in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5

Kyakkyawar budurwa yar kimanin shekara sha takwas a duniya, tana tafe itada kawarta wadda itama zatakai shekaru sha takwas din. Layin dazai sadaka da gidansu suke bi, labari suke, saidai daya daga cikin yan matan nan kwata kwata hankalinta baya kan labarin, gabadaya hankalinta yana duniyar tunanin da takeyi. Da dayar budurwar ta gaji da magana, sai tayi nudging kafadarta “Wai Badiyya tun dazu ina magana, amma kinyi banza dani,” Badiyya wadda fuskarta take a daure, kamar bata taba yin dariya ba a rayuwarta, tasha unifoam dinta na Government girls college, wadda akafi sani da WTC.
Kallon kawar tata tayi, saidai expression din fuskarta bai canza ba, dan yake tayi “To Ikhlas me zance maki? Nasan dai maganar bata wuce na new lecturer ku, ni kuma inada abunda ya kamata nayi tunani akanshi, so why will I pay heed to your silly talks?” Badiyya ta fada alamun kosawa, tana kallan Ikhlas kawarta, wadda a yanzu tana matakin aji daya a jami’ar Alqalam university Katsina. Ikhlas wata irin dariya tayi, “Hehe.. I know what you’re thinking about, bai wuce Sultan ko?” Ta fada tana kurama Badiyya idanu, alamun ko tayi karya zata gane. Fadan sunan Sultan saida zuciyar Badiyya ta buga, dan kuwa ta manta dashi ma, after 7 years bai nemeta ba, why will she think about him? Men are all the same, basuda alkawari. Tsaki taja tana ma Ikhlas kallan bakida hankali “Ikhlas wai sau nawa zan fada maki banasan maganar namiji, na tsani maza, a tsarin rayuwata babu namiji a ciki, burina in gama secondary school inje in karanci law,” ta fada, bacin rai karara kan fuskarta da kuma yadda maganarta take fita. Ikhlas wani gauron numfashi taja, “Badiyya! Bafa ko wane namiji bane daya, karki ma
maza muguwar shaida mana, sannan kuma maganar Sultan bai nemeki ba ki bashi uzuri mana, kikasan dalilinshi nakin nemanki all these years? Kuma you were at fault ai, har barin boarding school yayi saboda ke, ya dawo kullum sai yazo gidan Gwaggo saboda ke, ganin you were depressed and heart broken, shekara daya yana abu daya amma Badiyya baki kulashi ba, does’nt he have feelings? Haba Badiyya, yayi kokari fa, shima dole yaje yayi building future dinshi,” Ikhlas na gama maganarta har sunzo kofar gidajensu, babu wadda tace kala haka suka shiga gidajensu. Badiyya na shiga gida ta iske Gwaggo tsakar gida tanashan fruits, ko kallon inda take batayi ba, har tayi hanyar falo sai Gwaggo ta kwala mata kira “Ke yanzu dan ubanki har kinyi girman da zaki dawo gida amma ki wuce ko gaisuwa?” Gwaggo ta fada cikeda masafi. Badiyya batace komai ba dawowa tayi ta gaidata sannan ta wuce dakinta, ta fito domin tayi wankan da yazame mata ibada, tazo wucewa ta wajen Gwaggo “Shegiyar yarinya me bakin jinin tsiya, kowa ya tsaneki, nidai Allah ya hadani da bala’i,” Gwaggo ta fada tana harararta. Badiyya saurin maida hawayen da suke niyyar fito mata, ruwa ta diba a tap sannan ta wuce toilet, tana fitowa taje daki ta shirya cikin gown dinta ta atampa, wadda Anty Bilkisu ce tayi mata, kusan duk kayan Badiyya yanzu ita keyi mata, dan rabonta da ganin Ahmad har ta manta, kuma kota tambayi Gwaggo bazata fada mata ba. Shekaru takwas dinnan Badiyya tayisu ne cikin kunci da bakin ciki, first year din Sultan kullun yana gidan, amma kwata kwata Badiyya bata bashi chance ba, har Sultan yayi graduating kullun sai yazo, domin yasan she needed him, she was depressed, but all in vain. Bayan Sultan yayi graduating, daganan life din Badiyya tayi taking drastic turn, dan kuwa koda ganinshi kadai na rage mata wani abun, amma tunda yayi bata kara ganinshi ba har yau. Ahmad kuwa daga lokacin baya zuwa sai lokaci zuwa lokaci, Adama kuwa bata zuwa saidai Gwaggo taje. Badiyya saida tayi shekara biyu a gida, babu wanda ya kaita makaranta, Uncle din Ikhlas ne yayima Gwaggo magana akan zai kaita WTC, yanzu haka shi ke bata kudin transport dana break, duk wata hidima tata shi yake mata.
