in

RAINA KAMA CHAPTER 5

RAINA KAMA CHAPTER 5

.Da kuka na farka, duk da naji dad’in jikinna kuwa, dan banajin azabar kamar jiya, tashi nayi zuwa toilet danna d’auro alwala, na tuna labarin da wata k’awarmu ta ta6a bamu akan yanda taita ciwon jiki, saida mijinta yata mata ruwan zafi a ranar, ruwan mai d’an zafi na had’a na shiga ciki, nasha zafi kuma naji dad’i, amma inajina kamar ba a dai-daiba maganar gaskiya, haka dai nasamu nayi sallar asubahi, ina tsaka da sallar yashigo da nufin tadani, ganin na tashi ma saiya juya yafice abinsa zuwa masallaci shima.
Koda na idar kwanciya nayi saman abin sallar nacigaba da kuka na, ina kuma tunano abinda yafaru a jiya tamkar a films ko novels ko mafarki, babu abinda zuciyata keyi sai tsinemar, a yau d’inan dolene saiya bani Sakina natafi gidanmu, nafasa auren Contract d’in ma, da dai na zauna da mugunnan gwamma nakoma gidanmu nacigaba da rayuwa dasu innaro yafimin….

Tun d’azun yana tsaye a kaina, tausayina yakamashi, dan yasan shine silar kukan mawa, bayason zalunci ko kad’an, amma saigashi shine da aikatawa kuma, zama yayi a bakin gadon, cikin muryar nan tasa mai kama da anmasa tilas yace “tashi zaune muyi magana”.
“baza na masa, a zuciyata nace bazan tashiba mugu kawai, bakada abinda zaka fad’amin na yarda, azzalumi, dama abinda ka shiryawa rayuwata kenan? Dan kaganni d’iyar talakawa banida k’arfin gogayya da kai, tabbas nayi kuskuren yadda da Wanda shikansa ma bai gama yadda da kansaba, ALLAH ya Isa wlhy tunda ka ketamin mutunci har abada bazan yafe makaba, kullum cikin sallata saina sakoka da neman sakkaya ga mahaliccina akan zalincin dakami………
A fili kuma nace, “kagama zalintata kazo kanamin mazurai da mulki, ank’i tashin”. a hankali nake maganar banyi tunanin yana jinaba, sai tsawa kawai naji ya dakamin
“k!!!!!”.
Yafad’a cikin daka tsawa, Ashe tunda nafara maganar ya rumtse idanu saboda yanda Kalmar zaluncin suke sukarsa a zicciya, ban ta6a ganinsa a wannan yanayinba, a cikin fad’a yace, “Niba azzalumi baneba, zina nayi dakene!? dazaki dunga aibantani damun duk furucin dayazo bakinki? to bara na tuna miki idan kin manta, SADAKI na biya na auroki! tun jiya kike fad’an magana amma na shareki, ni sa’an kine? wlhy idan bakiyi wasaba zan koya miki hankali! danaso muyi magana ki saurareni mana kiji mizance?………”
Zumbur namik’e zaune, duk da azabar da k’asana kemin, na kallesa ido cikin ido ina zubda kwalla nace, “bakada abin fad’a shiyyasa bazan saurarekaba, bar ganina ‘Yar talaka bana d’aukar raini wlhy, mina maka ne? miye had’ina da kai kaketa bibiyar rayuwata da bala’i, tunda na had’u da kai ban kuma samun nishad’iba, wlhy bazan yafe makab…….
Jikake bamm! ya make bakina da bayan hannunsa, cikin zazzaromin ido yace bazaki nutsuba Ashe?”.
Naji zafi sosai, dan haka nafashe dawani marayan kuka mai ban tausayi, ga wani bala’in tsoronsa daya kuma shigata, maganar ma a tsorace dama nayita, Dan tsabar bala’i na hango cikin idonsa Dana kallesa.
Kansa ya dafe da hannu, jiyake tamkar ya tariyo jiya a rayuwarsa ya goge dukkanin abinda yafaru
Ganin bazan sauraresan ba da gaske saiya tashi ya fice yabarmin d’akin.
Nakuma 6arkewa da kuka.

