in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 4

Washe gari da safe, Gwaggo cikin mutunci ta tayarda Badiyya, Badiyya cikin mamaki ta tashi. Tashi tayi har ta fita domin shiga bayin tsakar gidan, sunanta taji Gwaggo ta kira “Na’am Gwaggo,” ta amsa hade da komawa cikin dakin. “Badiyya ki shiga nan kiyi wankan, sannan kuma daga yau karki kara shara da wanke wanke har sai nace kiyi,” Gwaggo ta fada, tana nuna mata bayin dake tsakanin dakunansu. Badiyya nodding kanta tayi, sannan ta wuce sum sum ta shiga ciki, tana shiga ta kunna tap din ruwan zafi, bayan ta sirka ruwan, tana watsawa tasauke wata irin ajiyar zuciya, domin raban da jikinta yaga ruwan zafi harta manta, tunda tazo gidan Gwaggo bata kara wanka da ruwan zafi ba, kuma gashi an fara sanyi sosai. Tana wanka ta fito, dakinta ta shiga domin shiryawa, bayan ta shirya cikin unifoam dinta tsaf, tayi kyau abunta, domin dama Badiyya ba daga bayaba wajen kyau, though chocolate skin gareta, amma Allah ya mata kyau kamar mahaifiyarta, matsalarta daya; hancinta yanada tukunya. Like kaman daga saman hancin ya bude haka. Dukda ta shirya, hakan bai saka ta fita ba, domin dukda sauyin halayar data gani wajen Gwaggo, hakan bai hanata yin dari dari da ita ba. Tana zaune taji Gwaggo ta kwala mata kira “Badiyya zokici abinci kinji yata,” Gwaggo ta fada cikin murya mai sanyi, muryar da bata taba jinta da itaba. Badiyya saida tayi jim… sannan ta mike domin fita, mamaki take anya Gwaggo ce ta kirata, domin bata taba jin irin wannan side din na Gwaggo ba. Tana fita taga Ahmad ya hakimce kan kujera, ga plate din dankali da kwai yanaci, fuskarnan daure ba alamun nurmushi a tattare dashi. Yana dagowa ya kalleta, wani murmushi ya sakar mata, wanda itama ta maida mashi, amma tayi tsaye bata karasa wajen shi ba, saida Gwaggo ta dafata “jeki mana yar nan, je kuci abinci da Dadynki,” Gwaggo ta fada, yadda muryarta ta fito yana nuna tabbacin ba’a san ranta tayi maganar ba. Badiyya murmushi tayi mata sannan ta wuce kusa da Ahmad, “Dady ina kwana,” ta fada tana zama kasa, yana ganin haka shima ya sauko ya zauna, murmushi me tsada ya mata “Badyna ta tashi lafiya kalau ko?” Ya tambaya yana dago fuskarta data sauke kasa. Ganin hawaye a idonta yasa yayi matukar razana, “Badiyya meya faru? Meyasa kike kuka?” Ai bai ida maganar ba yan hanjin Gwaggo suka kada, dan ita tasan bata mata komai ba yau. Share hawayenta tayi, ta kalleshi, smiling ruefully “Dady, Momy na tuna, tunawa nake lokacin da muke zama tare da ita a kasa muna breakfast,” tana fadan haka ta fashe da kuka, janyota yayi a jikinshi, zuciyarshi na bugawa, wani irin daci yakeji a cikin ranshi.
“Badiyya kiyi hakuri kinji, addu’a zakiyi mata Badiyya. Tunda gani, inanan tare dake insha Allahu,” ya furta yana mata murmushi. Dagowa tayi tana kallonshi, goge hawayen idonta tayi “Dady da gaske kana tare dani? Da gaske bazaka barni ba?” Ta fada a hankali, dan gani take tunda Momynta, wadda tafi kowa santa, ta tafi ta barta to kowa ma zai iya tafiya. “Da gaske nake Badiyya bazan tafi na barki ba, na miki alkawari,” ya fada yana murmushi. Miko mashi karamin hannunta yayi alamar su kulla alkawari, shima mikoma mata yayi, suna kullawa a tare suka fashe da dariya, ya rungumeta a jikinshi. Gwaggo wacce tana zaune kamar statue tana kallonsu, bakin ciki kamar ya kasheta. Basu kulata ba suka gamacin abincinsu sukayi hanyar fita, da Gwaggo taga dai da gasken gaske ba magana zasuyi mata ba, “Allah ya bada sa’a Badiyya,” ta fada kamar an tursasata. Well tursasata akayi mana, tunda tasan halin Ahmad, tsaf kula yake da yarda take treating Badiyya. Juyowa tayi tace “Ameen Gwaggo,” har yanzu murmushi baibar fuskarta ba, ji take kamar matsalarta ta kare, tunda har Dady ya mata alkawarin bazai barta ba. STORY CONTINUES BELOW  Kankan suka gani yana sharar tsakar gidan, bayan sun gaisa suka hau mota, as usual Ahmad saida ya