Bayan Badiyya ta shirya, kitchen taje ta dauko dumamen tuwon dataci da safe, dan tuwo yanzu ya zama abincinta na koda yaushe. Shi zataci da safe, idan ta dawo school ma taci, da dare ma taci. In har taci wani abun to gidansu Ikhlas taje. Bayan ta gamaci ta nufi gidansu Ikhlas domin ta bata hakuri, dan kuwa kullun inhar sukayi maganar maza dole Badiyya taji haushi, ita kuma Ikhlas bata fasa fada mata magana, amma kuma basa kwana haka sai taje ta bata hakuri. Bayan Badiyya ta dawo har tayi Sallar Maghrib, tana zaune ta debo tuwon dare tanaci Kankan yayi sallama “Hajiya, ana sallama da Badiyya,” ya fada da karfi sannan ya koma gaban gida. Badiyya tsaki tayi, sannan ta ayyana ma ranta yau duk bala’in Gwaggo bazata je ba. Gwaggo fitowa tayi tazo ta sami Badiyya falo tanacin tuwo tana kallo “Bakiji Kankan yace ana sallama ba?” Gwaggo tayi mata tsaye. Badiyya turbune fuska tayi “Gwaggo nifa bazanje ba, nifa na tsani maza Gwaggo,” ta marairaice fuska. Gwaggo rike haba tayi, tana mata kallan mamaki “Ah lallai yarinya, kika tsani mazan ubanki, zaki tashi ko saina tattakaki, uban kowa ya tsaneki amma dan kin samu wannan shine har kike wulakanci ko? Sannu,” Gwaggo ta fada tana hararta. Badiyya sanin halin Gwaggo yasa ta mike taje ta dauko hijab dinta sannan tayi hanyar fita, tanajin Gwaggo na cewa tazo tayi kwalliya ta saka gyale, amma kin kulata tayi ta wuce tana zumburo baki. Tana fita taga ya jingina da jikin motarshi, tsaki tayi ta tsaya daga kofa. Takowa yayi yazo har inda take, murmushi shimfide kan fuskarshi “Barka da fitowa,” ya fada yana smirking, hade da cize lower lip dinshi. Badiyya harararshi tayi “Wai Nabil sau nawa zan fada maka na tsane ka, infact ba kai kadai ba, duk maza ma,” ta fada da yar tsawa, tana harararshi kamar idanunta zasu fado. Wani irin murmushi yayi irin na yan daba, kuma ya yan manya “Badiyya wai meyasa kikeman haka ne? Inada kudi, idan kinaso ko nawa zan baki wallahi, Just give me a chance.” Harararshi Badiyya ta karayi “Why can’t you understand, Nabil? I hate you! Men are beguillers, you too will betray me, you’ll leave me, better pack your bullshits and leave. I will not marry, I hate men!” Ta fada da tsawa, hawaye sun gama wanke mata fuska, juyawa tayi ta shiga cikin gida. Nabil kuwa tsayawa

yayi yana kallan inda tabi, wannan irin murmushi mai wuyar fahimta kwance kan labbanshi “Hmm….Badiyya kenan! I love you, and I can do whatever it takes to marry you, I just wanna taste you, I know you’ll be sweet like hell!” Wata irin dariyar mugaye yayi sannan ya wuce ya hau mota, with high speed yabar GRA. Kamar kullun, Badiyya taje makaranta ta dawo, bayan sunyi sallam da Ikhlas, tana shigowa taga Gwaggo zaune tana waya, jin alamun da Ahmad ne yasa ta zauna kusa da ita “Gwaggo dan Allah ki bani shi mu gaisa, wallahi na dade ban ganshi ba,” ta fada a raunane, dan dukda haushin Ahmad din da takeji, tayi missing dinshi sosai.5 Har Gwaggo tayi niyyar kashe wayar sai Badiyya tayi magana da karfi, dan Ahmad din yaji “Dady ina wuni,” ta fada da karfi, hawaye na zuwan mata a idanu. Jin muryar Badiyya daga nesa saidai gaban Ahmad ya fadi, dan kuwa rabon da ya ganta shekara biyu kenan, tunda aka mashi transfer zuwa Lagos bai kara dawowa ba har yanzu, saidai yakan kira Gwaggo, amma bata taba bashi Badiyya sun gaisa ba. Dakyar ya iya bude baki “Yaya, ki bata mu gaisa, it’s been long,” ya fada da kyar, dan idan baya kusa da ita yakanji kewarta, amma daya ganta sai yaji kamar ya kasheta. Gwaggo kuwa jin maganarnan daga bakinshi ba karamin tada mata hankali yayi ba, tunaninta daya; shin maganinsu ya fara daina aiki ne? Dan kuwa Ahmad bai taba maganar Badiyya ba sai yau. Dole tasan abunyi. Da kyar ta mika ma Badiyya wayar, tana mata kallon tsana. Badiyya karbar wayar tayi hannunta na rawa, ta kosa taji muryar Dadynta, dukda yanzu ta tsaneshi, amma hakan bai hanata missing dinshi ba. “Hello Dady,” ta fada muryarta na rawa. Wani irin sanyine ya ratsa zuciyar Ahmad, duk duniya babu abunda yakeso kamar Badiyya. Yana bude bakinshi zaiyi magana, yaji