wanka da ruwan sanyi,” Ikhlas ta fada tana yaye bargon da Badiyya ta rufa dashi, cire mata hijab din tayi kafin ta mikar da ita. Badiyya tashi tayi tsaye tana turbune fuska “Ikhlas inajin sanyi fah, kuma kince ruwan sanyi,” Badiyya ta fada tana bata fuska, hade da kankame jikinta alaman sanyi. Ikhlas kallon tara saura kwata ta mata “Lallai, wato kinyi aure shine har kike da bakin magana dan ance kiyi wanka da ruwan sanyi ko? See who is talking dan Allah. Da can shekara takwas din da kikayi kina wanka dana sanyi ai sai naga kin mutu. Abeg jeki wanka likitanki yazo ya duba ki,” Ikhlas ta idasa maganarta cikeda zolaya. Kallan bansan rainin wayau Badiyya ta mata kafin ta bude baki dakyar ta fara magana “Kai Ikhlas, abun hada gori ko? Kin kyauta diyar masu kudi,” Badiyya ta fada tana harararta, dan dama idan tana san jan Ikhlas to tace mata diyar masu kudi. “Nidai karki chanza mani magana, jeki wanka ki fito uwargida kuma amarya ga Sultan dinsu,” Ikhlas ta fada cikeda dariya. Badiyya batace komai ba, cikin dingishi ta fara takawa zuwa toilet, Ikhlas wani suspicious look ta bita dashi, sai can kuma ta fashe da dariya, wanda hakan ya tilasta ma Badiyya juyowa “Ke lafiya kike wani kallanmin kafafu kina dariya kamar sabon kamu?” Badiyya ta tambaya tana bin idanun Ikhlas wanda suke zaune kan kafafunta. Ikhlas gumtse dariyarta tayi, dan tasan wani lokacin Badiyya akwai saurin jin zafi, kallonta tayi tana sniggering “Ke babu wani abu fah, kinsan sabon kamu akwai saurin gano sabbin matan da suka tashi daga layin ladies suka koma na women,” Ikhlas ta bata amsa with ful sarcasm, tana kara fashewa da dariya “Ai sai kice mani aiki Sultan dinsu yayi, shine hada wani

kirana wai baki da lafiya dan rashin kunya, ke kuma kika debi uban hili kinata kuka kamar wata sakara, kai Allah kunada abun dariya,” zuwa yanzu Ikhlas ta kasa tsaida dariyarta, dan daukar abunda sukayi childishness tayi, to miye a cike, hada laifin Sultan dinma daya biye mata. Badiyya batace mata komai ba, girgiza kai kawai tayi “Zakiyi bayani lokacin da Abdallah ya rikeki ne banza,” tana fadar haka tayi shigewarta bayi. Ikhlas kwashewa da dariya tayi “Ke ai ni bana halin yan yara, kuma yanzu su Badiyya an girma an bar cire kaya gabana ko? Gaskiyane matar Sultan dinsu,” ta fada kafin tayi hanyar gadon domin gyarawa. Gyarawa tayi kafin ta wuce kitchen dan ta dafa masu wani abun, bata ga Sultan a falo ba, hakan ya tabbatar mata may be ya tafi sallah, dan kuwa masallatai nata gabatar da tasu. STORY CONTINUES BELOW  Chips ta yanke sharp sharp ta soya, tana dawowa taga Badiyya kan prayer mat tana sallah, ajiye tray din tayi gefen Badiyya kafin ta zauna kusa da ita, Badiyya murmushi ta mata flashing me cikeda godiya. “Badiyya, dauki wannan ki kaiwa Sultan dinsu,” Ikhlas ta fada tana ciro plate daya daga cikin tray din, sai cup din juice din data zuba masu. Badiyya yamutse fuska tayi, saidai gudun kar Ikhlas tayi suspecting wani abu yasa ta mike, tana cije kasan lebe, mika mata plate din tayi tana fadin “Ayi a hankali fa kayan Sultan dinsu,” cikeda zolaya ta koma ta zauna. Badiyya tana shiga dakinshi ta ganshi kwance kan gado kanshi yana kallon ceiling, kallon mamaki ya bita dashi, ajiye plate din tayi kan bedside drawer kafin ta kalleshi ta kasan ido “ka taso kaci abinci,” tana fadar haka ta juya ta fita, maganar ma datayi badan taso ba, dan kawai daga ganin yanayinshi yunwa ce ke cinshi, saidai tasan inhar bata ce mashi yaci ba bazai taba ci ba. Sultan a hankali ya furta ya gode kafin ya janyo tray din ya faraci, a ranshi yana gode ma Ikhlas ba adadi, dan kuwa yasan saidai miracle din Ikhlas din, amma da babu abunda zaisa Badiyya kawo mashi abinci yau, inba wani ikon Allah ba. Badiyya na komawa taga Ikhlas har ta faracin chips din, zama tayi itama ta fara ci, saida suka kusan rabi kafin ta kalli Ikhlas “Ke wai bakiga kowa yayi sallah bane? Baki tashi kiyi taki kamar dangin arna?” Badiyya ta tambaya

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 7

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 9