in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

Gwaggo ta fada da alamun damuwa saman fuskarta. “Wannan ai ba matsala bace, tunda Juma’ar ta kusa, yanzu nasan maganin Malam ya fara aiki a kanshi, dayazo ki mashi maganar auren, in yaso kafin a kaita sai a anso na rabasu,” Larai ta fada tana murmushi, itadai Adama binsu da idanu kawai take, domin Allah kadai yasan irin farin cikin dake cikin ranta, ba karamin temako suka mata ba. Anan suka jaddade magana akan zata mashi maganar auren, sannan kuma za’a anso magani ranar Friday. Badiyya na zuwa ta gaishe dasu, a dakile suka amsa, itama uwar gayyarma; Adama harara ta watsa mata, sum sum Badiyya ta wuce cikin gida. *** Da daddare Ahmad yazo, Badiyya da gudu ta rungumeshi, bayan sun gamacin abinci, sai Gwaggo tazo ta zauna kan kujerar dake kusa dashi, kallon Badiyya tayi tana murmushi “Badiyya jeki ciki zamuyi magana kinji,” ta fada, tana murmushi. Ahmad baice kala ba, domin yana tunanin ko hakuri zata bashi, kuma bai kamata ta bashi hakuri gaban Badiyyar ba. Bayan Badiyya ta tashi, Gwaggo tayi wearing lugubrious face “Ahmad shawarace nazo maka da ita, mekai hana ka kara aure, kaga yarinyar nan tana bukatar gatan uwa, ni kuma kaga kashina ya fara sanyi,” ta fada tana kura mashi ido. Numfasawa yayi, sai yaji duk haushin Gwaggo dayakeji ya daina “To Yaya kina ganin ko zanyi aure yanzu, wa zan aura?” Ya tambaya, yana palming face dinshi da hannanyenshi, alamun rasa mafita. Wani murmushine ya subucema Gwaggo, ganin hakarta ta cinma ruwa “wannan ai ba matsala bace, Adama diyar Larai mijinta ya saketa, ai inaga sai ka aureta,” ta fada, tana kallon fuskanshi domin gani ko yanayinshi zai canza, amma sai taga babu. “Kina ganin zata kula da Badiyyar sosai?” “Eh Insha Allahu.” “To shikenan Allah ya kaimu, inaso asaka kusa sosai, saboda zuwa gidannan kullun yanamin wahala, gara mu koma tare gaba daya,” “To shikenan, zanma Larai magana, in yaso ko ranar Saturday sai a daura auren, nasan bazata ki ba,” fadar Gwaggo, ji take kamar ta daka tsalle dan dadi. “Allah ya kaimu.” A haka Badiyya ta cigaba da rayuwarta, kullun sai Ahmad yazo ya fita da ita, wani lokacin da Adama suke fita, amma hakan bai taba damunta ba, domin ganin yadda Adama ke mata faram faram a gaban Ahmad. Kullun shi yake zuwa ya dauketa ya kaita makaranta, wani lokacin yakan kaita gidansu Sultan am, sai ta dade sunyi wasa da Khadija sannan ya maidata gida. Musaddiq ma yazo, lokacin dayazo basunan sunje yawo, sai Ahmad ya kira, a lokacin yace suna gidansu Sultan, koda Musaddiq yaje gidansu Sultan din sai yaga Adama tare dasu, yarda tayi mashi wani kallo lokacin da taji cewar shi dan uwan Firdausi ne abun ya bashi mamaki, amma bai kawo ma ranshi komai ba. Yau Friday, yau Gwaggo da Larai zasuje karbo maganin raba Badiyya da Ahmad. Koda Badiyya ta tashi da safe, toilet din dake tsakanin dakinta dana Gwaggo ta shiga, dan zuwa yanzu ta gama sakin jikinta da Gwaggo, ta gama yarda Gwaggo na santa, yanzu kowa yana santa. Wanka taje tayi, tana fitowa ta iske Gwaggo tayi hanyar