siya mata abun yin break a school sannan suka wuce Saldefi International School. *** Bayan Ahmad ya daukota makaranta saida suka biya gidansu Sultan, wanda har yanzu kanwar Maimuna tananan bata tafi ba, tunda ta gama service dinta. Abinci sukaci sannan, bayan sun gama wasa da Khadija, sai Ahmad ya dauketa suka tafi gidan Gwaggo. Suna isa suka iske Kankan bakin gate yayi tagumi, alamar yunwa ta isheshi “Ranka ya dade in wuni, ai Hajiyar bata nan,” Kankan ya fada yana sosa keya. “Ina kuma taje? Yarinyar kuma ya za’ayi da ita?” Ahmad ya fada, dan ya gane take taken Gwaggo, wata ya bata mata rai, itama dole ta rama. “Wai taje barka ta dawo, amma tace Badiyyar ta shiga nan gidan, ta fada masu zatazo,” ya fada yana nuni da gidan dake kusa dasu. “To shikenan Badiyya, ki shiga kinji, ni kuma anjima zan dawo in duba ki,” ya fada a kasalance, domin yanzu wata irin kasala da faduwar gaba yaji sun sauko mashi. Hugging dinshi Badiyya tayi sannan ta nufi bakin kofar gidan. Ya juya zai tafi Kankan ya fara inda inda, Ahmad ya gano logon shi, domin dama kusan kullun shi yake bashi kudin abinci yanaci. Dan Gwaggo ba ruwanta da wannan, kuma komin nisan waje zata aikeshi yaje a kasa ya dawo, amma bata bashi abinci. Mika mashi dari biyar Ahmad yayi sannan yayi mashi sallama, hade da bashi sakon gaisuwa ma iyalinshi, domin Kankan mutun ne me mutunci da barkwanci. Badiyya na shiga gidan ta shiga kwala sallama, wata yarinya ta fito wacce take sa’arta a shekaru, kallo daya tayi mata ta ganeta, da gudu ta ruga ta rungumeta “Ikhlas! Yaushe kikazo nan? Ina kishiyan Ummanki?” Badiyya ta furta with full enthusiasm, dan akwaita da rikon face din mutum. Nanfa suka shiga gaisawa, Ikhlas na bata labarin akan nan gidan kanin Abbanta ne, yanzu wajenshi taje zama. “Badiyya, ina Momy?” Ikhlas ta tambaya tana murmushi, domin har yanzu abunda Firdausi tayi mata baibar ranta ba. Ai nanfa Badiyya ta fashe da kuka, Ikhlas da batasan dalilin kukan ba amma itama ta biye mata, nan sukayita kuka ba wanda ke lallashin wani har saida Aunty Bilkisu matar kanin Abban Ikhlas ta fito, dariya ta kwashe dashi sannan ta fara basu hakuri, nan Badiyya ke fada mata akan Momynta ta rasu. Dasu Gwaggo suka dawo, sai ta aika Kankan ya kira mata Badiyya, sunanan tsaye suna magana itada Larai da Adama, “To yanzu kunga Malam yace sai ya kusanceta sannan za’a iya rabasu da diyar, kuma shi bai irin wanann aikin, dole mu jira Juma’a,”

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 3

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 5