in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

bazataje Anty Adama ta kasheta ba. Washe gari da sassafe, ta tashi feeling dizzy, dan mafarkin Momynta tayi, tana mata magana akan tayi hakuri, komai na duniya yana wucewa. Mafarkin datayi ya kara mata karfin guiwa nesa ba kusa ba, gata dai yarinya amma Allah yayi mata basira da wayau matuka, kuma hakan yasanya ta kara kafewa a ranta cewar bazata koma gidan Dadynta ba, gara tayita zama anan, koda kuwa kullun Gwaggo dukanta zata rikayi. Tashi tayi, cire kayanta tayi domin tayi wanka, tana zuwa zata shiga toilet Gwaggo ta janyo mata gashi, wata irin karar azaba ta saki, dama gata dajin zafin kai, balle sanyi ya fara shigowa. “Gwaggo kiyi hakuri, ki sakarmin gashi dan Allah,” ta fada, hawaye har sun fara zubo mata, dan ba karamar azaba takeji ba. Kara jan gashin Gwaggo tayi, “Dan ubanki nan bandakin uwarkine da zaki shiga yadda kikeso? Ba kinki bin ubanki ba, to wallahi zakiyi bayani, kuma bari yazo yau, dole ki bishi,” Gwaggo ta fada, tana hankadata waje, janta takeyi har tsakar gida, saida tazo bakin toilet sannan ta wurgar da ita. “Daga yau ga inda zaki rika wanka nan, sannan kuma..” ta fada tana kallon tsakar gidan, da niyyarta tace tazo tayi shara, saidai kuma tasan Ahmad yana iya zuwa kafin ta gama, sannan kuma batada tabbas idan maganin ya fara aiki. Badiyya cikin kuka ta tashi taje ta debo ruwa a tap, zuwa tayi jikinta na kyarma dakyar ta watsa ruwan mai sanyin tsiya, ga wani sanyi da ake tsulawa. A haka jiki na kyarma ta karasa dakinta, mai ta shafa sannan ta dauki kayanta masu nauyi ta saka, dan har zazzabi ya fara kamata, kasancewar sanyin yau gaba daya ya taho. Bayan ta gama sanya kayanta sai tadan kwanta, har ta fara bacci wata irin yunwa ta kulalo mata, nan take ta farka, dakyar ta karasa falon, kasancewar jiya chocolate tasha kawai. A daddafe ta karasa falon, tana fita taga Gwaggo na breakfast, rabewa tayi daga gafe, “Gwaggo yunwa nakeji,” ta fada idanunta na kallan kasa. Kallan banza Gwaggo ta mata, “Jeki kitchen, akwai dumamen tuwo ki dauka,” tana fadar haka ta cigaba dacin abincinta. Tashi tayi taje ta dauko, yadda ta ga tuwon tasan baci zatayi ba, amma sanin halin Gwaggo, da kuma yunwar datakeji yasa bazata iya yin musu ba. Tana yin loma daya tayi sauri ta ruga ta zubda na bakinta, dan jin miyar taushen tayi tsami sosai, kuma miyar tun ta jiyace. Tana dawowa ta matsarda plate din gafe, hawaye na zuba a idonta, “Gwaggo dan Allah ki bani wani abun, wallahi miyar tayi tsami sosai,” ta fada, tana kurama abincin Gwaggo ido. Ganin yadda take kuka yasanya tabawa Gwaggo tausayi, tura mata plate din indomie din tayi, ta gudu ta karba ta faraci kamar mayya, ganin haka Gwaggo tayi mata kwanya akanta, Badiyya bata damuba. Cikinta ko tasawa baiba indomie ta kare, tana lasar plate din Ahmad yayi sallama, da gudu ta ajiye plate din ta ruga ta rungumeshi, saurin yakiceta yayi, ya turata kan kujera. Tsayawa tayi sototo tana kallanshi, mamaki take me tayi mashi? Wasu hawaye ne taga suna zubo mata, binshi inda ya zaune tayi, “Dady kayi hakuri, wallahi ba hakanan naki binka ba, kawai banasan barin Gwaggo ne,” ta fada, hawayenta na kara zubowa. Ahmad kallan banza ya kara mata sannan ya cire hannayenta daga jikinshi, ita Badiyya a tunaninta rashin binshi jiya yasa yake fushi, not knowing zancen ba haka yake ba, abun daga kasa ne. Babu irin magiyar da Badiyya batayi ba amma Ahmad yaki koda kallonta, kuka kam tashashi, haka Gwaggo tazo ta samesu, wani truimphant smile ne yayi plastering akan fuskarta, takawa tayi taje kusa dashi, zama tayi akan kujerar dake kusa da tashi, “Ahmad ya haka? Naga yarinya ta tasaka gaba tana kuka amma ko kallonta bakayi ba,” Gwaggo ta fada, tanama Badiyya kallon kin tashi aiki yarinya. Harara Ahmad ya kara watsama Badiyya kafin ya sauke numfashi, kallon Gwaggo yayi “Wallahi Yaya ni bansan meyasa ba, amma kawai yau naji na tsaneta, ko kallonta banasan yi,” ya fada, yana wurgama Badiyya wani hateful glare. Badiyya jin kalmar tsana daga bakin Dadynta ba karamin bata mamaki yayi ba, kuma wai yace baya san ganinta, bashine yayi mata alkawarin yana tare da ita ba? Ta shiga ukkunta, Dadynta baya santa. Kuka kawai Badiyya keyi, ga wata irin masifaffiyar yunwa dake cinta, haka Gwaggo ta kawo mashi abinci, dan yace ya baro Adama tana barci ko karyawa baiyi ba. Har yagama cin abinci ko kallon Badiyya bai karayi ba, saima idan yaga

