in

RAINA KAMA CHAPTER 4

RAINA KAMA CHAPTER 4

Kallone ya koma sama yayinda kuyangin suka shigo cikin gidanmu, na d’akima tuni sun fara rige-rigen fitowa, baba k’arami da fitowarsa kenan daga sashensa yak’araso ga kuyangin, domin tambayarsu daga ina haka?.
Baiwa d’ayace tabashi amsa da fad’in basu kad’ai bane, masuyin bayanin suna waje.
Fita yayi sukuma suka ajiye kayan gefe suka kuma fitowa domin kwaso sauran.
Muna falo a zaune inna lami ta tsaremu sai mun sha romon wani nama da aka dafa k’anana, sai yatsine fuska mukeyi saboda rashin dad’in naman. shigowar Ahmad da Aryaan da gudu yasa mama Rabi’a tambayarsu lafiya?.
Ahmad yace 鈥渕ama wlhy bak’ine da akwatina da yawa suka shigo鈥?.
Gaba d’aya muka zuba masa idanu, kafin wani yay masa tambaya a cikinmu mukajiyo sallamar baba k’arami.
Innarmu ce tamik’e domin fitowa, ganinsa da manyan mutane cikin alk’yabbu yasata fad’in 鈥渂aba k’arami bak’i mukayi?鈥?.
Cikin washe baki yace, 鈥渨lhy kuwa maman biyu 鈥?.
Itama murmushine shinfid’e a face nata, tabasu hanya suka shigo falon, duk suka zazzauna.
Muduka muka durk’usa muka gaisasu, yayinda suka kuma gaisa dasu innarmu cikin mutunci.
Fita baba k’arami yayi yasa yaa Anas ya kunna Gen….. dayake babu nepa. Shikuma yakuma fita da hanzari domin nemawa wad’annan bak’i masu bazata kayan tarba, bayan yakira Dady da Abba ya Sanar musu.
Kaf matan gidanmu suka shigo, kowa yanason jin daga ina kuma.
Mukam d’akinmu muka koma muda su Ayusher muna hasashen bak’i daga ina haka? da gani dai kasan jinin sarautane, ko kad’an ban kawo Galadima a rainaba ma, dan narigada Na shafe labarinsa ni.

Suna cikin gaggaisawa da matan gidanmu saiga innaro tashigo, kai kace an wurgotane. baki tarik’e tana fad’in 鈥渙 ni Marwanatu, manyan bak’i irin wad’annan surasa gurin sauka sai 6angaren Ai’sha? kuko bayin ALLAH daga ina haka? 鈥?.
Su aunty Mimi basu fahimci zancen taba, dan haka duk sai sukayi d’an murmushi, matan gidanmu kuwa kowacce tayi k’asa da kai dariyar mugunta Na cinta, Innarmu dai bata tankaba, hakama mama Rabi’a, sai inna lami ce tace, 鈥測o inna in banda abinki waka hana rana fita idan lokacin fitar tata yayi?鈥?.
Kallonta innaro tayi zatayi magana baba k’arami yashigo da sallama, su Yaa Anas na biye dashi da kayan ciye-ciye nik’i-nik’i, bayan sun ajiye suka gaishesu cikeda girmamawa suka fita.
Zama baba k’arami yayi suka sake gaisawa, sannan yace, 鈥渒ufayi hak’uri, mukam duk kun sakamu a duhu wlhy鈥?.
K’asaitaccen murmushi aunty Mimi tayi, domin dama papi yamata bayani akan komai na 6oye musu dasukayi. ta gyara zamanta sosai 鈥淎lhaji daga masarauta muke, munkuma zo kawo kayan k’anwatane Gimbiya munaya鈥?.

