in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

murmushi. *** A yau Asabar aka daura Auran Ahmad da Adama, amma Badiyya batasan wainar da ake toyawa ba, illa taga wasu mata suna shigowa gidan Gwaggo.Badiyya data tashi, itadai taga mutane yan kwarara, abun bai dameta ba, haka ta tashi taje tayi wanka, wajen Gwaggo taje suka gaisa, inda Gwaggo ke cemata breakfast dinta yana kitchen ta rufe mata taje ta dauka. Badiyya haka ta fita cikin nishadi, domin duk kallon banzan da mutanen Gwaggo suke mata bai dameta ba, saboda tasan yau Sultan am zai dawo, kuma yace zaizo ya dauketa suje yawo.+
Bayan ta gama breakfast, zama tayi tana jiran Ahmad, domin dayazo zata ce mashi ya kaita gidansu Sultan am, she’s eager to see him. Tananan zaune, harta fara gajiya, sai ji tayi mutanen Gwaggo na guda, wasu sunata cewa barka an daura aure, kwata kwata abun bai dameta ba, dan batasan ko auran wa aka daura ba, koma ta sani abun ba damunta yayi ba. Hardai ta tashi tayi sallah, ta koma ta zauna, tananan zaune Gwaggo tazo wucewa, mikewa tayi “Gwaggo dan Allah ki kiramin Dady,” ta fada, idanunta na kawo ruwa, dan abun ya fara damunta, ta kosa taga Dadyn shi kanshi balle Sultan am. Gwaggo harara ta zabga mata, tunani take lallai ma yarinyar nan, nufinta batasan wainar da ake tonawa? “Ji yarinya da kilbibi dan Allah, wato uwarki kike tayawa kishi ko? To ai dai ta zama gawa, kuma kema daga zuwa gobe zaki zama gawa wajen uban naki, shegiya kawai. Kuma kiran wayar ne bazanyi ba,” da haka ta balla mata wata hararar sannan ta wuce, tayi gaba abunta. Ita kuwa Badiyya abun daure mata kai yayi ma, ita a tunaninta Gwaggo ta fara santa, tunda an kwana biyu bata mata wani abu ba, suna zaune lafiya, amma laifin me tayi mata yanzu? Dan tasan mutum baijin haushin wani sai an masa laifi. Tana zaune ita kadai, ga wata azababbiyar yunwar dake cinta, rasa yadda zatayi tayi, kuma yadda taga yanayi Gwaggo she knew not to ask, dan tasan sarai kila har dukanta zata iyayi, ga wadannan mutanen da suke mata kallon wulakanci. Har bacci ya fara daukarta sai taji ana tadata a hankali, bude ido tayi taga Ahmad ne sanye cikin babbar riga Milk colour, kyawunshi ya kara fitowa, ga wani haske da yayi mata. Nan take ta fashe da kuka, ga zaman jiranshi da tayi, ga yunwar cikinta data dameta, sannan ga Sultan am tanasan gani. Zama yayi kusa da ita, ya rungumota jikinshi, “Badiyya lafiya? Meya faru? Wani abu aka miki? Fadamin kinji,” ya fada cikin sigar lallashi, dan yasan tabbas wani abu ke damunta. Dago idanunta tayi sannan ta share hawayenta, “Dady, inaso naje gidansu Sultan am, sannan kuma Dady kace man kana tare dani, amma yau nayita jiranka baka zo ba, kuma Dady yunwa nakeji sosai,” ta fada, hade da share hawayen da suka zubo mata. Hannunshi ya sanya ya share nata hawayen, murmushi yayi mata wanda yake bayyan white dentition dinshi, “To Badiyya sai kiyi kuka? Ai gani nazo ko, aure aka daura man nida Auntynki Adama, kinga yanzu sai mu koma tare can gidan ko?” Ya fada yana kallon fuskarta, nan kuwa yaga expression din fuskarta ya chanza, though dama bawai farin ciki take ba, saidai yanzu yaga wani glint of sadness and fear a idanunta. Girgiza mashi kai kawai tayi, alamun Aa, dan gani take ita bazata iya komawa wannan gidan ba, batare da Momynta ba, kuma ma to top it all; da Aunty Adama. Murmushi yayi, dan ya lura fushi takeyi, “Badiyya to tashi kice abincin muje gidan Kamal din,” ya fada yana mikar da ita. Girgiza mashi kai tayi, “No Dady, muje gidansu Sultan am din, sai naci abincin,” ta fada tana mikewa tsaye. Tashi kawai yayi, ya kama hannunta sukayi hanyar fita. Har kun kusa kai bakin kofa yaji Gwaggo ta kwala mashi kira, “Ahmad! Har kazo kuma zaka tafi baka tsaya mun gaisa ba, kodai har angoncin ya fara sakaka manta mutane,” ta fada tana da tahowa kusa dasu. Murmushi yayi, yana janyo Badiyya jikinshi, “Wallahi Yaya, Badiyya ce zankai gidan Kamal, shiyasa,” ya fada yana sosa keya. “Toh ka tsaya kaci abinci mana, ke dawo sai yaci abinci,” ta fada tana riko hannun Badiyya. Badiyya noke hannunta tayi, sannan ta kara shigewa jikin Ahmad, murmushi yayi kawai yaima Gwaggo sai anjima, itama Gwaggon murmushin yake tayi, irin murmushin zaku gane kurinku, sannan ta koma cikin gidan, su kuma su Badiyya suka fita. Bayan Ahmad yakai Badiyya gidan Kamal sai ya wuce hidimarshi, ita kuma bayan Aunty Murjanatu ta kawo mata abinci taci, Khadija sai magana take mata amma ta shareta, sai juye juye take tana kallon inda Sultan zai bullo. Suna zaune har tayi giving in, sai labari suke, kawai sai taji an rufe mata ido. Dariya kawai tayi, dan tasan ba wanda zai rufe mata ido sai Sultan dinta,

