in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 6

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 6

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 6

Badiyya kwana tayi tana sallah, akan Allah ya kawo mata mafita, kuka kuwa tayi shi kamar ranta zai fita, dan tasan tabbas babu abunda zai hana a daura auren nan gobe.+ Tunowa da mahaifiyarta yasa ta kara wani kuka, hade dayin adduar Allah yakai rahama kabarinta, camera ta kara daukowa, ta kunna pictures dinsu tana kallo, koda tazo kan video din kasa kunnashi tayi, dan kuwa matsala ta mata yawa, batayi shirin kara shiga wani bala’in ba, amma tasan ko badade ko bajima akwai lokacin da zata kalli video dinann, tana tare da wanda zai share mata hawaye. Amma ba yanzu ba, wanda damuwarta ma ta isheta balle har ta dauko wata ta dora ma kanta. Sallar ta karayi sannan ta dauko Al-qur’ani tana karantawa, har zata rufe ta tuno ranar da suke karantawa itada Momynta tace su karanta Suratul Mulk, haka ta bude ta fara
karantawa, tana karantawa tana kuka saboda tsananin zafi da zuciyarta ke mata, wannan lokacinne take bukatar mahaifiyarta, ko wani dangi nata, amma babu ko daya. Gashi rabonda taga su Anty Kausar kusan 5years kenan, tunda sukazo Gwaggo tayi musu wulakanci tayi masu korar kare basu kara zuwa ba, tasan yanzu dinma basu sani ba amma da sunzo. Saida tayi sallar asuba sannan ta kwanta kan gadonta, hade da shasshekar kuka haka wani wahalallen bacci yayi gaba da ita, me cike da mafarkai kala kala.2 _”Badiyya kin zama mallakina, Allah ya bani ke, kuma abu daya da nake so dake shine; ban taba sanki ba, jikinki ne kawai yake burgeni, kuma yanzu tunda na aureki zanyi abunda naga dama dake, sannan in barki cikin jifa’i a gidana, zaki zama sex machine dina har sai ranar da kika gundure ni in koraki gidanku,” ya fada haka tare da kamo hannunta da hannu daya, ya saka dayan yana shafar gefen fuskarta lustfully._ _Cikin sheshekar kuka ta warce hannunta sannan taja baya, wani irin kallo tsana take mashi, zuciyarta na matukar zafi, “Nabil, ka sani Allah ya fika, kuma mallaka maka ni dayayi bawai hakan yana nufin ya baka damar ka wulakanta ni bane, sannan maganar da kake fadi na baka taba sona ba, ni bazanyi musu da hakan ba, domin kuwa na dade da sanin kai ba mutumin arziki bane, kai mugune, azzalumi, mahainci, munafika, mazinaci, fasiki!” Kafin ta ida maganar ya sharara mata mari, rike wajen tayi wasu hawayen na kara zubuwo daga idanta, ji take farin ciki yayi bankwana da ita._ _”Ke dan uwarki ni zaki kira da wadannan sunayen? Har ni zaki cema mazinaci fasiki? To yau zan nuna maki asalin fasikanci,” yana fadar haka ya fara matsowa inda take, tashi tayi ta fara ja baya, yana binta har suka kure ma bangon dakin. Yakai hannu zai tabata kenan yaji an buge hannun hade da jan Badiyya gefe, juyowa yayi abruptly domin yaga wannan wane isasshene._ _”Kar ka sake ka kara dora hannunka akanta, domin kuwa bata riga ta zama matarka ba, wallahi zan iya yin komai a kanta, kuma bazaka aureta ba inhar ina raye,” mutumin ya fada sannan ya rike hannun Badiyya ya jaya zuwa waje, ajeta yayi akan wani dakali, sannan ya juya fuskarshi “Kiyi zamanki anan, zanzo in ceceki,” yana fadar haka ya kara gaba, saurin riko hannunshi tayi, cikin muryar kuka ta fara magana “Bawan Allah ka nuna mani fuskarka in gani, sannan kuma ka fadaman sunanka,” ta fada da sigar roko, dan kuwa ko ba komai ya ceceta daga hannun azzalumincan._ _Bai juyo ba a haka ya bata amsa “Badiyya, sunana Aliyu, sannan kuma nine zan kasance mijinki. Fuskata kuwa nan bada dadewa ba zaki gani, na barki lafiya,” yana fadar haka ya janye hannunshi cikin rikon Badiyya hade da

wucewa._ Badiyya a razane ta farka daga wannan mummunar mafarkin da tayi mara ma’ani me wuyar fassara, zufar data keto mata yasa ta tuna dafa mafarkine ba gaske ba, kuma nanda yan awanni kalilan za’a daura aurenta da Nabil, the person she so much despise. Nan da nan ta fara kuka, kuka take kamar ranta zai fita, tana zaune tana kuka aka shigo dakinta, Ikhlas ce cikin shiga ta alfarma, zama tayi kusada ita, sannan ta dora kanta bisa kafadarta, nan Badiyya ta kara fashewa da kuka, sun dade a haka kafin Ikhlas ta dagota daga kafadarta “Badiyya kiyi hakuri kiyi tawakkali da Allah, komai yayi zafi maganinshi Allah,” Ikhlas ta fada da raunanniyar murya, dan itama gudun kar su taru suyita kukan tare da ta taya Badiyya kukan, dan kuka bakin cikin dake ranta baya misaltuwa, tausayin Badiyya takeji, dan kuwa tasan tana kin karbar soyayyar maza ne da sunan ta tsani maza, amma real fact din har yanzu Sultan ne bai bar zuciyarta ba. STORY CONTINUES BELOW  Badiyya dagowa tayi, “Ikhlas bai kira ba ko?” Ta tambaya, wasu hawayen na zubo mata. Nodding kai Ikhlas tayi alamar bai kiraba, “Ikhlas karfe nawa?” Badiyya ta kara tambaya, hawaye na kara wanke mata fuska, dan kuwa jiya taji Gwaggo na waya da mutane akan lokafin sallar Azahar za’a daura auren, wanda yanzu 12:30pm ake fara sallah. “Yanzu 11:30am Badiyya, me zakiyi da lokaci ke kuma?” Ikhlas ta tambaya, domin ganin yanayin Badiyyar lokacin da ta fada mata da alamu akwai abunda take expecting. “Na shiga uku Ikhlas, wallahi saura 1hour, kuma bazai zo ba, yamin alkawarin zai ceceni, yace shi zai aureni, Ikhlas ki taimakeni kice yazo, na bani ni Badiyya, Ikhlas Nabil kasheni zaiyi nima kamar yadda aka kashe Momy in har na aureshi, Ikhlas ki taimaka mani, Ikhlas bai zo ba,” Badiyya sai magana take tana hawaye kamar tababbiya, zuwa yanzu Ikhlas ta kasa daurewa, hawayenta itama ta saka suka zubo freely, tausayin Badiyya na kara cika mata zuciya, amma to waye wannan daya fadama Badiyya zaizo? “Badiyya waye ya fada maki zaizo? Badiyya lafiyarki kalau kuwa?” Ikhlas ta tambaya tana share hawayenta, she needs to be strong for Badiyya, dan tana bukatar hakan.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 7