in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 10

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 10

Dakyar likitocin suka samu numfashin Gwaggo yayi stabilizing, kafin suka mata other necessary abubuwan da suka kamata. Inda Allah ya taimaka mata babu karaya ko daya, saidai buguwar da tayi, ga yunwa da tayi mata mugun kamu.

Kudin ya biya kafin ya wuce gidanshi, sai bayan sallar juma’a kafin ya biya ya siyo mata abinci ya wuto asibitin, dan yasan in yace nasifaffiyar matarshi ta mishi to kishinta sai ya motsa, bama zata yarda wai accident ya samu ba, to it’s better ya siyo kawai hankali kwance.

Yana shiga dakin yaga ta farfado, amma babu abunda ke fita daga idanunta banda hawaye, kuka take a hankali irin mai taba zuciyar mai kallonta, dan ko sauti daya baya fita daga bakinta. Kukane wanda zuciya ta dade tanayi amma idanu basa bata hadin kai, kukane mai cike da tarin dana sani da takaici.

Karasowa yayi bakin gadon, har ya zauna batasan ma ya zauna ba, wani irin tausayinta ne ke ratsa dukkan wata gabba ta jikinshi, zuciyarshi tayi wata irin mutuwa. A hankali ya buda baki kamar bai san maganar “Baba, dan Allah kiyi hakuri, wallahi kuskure ne. Ba’a san raina nayi maki haka ba,” ya karashe maganar da raunin zuciya.

A hankali ta bude idanunta, ganinshi sai ya tuna mata da Ahmad dinta, wasu hawayen bakin cikine suka kara zubo mata. “Ba kuka nake dan ka bugeni ba yaro, kuka ne nike na bakin ciki da dana sani, kuka ne nike wanda zuciyata ta dade tanayi sai yau hawayen suka zubo, kuka ne wanda inba mahalicci na ba babu wanda yasan yanda zuciyata kemin kuna. Kuma ni ko kadan bugenin da kayi bai batamin rai ba, saima alkhairin daya zamemin, dan kuwa na samu koda na awanni ne na kwanta a lafiyayyen gado, sannan kuma na samu albarkacin rufi mai sanyi ba irin wanda rana ke mana rumfa ba. Nagode maka kaji, Allah ya shi albarka. Karka sake ka cuci wani rayuwarki, dan kuwa komin dadewa sai ka girbi abunda ka shuka,” ta karashe maganar tana wani gunjin kuka.

Dabas ya ida zama akan kujerar, zuciyarshi wata irin karewa tayi, saida ya tattaro dukkan natsuwarshi kafin ya fara magana cikeda natsuwar da yake da ita “Baba, yadda naga yanayinki kina cikin matsala, karkiji komai, ki fada mani abunda yake damunki, ko nasan ta inda zan taimaka maki,” yadda yayi maganar kawai saida taji wani irin sanyi yana ratsa zuciyarta, dan rabon da taji wani ya furta kalmar kulawa gareta an dauki dogon lokaci.

Cikin kuka ta fara magana “Yaro nidai sunana Binta. Iyayenmu suka rasu suka barni da kanina, na kula dashi tun yana yaro har ya girma yayi aure shima ya haifi diya. Allah ya saka mani tsanar matarshi; wanda hakan zugar aminiyata ke rura wutar tsanar, dan duk abunda zanma Fiddausi bata taba daina girmamani. Bayan rasuwar mijina ya daukoni ya siyamin gida a GRA nake zama, duk wani jin dadi na duniya Ahmad ya bani shi, sutura kuwa saidai in bayar. Ba kowa nake girmamawa ba sai wanda yake da arziki, duk wanda yake karkashina baya jin dadina.

Ana haka aka kashe Firdausi, sai kuma yan uwanta suka zargi Ahmad da kisan, saboda saida ya saketa kafin aka kasheta. Ni na bukaci a bani rikon yarinyarta Badiyya, badan komai ba saidan shawarar da aminiyata ta bani akan yin hakan kadai ne zaisa na huce bakin cikin dorawa dan uwana laifin kisan da akayi. Yan uwanta basuso ba haka suka bani, tun lokacin na fara kuntata mata, duk inda nasan zataji dadi sai na toshe, da naga Ahmad bayajin dadi sai mukaje wajen boko aka rabasu dashi, kuma muka hada auren shi da diyar aminiyata, a cewarta sai diyar ta dauka daga inda na tsaya, wajen kuntata ma Badiyya.

Cikeda rashin sani ashe wajen toshe ma wani farin ciki na budema kaina shafin bakin ciki. Dan kuwa yanzu Badiyya tayi aurenta cikin kwanciyar hankali, ni kuma Adama sun rabani da Ahmad. Hakan yasa na saida gidan na dawo cikin gari, komai nawa yanzu ya kare, duk jarin dana kama saiya lalace, na koma rayuwar dana dade ina son naga Badiyya cikinta, na koma kaskantacciyar dana dade ina fata naga Badiyya ta zama, na koma miskiniya wadda bata da komai, wanda ada kallon da nakema Badiyya kenan; ganin bata da uwa, uban kuma ya zamar mata hoto. Ashe Allah ba azzalumin bawanshi bane, sai gashi kaikayi ya koma kan mashekiya.”