“Sultan am, ka bude man ido Allah, nagane ka,” sai dariya takeyi, tsananin farin ciki bayyane kan fuskarta. Zama yayi kusa da ita yana dariya, bude hannunshi yayi alamar tayi hugging dinshi, ai kuwa da hanzari tayi hugging dinshi, sai dariya suke kamar sun shekara basu hadu ba, sai ya dago fuskarta su kalli juna sannan su karra hugging kansu suna dariya.4 Nanfa sukayita labari, kin kawo maganar Firdausi yayi, dan yasan confirm tana iya yin kuka, kuma shi bazaiso hakan ba, labari sukayita yi. Nan take fada mashi wai Dadynta yace zasu koma gidansu na Barhim itada Anty Adama, kuma ita bataso. Dakyar ya lallaba ta akan ta yarda ta bishi suje gidan, idan Allah ya kaimu gobe zaije gidan, zai duba idan tanajin dadi ko babu, idan batajin dadi zai dauketa ya maidata gidan Gwaggo. Sai yamma lis Ahnad yazo ya dauketa, bayan sunje gidan ta iske har an kawo Anty Adama gidan, dama Ahmad ake jira sai su tafi, suna shiga gidan taga ana mata wani kallo, amma sai bata damu ba. Gwaggo da Anty Adama da Ahmad suna zaune a falo, bayan Gwaggo ta gama masu fada, itadai Adama jinsu kawai takeyi, amma farin cikin dake ranta bai misaltuwa. Bayan an gama komai, Badiyya ta tashi zasu tafi, sai ta tuna pack din chocolate din da Sultan ya bata a daki, komawa tayi da niyyar dauka, bayan ta dawo har zata fita sai taji Gwaggo tanama Adama kus kus, “Adama kina jina? Kiyi duk yadda zakiyi yau abun ya faru, saboda so nake zuwa gobe ki fara cin uwarta, sannan kuma ki tabbatar kin gallaza mata azaba, kiyi mata azabar da har sai ta mutu shegiyar.” Aikuwa jin hakan ba karamin tadama Badiyya hankali yayi ba, taji ance harta mutu, to kuma tasan mutuwa itace abunda Baba, Mama, da Momynta sukayi. Does that means idan ta mutu bazata kara ganin Sultan am ba? Bazata kara ganin Dadynta ba? Ai kuwa bazata bisu ba!. Gwaggo jin shirun yayi yawa, sai ta shigo Falon, ganin Badiyya tayi zaune tanashan chocolate dinta, hankalinta kwance. Wani uban salati ta doka, “yanzu Badiyya anacan ana jiranki amma kika zauna kina shan chocolate.” Badiyya jiyowa tayi ta kalleta, “Gwaggo nifa bazani ba, ina nan gidan,” tana furta haka ta cigaba dashan chocolate dinta kamar ba abunda ya faru. Dukkansu sun taru kan Badiyya amma Fir taki yarda ta bisu, Ahmad ba irin pleading dinta da baiyi ba amma tace wallahi ita bazata ba. Cikin fushi Ahmad yace, “Badiyya wai bazaki tashi mu tafi ba? Wallahi zan zane ki, ki tashi nace!” Ya fada da tsawa, amma Badiyya ko gezau batayi ba, bata kuma da niyyar motsawa. Badiyya yan kafiyar sun motsa, mikewa tsaye kawai tayi, “Dady kana so na? To indai kana so na, kuma kanasan ka ringa ganina kullun to ka barni na zauna anan, wallahi bazan biku ba,” hawaye har sun fara fitowa daga idonta, tana fadan haka ta wuce dakinta. Ahmad ganin tana kuka ya sanya yayi tunanin ko Momynta ta tuna, kuma ta bata mashi rai, bazai iya rarrashinta ba yanzu, dan haka kawai ya fita abunshi, Adama da Gwaggo suka mara mashi baya, Gwaggo sai assuring ma Adama take akan zatasan yadda za’ayi Badiyyar tazo zuwa gobe. A haka suka bar gidan.Gwaggo bata kara cema Badiyya komai ba, saima harararta takeyi, a haka sukaje suka kwanta, ita kuma Badiyya ta kuri aniyar saidai ta mutu gidan Gwaggo amma

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5