Koda yafita a falona ya zauna, ya dafe kansa daya koma masa ciwo k’asa-k’asa yau, tunaninsa yafara komawa baya daga jiya zuwa yau, shin miya sakashi wannan matsananciyar sha’awar ne wai? dan bai ta6a jin makamancin feelings irin na jiya ba, da sauri yamik’e yanufi sashensa, a falo ya tsaya, ya d’auki kwalin hollandia fresh milk d’in jiya yana dubawa, shi dai yasan shine last abu daya sha a jiya, to kenan koma miye daga cikinsa yake?. to amma ai ba yaune yafara shan fresh milk ba a gidannan balle yace kuma shine. kwalin ya ajiye yakuma dafe kansa, gaba d’aya tunaninsa ya kulle, dama shi indai yana cikin 6acinrai to komai nasa birkicewa yakeyi, dolene saiya kwantar da hankalinsa zai iya kamo bakin zaren. a kujerar Yakoma ya kwanta, ko azkar yakasayi yau, babu dad’ewa barci yakuma kwasheshi anan.

Itama Munaya daga kuka barci yay awon gaba da ita a wajen.
Har Samha suka kawo abinci duk barci suka Tatar sunayi, tasan halin Uncle Sam shiyasa bata tadasu ba, kad’an daga aikinsa ya mammaketa a safiyarnan.
Su duka sai wajajen 12 suka farka, kowanne yatashi da damuwarsa.
Tunda nayi takun farko nakuma tabbatar da akwai matsala, dan ruwan zafin da yaymin jiya kad’ai ya isa na daina jin zafinnan irin haka, balle kuma nima nayima kaina da safennan, amma maimakon k’asana yabar zafin saima zugi yake k’arawa, gashi idan nashiga ruwan, zafi nakeji sosai.
Yanda nake takawar ina hawayene yabashi mamaki, dan aganinsa yakamata nasamu sukuni saboda yanda yamin jiya. bansan yashigoba, maganarsa kawai naji..
“Wai mike faruwane? Ko dai kinji ciwone?”.
Wata uwar harara dataso bashi dariya na zuba masa, amma saiya danne baiyiba, takowa yayi har inda nake yakama hannuna na fisge, ya d’aure fuska shima yana hararata, “k! Wlhy kinutsu kafin na canja miki kamanni”.
“yo kammani na yaushe kuma zaka canja min? bayan Wanda ka canja min yanzu? dama haka kake? a fuska kamar babu ruwanka amma sai zalunci taf zuciyarka”.
Idonsa ya runtse dan bayason Kalmar zaluncin nan danake jifansa dashi, jinai kawai an fusgoni an zaunar a bakin gadon, nakuwa fashe da kuka ina fad’in “wayyo zafi, munubiya Azalumin nan zai kashe miki ni”.
Ko kallona baiyiba yafice, ina nan ina kuka saigashi yadawo da wayarsa a hannu, ya zauna saman sofa batareda ya kalleninba, bashida mafita saita kiran Akash, dan yanason sanin minene matsalar datake sakani wannan kukan da complain d’in zafin, yasan koya tambayeni ba fad’a masa zanyiba..
Da turanci suka gaisa, amma da zaiyi tambayar saiya canja harshe zuwa yaren daban saniba.
Akash yace saidai idan ciwo taji, dan bai kamata ace tana Complain zafi irin haka ba, zataji ciwo kam amma bawai yanda yake nuna masa yanzun ba.
Galadima ya gyara zamansa sosai yace “to ai na sanar maka fyad’e akama yarinyar fa”.
Akash yace “zata iya kai shekara nawa yarinyar?”.
‘Dago ido yayi ya kalleni kafin ya janye yana fad’in “Maybe 19years ko 20 kawai”.
“ai bama yarinya baceba can sosai, inaga taji ciwone gaskiya, yakamata doctor ya dubata gudun samun matsala, amma kabada gudunmawa a hukunta Wanda yay abunnan my man, please ka kwatarma yarinyar hak’k’inta wajen azzalumin nan”.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAINA KAMA CHAPTER 4

RAINA KAMA CHAPTER 6 KARSHE