in

RAINA KAMA CHAPTER 6 KARSHE

RAINA KAMA CHAPTER 6 KARSHE

Bansan yanda zan musalta muku farin cikin damuka tsinci kanmuba nida ‘yar uwata Munubiya, abin kawai ba’a magana.
Duk da bata yarda zan zo d’inba amma bata fasa tanadar min duk abinda tasan inasoba, tarasa inda zata sakani dan dad’i, gaskiya gidan munu yayi k’yau sosai, gashi an cika ko ina da kaya, kasancewar harda nawa aka had’a mata, muna yin salla muka 6arke da hirar yaushe gamo, a haka yaa marwan yazo ya samemu, yaukam abin mamaki naga fara’a a fuskarsa, nace lallai aure yayi citta kenan, yanda yake bama Munubiya kulawa sai abin ya birgeni, kamar Na lashesu kuwa Dan dad’i. Haka muka yini muna tad’i har lokacin sallar la’asar yafita salla.
A lokacinne aunty Salamah tazo gidan, Ashe Munubiya ce takirata ta fad’a mata zamu tafi India yau da daddare, mun tarbeta da murna sosai, yayinda ita kuma taketa yaba wai munyi k’yau. mukaita rufe fuska alamar kunya.
Shawarwari taita bamu akan rayuwar aure da yanda zamu tattali mazanmu, babu ko kunya take 6aro mana komai, sai mune muketa sunkuy da kai, itakam ko a jikinta, ta rarraba mana wasu buks da ke d’auke da abubuwa masu amfani dazasu bada gudunmawa a zaman takewar aure, nidai bawai na d’auki nawa da muhimmanci baneba.
Wajen 5 tatafi, tafiyarta babu dad’ewa saiga Galadima da yaa marwan sun shigo, Ashe wai ya dad’e a k’ofar gida zaune, ya kira yaa marwan yace baya gida amma gashinan zuwa.
Shine yajirashi amota harya iso suka shigo tare. Sun gaisa da Munubiya a mutunce, ta shirya musu abinci, da yace yagode sauri yakeyi, amma munu ta marairaice wai yaza’ayi mijin ‘Yar uwarta yak’i cin abincin gidanta, in baimasa baneba ta sake masa.
Murmushi yayi ya zauna yaci kad’an, yayinda mukuma muka shiga d’aki dan mu basu waje suci abincin, d’an kuskus d’inmu mukayi muma, takuma kwantar min da hankali akan auren nawa da wasu ‘yan shawarwari, da nunamin fushinta akan abinda nace nama Galadima d’in, ta nunamin wannan ba tarbiyyar da iyayenmu suka bamu baneba, gaskiya karna sake irin haka, kuma nabashi hak’uri akan hakan, nace “to amma tayaya zan basa hakurin?”.
‘Yar takarda ta d’auka tayi rubutun tabani wai nabashi.
Na kar6ane kawai badan ina tunanin zan bayar d’inba, duk da nasiharta ta shigine gaskiya, kuma nima tun a ranar nayi nadamar ce masa azzalumin gaskiya, Duk da nasan a cikin fushine Nima Na fad’a, Dan nashiga rud’ani sosai akan abinda yayimin daban zataba.
tabani kayan da aunty salamah takawo a Leda, batareda na dubaba na amsa.
Itama k’yauta mai tsoka yamata sannan muka fito, nida ita kowa yana sharar kwalla, bamason rabuwa da juna, amma yazamuyi? aure ya rabamu.
Daga nan gz yaa marwan muka nufa gaida mama rabi’a, namayi mamakin yanda yasanta, nankam tare muka shiga, su Ayusher suka rukunkumeni cikin tsantsar farinciki da kewa.
Bamu dad’e sosaiba itama ya ajiye mata alkairi muka fito, su Feena ma yabasu kud’i wai su sai kayan kwalliya, hakama Ahmad, yaa Fadeel dai mun tarar baya nan, yakoma inda yake bautar k’asa.
Nanma saida nayi kuka dazamu taho.
Saida muka shiga mota ina sharar hawaye sannan ya kalleni cikeda k’asaita yana ta6e baki, “ke wai bak’ya tsoron hawayenki su k’are ne?”.
Bance masa komaiba nacigaba da kukana, shima saiya shareni.