Tunda ta fara magana yake juya kanshi, tausayinta da kuma kyamar abunda ta aikata yana lullube zuciyarshi. Ganin tayi shiru tana kallon ceiling kafin ta dago ta mishi magana “kaima yanzu ka tsaneni ko? Dama ai karshen alewa kasa. Nasan babu sauran wanda zai jikai na bayan ban jikan marainiyar Allah ba. Zanje naita istigfari, har ciwon yunwa ya kasheni,” ta karashe maganar, a lokacin wasu hawayen nadama suka kwace mata.

Sun dauki tsawon lokaci kafin ya fara magana “Nima maraya ne, banda iyaye. Iyayen matata su suka rikeni a matsayin driver dinsu, suka sakani makaranta har Allah ya kawoni a yanzu. Sunan matata Hannah, nikuma sunana Sagir. Idan bazaki damu ba zan kaiki gidana ki zauna, sai ko aikace aikace ne ki rika taya matata, dan bazata yarda ki zauna hakanan ba. Kasancewarta mai tsananin kishi da fada,” abunda ya iya fada kenan, dan kuwa a ganinshi shine best solution, bazai taba iya barin wannan matar a haka batare da taimaka mata ba. Inma yayi hakan, to he won’t ever rest in peace.

A wahale ta mike, “babu komai wallahi. Nagode, Allah ubangiji ya saka maka da mafificin Alkhairinsa. Kuma aiki ko wane irine zanyi mata wallahi. Allah yayi maka albarka,” ta fada wasu hawayen farin ciki na zubo mata, atleast zata samu muhalli da abinci mai kyau, dan duk wani jin dadin duniya tayi sallama dashi. Kuma zata jure wahala, komin tsananinta.

“Bari naje muji in zasu iya sallamarki,” yana fadin haka ya mike, zuciyarshi ya raya mashi irin fitinar da zai tadda in yakai Gwaggo gida.

***

Zuwa yanzu Badiyya tayi kyau tayi fresh, cikinnan yadan taso ba kamar da dayake kamar wani kumburi ba. Baba baraka ta tare gidan, dan kula da lafiyarta da kuma aikin magani da addu’o’in da sukeyi akan Ahmad. Kullum sai tasha wasu magunguna, dan itama akwai abubuwan dake jikinta, sannan basu kwantawa basuyi salloli da addu’o’i ba.

Kamar kullum suna daki itada Sultan sun gama sallah suna lazimi, yatsina fuska tayi ta kalleshi “Sultan am, yaronka na bukatar abun kwadayi fah,” ta fada cikeda zolaya, dan tasan babban tashin hankalin Sultan a yanzu bai wuce ta bude baki tace tana san wani abu ba. Dan bata taba neman abu mai sauki ba.

Hannu ya dora a hannu cikeda nuna ‘na shiga uku’, kafin ya fara magana “kai kuwa dan baba ya zaka min haka? I thought mun gama yin agenda dakai cewa babu neman abu mai wahala cikin dare sai safiya ko?” Yayi wata irin muryar tausayi, hannunshi yana kan cikin Badiyya.

Itana hannunta ta dora saman nashi idanunsu nakan cikin, wata irin kaunar juna ce ke zagaye su. “Kai dan Baba kaji. Mudai ai tuwan dawa mukesan ci miyar karkashi, sai kuma gurya. Su baba ayi hanzarin nemo mana,” ta fara tana dariya, ganin kallon tsoron da Sultan ya bita dashi. Babban tashin hankalin da yake ciki bai wuce inda zai samo dawar da kanta ba balle karkashi, gurya kam baa maganar nemanta ai.

Marairaice fuska yayi “Dan baba dan girman Allah ka taimaka min, kuyi hakuri ku chanza da abunda yake cikin gidannan, gobe It’ll be the first thing da zan fita nemowa,” ji yake kamar yayi kuka, dan yasan sometimes in ta fara abu haka kamar wasa, to ranar babu bacci sai kuka in baa samo ba.

“Dan Baba muyi ma baba hakuri ko? A bamu custard, amma sai an cika sugar yadda zamu rage zafi,” ta fada tana gwalo, dan tasan Sultan ya hanata shan sugar.

“Eh naji din. Zakusha, amma na yau kawai. Abbu na godiya dan baba,” ya fada tare da pecking cikin, kafin ya fita dan zuwa kitchen.

In a minute ya hado mata ya kawo, a hankali take sha shi kuma ya cigaba da addu’o’in shi. Tana gamawa anan kan dardumar ta fara bacci, kallonta kawai yayi hade da murmushi kafin ya cigaba da abunda yakeyi.

Ya gama ya dauketa ya cire mata hijab din, kan gado ya kwantar da ita, kafin ya shiga toilet dan yin wanka, wata irin kara ta saki wadda yayi daidai da fitowarshi daga toilet.

“Daddy!” Ta fada cikeda kara, nan take hawaye suka zubo mata, sai kuka take cikeda firgici da tsoro.

A hankali ya girgizata akan ta fadamashi, bude bakin da zatayi sai amai, aman kawai takeyi kamar yan cikinta su zubo, ga wata irin zufa dake keto mata dukda ACn dake cikin dakin.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 9

MADADI CHAPTER 1