wani abu ya tokare mashi zuciya, dakyar ya amsata a dakile “Lafiya lau Badiyya, ya kike,” ba maganar da yakeso ya fada mata ba kenan, so yake ya fada mata yayi missing dinta, ya fadamata yanaso ya ganta, amma baisan ya akayi maganganun suka tsaya mashi a makoshi ba. Jin muryar Ahmad yasa hawayen da suka taru a idanunta suka zubo, “Lafiya lau Dady, dan Allah yaushe zaka dawo? Zaka kara guduna Dady?” Kukan bakin cikine ya kufce mata, tunawa da irin wulakancin da yayi mata lokacin baya. Yaso ya bata hakuri, ya fada mata yana tare da ita, amma budar bakin Ahmad “Wai meyasa kike hakane Badiyya, abeg bawa Yaya wayar, inada abunda zanyi, kuma idan na dawo me zan maki? I’ll be back soon,” ya fada a kufule, alamun ta isheshi, shi kanshi mamaki abun yake bashi, meyake hanashi expressing mata yadda yakeji? Tanajin haka ta mikama Gwaggo wayar hade da wucewa dakinta, hawayen bakin cikin tunawa da abunda Dadynta yayi mata da kuma murmushin farin cikin amsa mata magana dayayi suka hadu akan fuskarta. Bayan tayi sallolinta, taci abinci, tashi tayi taje gidansu Ikhlas ta fada mata, dan wannan labarine babba, yau tayi waya da Dadynta, after years, kuma bai mata tsawa ko fada ba. Nikam nace Allah sarki Badiyyarmu. Taje gidansu Ikhlas sunata labari Gwaggo ta aiko Kankan kiranta, zata fita tace Ikhlas ta rakata amma fir Ikhlas taki, saboda sanin halin Gwaggo, kullun taje sai ta zageta tas, wai sune munafukai itada Uncle dinta da Anty. Badiyya na fita taga Nabil jingine jikin motarshi, tsaki tayi zata koma gidansu Ikhlas yayi saurin tsayarda ita, ta hanyar shan gabanta “Badiyya ki tsaya mana, wai meyasa kike man haka ne? Meyasa bazaki gane cewar Ina sanki ba? Kullun fa sai nazo gidanku amma kina mani wulkanci, idan akwai wanda kikeso ki fada man mana,” ya fada da yar tsawa, yana mata kallon zaki gane kurenki yarinya. Wani irin wawan tsaki Badiyya taja, hade da galla mashi harara “I wonder me yasa bazakayi embeding maganganuna a wannan karamar kwakwalwar taka ba, nace maka na tsane ka! Nasan ba Alkhairi bane a tattare da kai. Sannan kuma first and last, ni bance kazo gidanmu ba, dan haka karka kara zuwa gidanmu, ka rabu dani!” Tayi spatting angrily, tana wurga mashi kallon tsana. Kafin ya bata amsa saiga Larai tazo, wadda tunda Badiyya ta fara magana tana jinsu, matsowa inda suke tayi “Ke Badiyya baki da hankali ne? Haka ake karbar bako idan yazo wajenka? Ji fa yadda kike mashi magana cikeda masifa,” Larai ta fada cikeda siyasa alamar neman fada wajen Nabil, dan ta lura dan gidan masu kudi ne yaron, ko fatar jikin ta isa ta nuna wannan, balle sutura da motar shi. “Yaro kayi hakuri kaji, matsala kuka samu ne?” Ta tambaya tana kallon Nabil, wanda tun zuwanta yake murmushi, alamar ya kusa cin nasara. Keya ya fara sosawa alamar kunya, “Wallahi Hajiya ni bansan me nayi mata ba, kullun sai nazo amma bata saurarata, kullum maganarta daya; ta tsaneni, ni kuma wallahi da gaske nike santa, da niyyar aure nake zuwa wajenta. Amma Badiyya taki ta bani chance,” ya ida maganarshi yana kallan Badiyya, alamun ta tausaya mashi. Jin batunshi Larai kuwa ta gyara tsayuwa, dan ta lura yaran da gaske yake san Badiyya, kuma da alama ya shirya yin komai gameda ita “To kai yaro ai ba’a haka, manya zaka samu kayi ma magana, karka biye maganar wannan shashashar. Anjima kazo da daddare kayi ma ita Gwaggontata bayani, mahaifinta baya gari, idan ya dawo sai a fada mashi,” ta karasa tana kallon Badiyya, wadda tunda tazo take sauke mata buhun harara cikeda tsana. Wani irin murmushi ya sauke, ganin da alamu ya kusa samun Badiyya “Nagode kwarai Hajiya, Insha Allahu zan dawo anjima. Ga wannan sai abata, wannan kuma naki ne,” ya fada, yana mika mata kudi, dubu biyar nata, na Gwaggo dubu goma. Badiyya tsaki taja ta shige cikin gidan, ita kuwa Larai godiya tayi sannan ta bi bayan Badiyya, tana zaginta akan zata ja masu asara, wannan yaro kashin arziki. Tana shiga ta iske Gwaggo tsakar gida ta fito daga wajen awaki, nan suka zauna ta fara bata

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 6