★★★***★★★

Koda muka isa Masarauta bamu wuce sashenmu kai tsaye ba, wasu 6angarorin gidan mukaje mukai musu sallama, harda sashen mama Fulani, yauma dai babu magana mai dad’i tsakaninta da Galadima, nifa lamarin nasu na d’aure kaina gaskiya.
Mai martaba kam munsha addu’a a wajensa, sannan muka fito.
Mun shiga sashenmu ana kiran sallar magriba, zan shige yace “kiyi azamar shirya kayanki trolley d’aya, karki wani kwashi kaya dayawa”.
Da to kawai na amsa nayi shigewata ciki.

*_7:30pm_* Muka bar masarautar, nida shi da Samha motarmu d’aya, muna baya tana gaba.
d’ayar motar kuma Sauban da aunty Mimi da khaleel ne aciki.
Mun sami rakkiyar Harun da Muftahu sai wasu k’alilan daga masarautar.
Tom nidai ba k’auyace a airport, dan banta6a shiga jirgiba, amma kunsan mutuniyar taku da Jan aji,? saina Fiske abina nima inajan citta tamkar wadda ta saba.
Duk abinda yadace ayi anyi mana, musamman ma ni danake sabuwar fita k’asar, harun yad’an sha cukuniya a kaina tunda rana.
9pm dai-dai jirginmu ya shilla a gajimare???.

Lokacin da akace asaka belt ban sakaba, sai shine ya jawo yasakamin batareda yace uffanba, yana jikin window nikuma ina gefensa, sai bayan mu khaleel da Samha, can baya kuma aunty Mimi da Sauban.
Ina lafe jikin kujera, yayinda shima yake kwance ya jingina bayansa, wani English novel ne a hannunsa yana karantawa, dama tun amota yake rik’e da kayansa.
Da akazo tambayarmu mi muke buk’ata Coffee kawai yace yacigaba da karatunsa, nima ta tambayeni saina girgiza mata kai alamar bana buk’atar komai.
Janye book d’in yayi yana kallona, saikuma ya janye ya maida kanta, harta bar wajen ya kirata, yace takawo min abinda su Samha sukace sunaso.
Bance komaiba nidai, shima saiya cigaba da karatunsa.

(*************)