dakinta, “Gwaggo ina kwana,” ta gaidata tana murmushi, itama Gwaggo murmushin ta mata sannan ta amsata, hade da patting kanta, tana mata kallon kaskanci, irin kallon yarinya jin dadinki ya kare. Badiyya murmushi tayi sannan ta wuce dakinta, zuwa tayi ta shafa manta, unifoam dinta ta duba sai taga bata gansu ba, can ta tuna Ahnad jiya yakai kayanta wajen wanki. Tunawa da wani set din unifoam din dake kasan akwatinta tayi, zuwa tayi ta zakulosu, tana fiddowa camera ta ta fado, saida taji gabanta ya fadi, nan ta tuno da Momynta, share hawayenta tayi, sannan tayi smiling ruefully hade da maida cameran inda take. Tana saka kayanta tana tunowa da Momynta, amma yanzu kwata kwata abun bai damunta, saboda daman dan bata da mai santa ne, amma yanzu ga Dadynta, kuma ya mata alkawarin yana tare da ita. Tana gama saka kayanta ta fita falo, breakfast dinta; chips da kwai sai cup din tea tagani, murmushi tayi, dan yanzu kan Alhamdulillahi. Tana gamaci taji sallamar Ahmad, gaisawa sukayi shima ya zauna yanacin abincin daganan sukayi ma Gwaggo sallama suka tafi. saida ya siya nata abun break kamar kullun sannan yake fada mata idan an tashi zai ajeta gidansu Sultan, saboda Gwaggo ta fada mashi akan zataje unguwa yau, kuma bazata dawo ba sai yamma. *** Bayan an tashi yaje ya dauko Badiyya, gidansu Sultan ya kaita sannan ya wuce hidimarshi, yana sheda mata akan da marece zai dawo ya dauketa. Murjanatu, wadda su Khadija suke kira da Aunty, ita tasaka Badiyya tayi wanka sannan ta bata kayan Khadija ta saka. Bayan sunci abinci suna zaune suna kallo wayar Aunty tayi ringing, ganin sabuwar number yasa taki dagawa har saida ta tsinke, ganin me kiran yaki dainawa yasa ta dauka, can cikin rai tayi sallama “Assalamu Alaikum, wake magana dan Allah?” Daga dayan bangaren, muryar favourite nephew dinta ya cika mata kunne “Aunty ina wuni? Ya gida, Sultan ne,” ya fada, kana iya jiyo yadda yayi murmushi. “Ahhh Malam Sultan, ya makaranta? Sai yau aka tuna damu ko,” Aunty ta fada murmushinta na fadada. Badiyya jin an kira sunan Sultan yasa tayi saurin dagowa, sai yanzu takejin kewarshi, tasan da yananan zaiji da ita sosai. Bayan sun gaisa da Aunty, anan yake shaida mata sun gama exams yau, ranar asabar zai biyo motar safe ya dawo, dayake a government school din Mashi yake schooling, yanzu yana

SS2, wanda sun gama exam din third term. Khalil aka fara bawa wayar suka gaisa sannan Khadija ta amsa, har zai katse wayar Khadija tayi caraf “Yaya, bakace abawa Badiyya ba,” ta fada tana kallon Badiyya, wadda tun lokacin da suka fara wayar take kallonsu, kawaidai ta kasa cewa abata wayar suyi magana ne. “Badiyya nanan? Yaushe tazo?” Ya tambaya a rude, domin ya dade yana mafarkai da Badiyya, kullun tana kukan neman taimakonshi, but bai kawoma ranshi komai ba, domin tunanin rashin Dadynta a kusa dasu ne yasa yake mafarkai haka. Nikam nace wannan matsalar babba ce, Sultan dinmu. Mikama Badiyya wayar Khadija tayi, dayake Khalil da Aunty tun dazu sun shiga kitchen tare, to tasan abun dadi za’a hada mashi, shiyasa itama ta