tana kallonshi ya wurga mata harara. Tashi yayi zai tafi, da gudu Badiyya ta ruga ta rike hannunshi, cikin kuka ta fara magana “Dady karka tafi please, wallahi yunwa nakeji, kumafa Dady kaman alkawarin kana tare dani, kaceman bazaki barni ba, Dady please karka tafi,” ta fada hade da fashewa da matsanancin kuka, taname rike hannunshi gam. Batayi aune ba taji ya kwace hannunshi daga rikon datayi mashi, sannan yayi wurgi da ita kan kujera hadi da yin tsaki yanamai fita daga falon. Wani irin kuka Badiyya ta saki, shikenan yanzu babu mai santa, tana wannan kukan wahalar ne baccin barawo yayi awon gaba da ita, can cikin baccin taji murya na tasarta cikin kwanciyar hankali, ji tayi kamar tasan muryar, hakan yasa tayi squinting eyes dinta, aikam sai ga Sultan zaune kan kujerar dake kallon tata. Jiki babu lakka ta mike, har tayi mashi murmushi, amma sai abunda ya faru dazu ya dawo mata cikin kai, nan take ta shaida ma kanta akan all men are the same, sun kashe mata Momy, sannan kuma basa holding promise din da sukayi, dole ta fidda duk wani namiji a rayuwarta, dan kuwa shima Sultan am kyaleta zaiyi. Da sauri Sultan ya taso ya zauna, ganin tayi maza ta matsa yasa yayi tunanin ko fushi takeyi, saboda baizo da wuri ba, “Badiyya fushi kikeyi da Sultan am dinki? Saida naje Barhim Anty Adama tace ai baki bisu ba, kinanan, shiyasa kikaga na dade. Kuma kinman alkawarin zaki bisu, meyasa baki jeba? Umm Badiyya? Banayi maki Alkawarin ina tare dake ba, karkiji komai Badiyya, bazan barki ba,” ya fada yana kokarin riko hannunta, da sauri ta mike tana hawaye, har wani jiri take gani saboda yunwar da takeji. Hawaye masu tsananin zafi suka fara zubowa daga idanunta, “Ka rabu dani, kaima you won’t hold onto your promise, you’ll leave me too. Ni daga yanzu bansan kowa ba, duk wani namiji babu ruwana dashi, kun kashe min Momyna, sannan kuma yanzu Dady ya kyaleni, dan haka babu ruwana da kowa. Kuma yanzu babu mai sona, ko Uncle Musaddiq da Aunty Kausar basa so na, tunda har suka barni anan, babu ruwana dakai, ka tafi ka barni,” ta fada tana kuka sosai, a haka tayi hanyar dakinta. Da sauri Sultan ya rike hannunta, “Badiyya, meya faru ne? Ni namiki wani abune? Wallahi Badiyya ina tare dake, bazan taba barinki ba. Wallahi Badiyya ina sanki,” ya fada, dan bai taba tunanin da gaske san wannan yarinyar yar shekara goma yake ba, dan kuwa ya dauka shakuwace tsakaninsu, amma words dinta sunyi hurting dinshi beyond what he think. Jin hannunshi a jikinta yasa ta fara tuna Momynta, gani take shima kasheta zaiyi, nan take ta fara numfarfashi, tana kallon hannunta daya rike, ganin kamar zata suma yasa Sultan sakin hannunta, da gudu ta shige dakinta tana kuka, “Momy,” shine kawai abunda yake fitowa daga bakinta. Sultan kam frenzing yayi a wajen, tunaninshi meyake damun Badiyya? Danshi abun ya daure mashi kai, yanzu kuma tsoronshi take? Ya Allah! Yanda kukanta yake fitowa tare da kiran sunan mahaifiyarta ba karamin taba mashi zuciya yayi ba, yanaji yana gani babu yadda ya iya haka ya fita cikin gidan, with a heavy heart yayi trudging out of

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5