in

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 1

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 1

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 1

Yarinya ce karama ta fito daga cikin makarantarsu, tana ta murmushin murnan ganin mahaifiyarta. Da gudunta ta ruga ta rungume ta tana mai fadin “Momy, ina wuni” mahaifiyarta tai murmushin farinciki hade da amsata. “Lafiya kalau my Bady, ya school?” Da haka ta dauketa ta saka ta cikin mota suka tafi. Suna tafe Badiyya nata mata surutu har suka karasa gidansu dake Barhim Estate, kuka road, a cikin jihar katsina. “Momy, ina Dady yake?” Badiyya ta tambaya tana me cire kayan jikanta. Ladi me aiki tazo ta dauki kayan tai wajen daya kamata dasu. “Bady, Dadynki yana wajen aiki, amma ya kusa dawowa.” Mahaifiyarta ta bata ansa tana me shiga cikin kitchen. “Kizo kici abinci Badiyya, kafin lokacin Islamiya yayi.” Ta fada da karfi domin yar tata taji. “Momy, bari naje nayi wanka tukun, jikina yanamin ba dadi.” Badiyya ta amsa hade da ruguwa zuwa dakinta.
Mahaifiyarta me suna Fiddausi, wadda a yanzu taji wani irin mugun bugawar zuciyar ta dakyar ta amsa yarinyar ta. “To Badiyya, kiyi sauri.” Da sauri taje parlour ta bude jakarta domin ta dauki wayarta, fatanta daya Allah yasa ba Dadyn Badiyya bane wani abu ya sameshi, domin zuciyarta taki daidaituwa. Cikin hanzari ta dauki wayar ta kara a kunnenta. “Hello Ahmad, da fatan kana lafia ko?” Ta fada a yayinda ya amsa wayar. “Lafiya kalau Fiddausi, wani abu ya faru ne?” Ya tambaya a hargitse, domin yadda yaji muryarta yasan ba lafiya ba. “Babu abunda ya faru wallahi, kawai naji bugun zuciya ta ya karu, shiyasa nai tunanin ko wani abu ne ya sameka.” Ta bashi ansa tana me goge hawayen dake fitowa daga idonta. “Babu komai Firdausi, ki kwantar da hankalinki, ganinan dawowa gidan. Amma kina iya kiran gida kiji ko lafia.” Ya bata amsa, domin ya kwantar mata da hankali. “To shikenan, Allah ya tsare.” Ta amsa a takaice tana me karar da call din. “Badiyya kiyi sauri.” Ta fada da karfi, yayinda take dailing number kanwarta Kausar. “Hello Kausar.” Ta fada a hankali. “Na’am Maman Badiyya.” Kausar ta ansa a raunane. “Kausar lafiya naji muryarki wani iri?” Firdausi ta tambaya a gigice, bugun zuciyarta na tsananta. “Yaya Fiddi.” Ta fada sai kuma ta tsaya. “Baba ya rasu.” Ta fada hade da fashewa da wani matsanancin kuka. “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un.” fadar Firdausi hade da fasa wata irin kara, wayar dake hannunta ta sulale ta fadi. Tana nan zaune hawaye na kwaranya daga idonta, ta rasa meke mata dadi, meyasa Baba zai tafi a lokacin da suka fi bukatar shi? Meyasa shima zaibi Mama a lokacin da kowa ya dogara a kanshi?. Tana cikin wannan halin ne Ahmad yaxo ya iske ta a haka, da gudu ya karasa yana mai tambayarta ko lafia. “Firdausi,

lafiyarki kuwa?” Ya tambaye a kidime, domin duk abunda zaisa fiddausi kuka to ba karamin abu bane. A hankali ta dago raunannu idanunta ta saukesu a fuskar mijinta, wanda a yanxu shine gatanta, dashi kadai ta dogara bayan Allah, bata da wani gata daya rage shi. “Baba ya rasu.” Ta fada tana me kara fashewa da wani kukan. “Innalillahi” kawai yake furtawa, domin ya kasa magana. Kanshi ya daure. Kullu Nafsin za’ikatul Maut! Saidai muce Allah ubangiji ya jikan Alhaji Salisu Zubairu. Badiyya ta fito a guje, tana fadin “Momy wane kaya zan….” Maganar ta tsaya mata a makoshi, domin ganin halin da iyayenta suke ciki. Da kyar ta taka taje inda suke. “Momy, Dady meya faru?” Ta fada a hankali, domin ta rasa
meke mata dadi. A matsayinta na yarinya yar shekara goma, wadda take primary 5; ganin iyayenta haka yasa komai na duniyar ya tsaya mata chak!. STORY CONTINUES BELOW  “Babu komai Badiyya, jeki hado kayanku kamar kala biyar keda Momynki, kizo mu tafi.” Ahmad ya ansa mata a hankali. “Dady ina kuma zamuje?” Ta tambaya a rude, domin ba kasafai suke tafiya har ta kwana wani waje ba. “Kankia zamuje, kiyi sauri Badiyya.” Ya bata ansa. A hankali ta tashi taje ta dauko masu kayansu, ta fito ta mika ma Momynta hijab suka fita. *** Suna shiga garin Kankia sukaga motoci sunata shiga, alamun babban mutun ya rasu, domin yanzu za’ayi jana’izarshi. Firdausi da kyar ta fito daga cikin mota, hawaye na fitowa daga cikin idonta, wai yau itace Mahaifinta ya rasu. Bata taba tunanin hakan ba. Tana shiga cikin gida, itadai Badiyya murna take yau sunzo Kankia, xataga Baba. Tana zuwa taga kannen mamarta suna kuka. “Anty Kausar, meke faruwa? Ina Baba?” Badiyya ta tambaya a kidime, domin ba haka ta saka zuwa ta iske gidan ba. Kasa ansata kowa yayi, domin tausayinta sukeji, Baba yafi kowa shakuwa da Badiyya duk gidan. Firdausi ce ta rungume yarinyarta, tana wani gunjin kuka. A haka suka je sukayima Baba addu’a sannan aka fita dashi domin kaishi gidanshi na gaskiya. Badiyya itadai bata gane komai ba, abun daya tsaya mata a rai shine; taga Baba kwance cikin fararen kaya, sannan yanzu wasu maza sunzo sun fita dashi. Wata mata taji tana cewa “yanzu shikenan Alhaji, har abada!” Sai a lokacin abun ya daki zuciyarta, badai Baba ya rasu ba? Aikau a take ta fashe da wani matsanancin kuka ta fadi sumammiya. Mutane sukayo kanta, Firdausi abun duniya ya isheta, ta rasa dame xata ji. Aka Daukesu aka kaita asibiti, nan likitoci suka fada masu ta shiga coma, farfadowarta ba yanzu ba.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 6

RAYUWAR BADIYYAH CHAPTER 2