bisu. Karbar wayar Badiyya tayi, idanunta har sun fara cikowa, tayi missing Sultan beyond words. “Hello, Sultan am,” ta fada murya can ciki. “Badiyya ya kike? Ai nayi fushi, tunda baki saka Momynki ta kirani ba, bakiyi missing dina ba ko?” Ya tambaya, yana nuna alamun baiji dadin rashin kiranshi da batayi ba. “Momy ta rasu Sultan am, yanzu ni kadai ce, dagani sai Dady, ina gidan Gwaggo yanzu,” sai kuma ta fashe da kuka, shasshekar kukanta kadai ake ji. “Badiyya kiyi shiru kiman magana, wa kuma ya rasu?” Ya tambaya, gaba daya ya rikice, tsoronshi daya Allah yasa kar ace Mamanta ce ta rasu. “Sultan am, Momy ce ta rasu, Momy ta tafi ta barni, yanzu ni kadai ce, banda mai sona, kowa ma tafiya zaiyi ko Sultan am?,” ta fada, wani kukan na subuce mata. Iyakar rudewa Sultan yayita, ashe shiyasa yaketa mafarkinta? Ashe shiyasa yaketa mafarkin tana kuka tana neman taimakonshi?. “Badiyya ki daina kuka, kiyi hakuri kinji, kuma ni ina tare dake, bazan barki ba Badiyya,” ya fada a kasalance, gaba daya jikinshi ya mutu, ji yake kamar shima yayi kukan. Badiyya share hawayenta tayi, wani kasalallen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, murna take Sultan dinta yayi mata alkawarin bazai barta ba, yace yana tare da ita. “Sultan am, yaushe zaka dawo? Nayi missing dinka sosai,” “Gobe zan dawo Badiyya kinji, zanzo da kaina in daukeki muje yawo,” ya fada hade dayin murmushin karfin hali. “Allah Sultan am, naji dadi sosai,” ta fada tana washe hakoranta. Haka suka cigaba da wayar, sai kokari yake ya sanyata dariya, aikuwa ta biye mashi sukayita dariya, suna gamawa takai ma Aunty wayar. Ba’a dade ba, Ahmad yazo ya dauketa suka tafi. A bangaren su Gwaggo kuwa, bayan sunje sun karbi maganin, anan Malamin yake shaida masu lallai su tabbatar auren bai wuce sati daya ba, dan maganin zai iya lalacewa, kuma samunshi wahala yake. Nan sukayi godiya suka tafi, wanda suka tsaida akan Gwaggo zata fadama Ahmad cewar zatayi tafiya zuwa Niger, amma mezai hana ayi auren gobe, in yaso sai su koma tare da Badiyyar. Su Ahmad na shigowa sukaga Gwaggo ta jabga uban tagumi, matsawa kusa da ita Ahmad yayi, damuwa shimfide kan fuskarta “Yaya, lafiya kuwa? Meya faru kikayi tagumi haka?” Ya tambaya yana riko hannayenta, Badiyya ma zama tayi kusa dasu tana kallon Gwaggo. Gwaggo numfasawa tayi “Hmmm bari Ahmad, wallahi wata aminiyatace, ta koma Niger shekara biyu da suka wuce, yau aka kirani akace ta rasu, yanzu bansan yadda zanyi ba,” ta fada hade da share kwallar karya. Jum Ahmad yayi, yama rasa mafita shima, dan daga gani Gwaggo ta damu sosai “To yanzu Yaya, ya za’ayi?” Ya fada yana kallonta. “Taimakamun zakayi, ka bari a daura auren nan gobe, in yaso sai ku tafi gidanku can, kaga bazan iya barin Badiyya ba ai,” ta fada tana kallon Badiyya. Shiru yayi sai can yace “To shikenan, Allah ya kaimu,” cewar Ahmad yana kallon Badiyya, fatanshi daya Allah yasa Adama ta kula da ita. “To nagode Ahmad, dama munyi magana da Larai tace sun yarda suma,” ta fada tana

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5