Alhmdllh mun sauka kasar India, k’asar da nake gani a films, abin mamaki sainaga dogarawa ne sukazo tarbarmu, saikuma Akash dawani danaji Galadima yakira da beejay.
Bamu 6ata lokaciba mukabar airport d’in, a nawa tunanin sainaga rayuwar tasu kamar dai tamuce gaskiya, saidai banbancin sutura zuwa wasu mu’amullat haka, mutane sunata hidimarsu da kai kawo hankali kwance.
Masha ALLAH na fad’a yayinda muka isa gidan danake k’yautata zaton nasu Galadima ne. gidan kam yamin k’yau gaskiya, su beejay basu shigaba suna saukemu suka juya, mune muka Shiga hannuna aunty Mimi tarik’e, yayinda su Samha suke agaba.
Galadima kam mun barsa a harabar gidan yana waya.
Ai kaina bai gama kwancewa ba saida muka shiga falon gidan, hummm manyan k’asarmu sunajin dad’insu gaskiya, yo kanada irin wannan gidan a k’asar daba takaba to k’asarka kumafa?.
A falo muka zube bayi suka Shiga hidima damu, muna zaune a wajen Galadima yashigo, shima zaman yayi ya aza k’afa d’aya bisa d’aya, Sauban yazuba ruwa a cup yabashi, kar6a yay yana fad’in “thanks”.
Ya kalli baiwar datake shirya abinci daga can gefenmu, “k zonan”.
Da sairi ta ajiye spoons d’in hannunta tanufo inda muke, agabansa ta zube tace “gani ranka ya dad’e”.
“kisamu wata ta tayaki Ku gyara d’akin can nakusada Samha yanzun nan”.
“angama ranka ya dad’e”. tayi maganar cikeda tdantsar ladabi.
Aunty Mimi Na najinsa batace uffanba. Shigowar momma tasaka khaleel tashi da gudu yaje ya tarbota, itama Samha zuwata ta kwakwameta, tunkan ma afad’amin nagane mahaifiyarsu Galadima ce, koda yanda fuskar kowannensu ta washe da farincikin ganin juna.
Hankalinta Na kaina tana murmushi da fad’in “oyoyo d’iyata”.
Zamowa nayi daga kujerar na durk’usa har k’asa ina gaisheta, ta k’araso inda nake ta kama hannuna ta tadani nakoma saman kujerar, “zauna kinji, sannunku da zuwa, kinsha hanya ko?”.
Murmushi nayi ina duk’ar da kaina.
Galadima yace “wai Momma dan ALLAH duk baki ganmu baneba?”.
Kallonsa tayi cikin Hararar wasa, tace, “yo naganku bata taku nakeba”.
Su aunty Mimi dariya suka Sanya, yayinda Galadima yad’an 6ata rai yana fad’in “da tsohuwar Zuma dai ake Magani Momma”.
“a fad’arka ba, amma sabuwa ma aitafi aiki da dad’i”.
Nidai murmushi nakeyi, Dan wasan nasu ya burgeni, inason ganin family haka cikin farinciki, gaskiya sai sunfi jin dad’in zaman nan fiyema da masarautar sun can.
Gaishe-gaishe aka shigayi, kowa yana k’ok’arin bama Momma labarin yanda biki ya kasance, sai dad’i takeji da sanya albarka, nidai nida Galadima babu mai cewa komai.
Mik’ewa Galadima yayi, “bara nad’an watsa ruwa Momma”.
“to afito lafiya Muh’d”. ta kalleni nima, “d’iyata tashi kibi mijinki kiyi wanka kuzo ga abinci”.
Harya fara tafiya saiya tsaya, juyiwa yayi yana mata magana a yaren daban saniba.
Ta galla masa harara da masa dak’uwa, itama bansan mitace masaba. naga dai ya tura baki yaci gaba da tafiyarsa. ita kuma tace natashi naje.
(Wai ashe cayay mata ai yasa a gyaramin d’akin da zan zauna, shine tamasa dak’uwa tana cewa d’akin safa?, shi idan ance Araba mana d’aki saiya amince?, to tare zamu zauna, shine yakuma cewa ammafa d’akinsa ai ba kowa ke shigaba, tace tasani aii, muje nima sirrinsace ai, shinefa ya tura baki gaba).

Kamar an maken k’afafu haka nabisa abaya muna taka steps d’in benen, har muka isa k’aramin falo mai k’yau, komai farine a wajen, TV ce kawai takasance bak’a.
Falon yad’anyi k’ura alamun ba’a gyaraba (babu mai aikin dake hawa samansa, gashi kuma sunyi tafiya suduka, Momma kuma batada time d’in gyara masa d’aki).
Guntun tsaki yaja yana yamutsa fuska, d’an zaman danayi dashi na fuskanci bayason k’azanta komin k’ank’antar datti yata yamutse fuka kenan, bamu tsaya ananba muka shiga bedroom d’in bayan yabud’e, mayataccen k’amshinsa yana manne da d’akin, sai dai nan d’inma yayi k’ura, waya yazaro yayi kira, ashe Samha yakira, yace “k zoki gyaramin d’aki”.
Bai jira cewarta ba ya yanke wayar.
Bance masa uffanba nima nataka nawucesa, bina yayi da kallo dan yaga ina zanje?.
Zanin gadon na yaye duka, nacire rigar filaluwan tareda rumfar da akama gadon, shidai kallona kawai yakeyi, yana tsaye jingine da bango (baiyi tunanin zance zan gyaraba).
Knocking d’in da akayine yabada izinin shigowa, Samha ce d’auke da kayan tsintsiya, ta zubesu a k’asa tana fad’in “aunty kibarsa zan gyara”.
Kaina na girgiza nace “barshi Samha, nunamin kawai yanda zanyi, kije kema ki huta”.
Nunamin komai tayi, har inda bedsheets suke, tafice a d’arare da zaton Galadima zai hanata yace takoma ta gyara.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAINA KAMA CHAPTER 5

DAN MACE CHAPTER 1