Kusan kowa dake falon saida ya waro idanu waje, domin jin furicin aunty Mimi, wasuma zuciyar tasu kad’an tarage tayo tsalle waje.
Aunty Mimi bata damu da yanayin nasuba tacigaba da fad’in 鈥渒uyi hak’uri fa, nasan nakuma sanyaku a wani duhun, mai martaba sarki Abdul’fatah da maimartaba sarki Jalaludden Abubakar, sune sukazo Neman auren yarinyar Ku Munaya wa d’ansu Galadima Muhammad Sameer Saifuddeen Abubakar, sun 6oye muku kansune saboda wani dalili, amma sun aikomu da sak’on ban hak’uri a gareku, yanzu dai mun kawo kayan lefen Munaya ne gasunan鈥?.
Jin jina kai kawai baba k’arami ke iyayi, bakinsa yakasa rufuwa saboda d’unbin farinciki da al’ajabin dake dank’are a zuciyarsa, yanzu nan daman manyan sarakunane agabansu a wancan karon sukazo Neman auren d’iyansu, lallai sun godema ALLAH dabasu aikata wani Abu Mara k’yauba agaresu, lallai ya yarda kwarjinin mulkine yasakasu mik’a Auren d’iyarsu ga mutanen dabasu saniba.
Ai su madam innaro sai aka zauna k’asa babu nauyi, muryarta har zuga take tace 鈥渞anki ya dad’e wai gaskene saboda ALLAH?, kokuwa wasa kikeyi?鈥?.
Murmushi aunty Mimi tayi, sannan ta kalli su Ummu hasheem da suma suketa murmushi, kallonta ta maido akan innaro, 鈥渉ajiya kaka mizaisa muzo muyi muku wasa irin wannan akan magana mai muhimmanci irin ta aure, tabbas maganar nan gaskiyace, munama fata gobe idan ALLAH ya kaimu iyanzu Munaya tazama d’aya daga cikin zuri’ar masarautar gagara badau鈥?.
Innarmu da mama Rabi’a juna suka rungume suka fashe da kuka, yayinda innaro tamik’e ta callara gud’ar data jawo hankalin tawagar jama’ar ‘yan biki, sai kawai tashiga taka rawa.
Dariya sosai tamaba su aunty Mimi, shi Kansa baba k’arami dariyar yayi yana girgiza Kansa da mamakin innar tasu mai kayan arzik’i Dana tsiya.
Matan gidanmu kam ba’a magana, kowacce tayi d’if takasa koda kwakwkwaran motsi, kowaccensu jitake tamkarma tafasa ihu take a nan.
Muryar gwaggon halimatu na rawa tace 鈥渨ai da gasken dai Munayar gidan sarauta zatayi aure?鈥?.
鈥渒warai kuwa鈥?. 鈥榠nnaro tafad’a tana mata wani kallo, 鈥渏ikata sai gidan sarauta, masu bak’in cikin kuma sai a mace鈥?.
Lallai maganar innaro tadaki zukatan dukkan matan gidanmu, Sanin halin innaro da baba k’arami yayi saiyace duk afita abama bak’i waje susha koda ruwane.
Jiki babu kwari sukaita Jan k’afa suna fita Su da danginsu ‘yan biki da gud’ar innaro tajawosu shigowa. bak’in cikin kuwa k’arara a fuskokin wasunsu, maman su yaa hameed tayi taga-taga zata fad’i saida aka taryota.
Gwaggo Safiyya tace 鈥渓allai jama’ar gidannan yau ake *RAINA KAMA KAGA GAYYAFA* duk Wanda kake Kallon bai kaiba to tabbas watan watarana shine zai kereka, babu ruwan arzik’i da mugun gashi, Wanda yace shine to tabbas bashi baneba鈥?.

Su Ayusher suka shigo suna gumtsa mana, kallonsu kawai nakeyi amma badan na gaskataba, munubiya ta rungumeni ta fashe da kukan dad’i, kallonta kawai nakeyi nakasa koda motsi, to murnar Auren shekara d’aya zanyi? Kokuwa murnar Ashe galadimane mijin nawa? bawani can da ban ba kamar yanda muketa hasashe?.
Ban iya ta6uka komaiba wata k’yak’yk’yawar budurwa tashigo, daka ganta kaga wadda Hutu yagama ratsawa, babu shakka zamu iya zama sa’anin juna da ita, fuskarta d’auke da murmushi tace, 鈥渢o ina amaryar Uncle Sam d’in?鈥?.
Feena ta nuna ni da hannu itama tana murmushi.
Gadon ta hayo batareda jiran abata iziniba, ta mik’amin Chocolates guda biyu tana kuma fad’ad’a murmushin nata.
Cikin mamaki muryata a sanyaye na girgiza mata kai nace 鈥測ar uwa namiye?鈥?.
Hannuna takamo tasakamin tana ‘yar dariya, 鈥渋nji Uncle Sam yace nabama matarsa, sunana Samha, d’iyar yayar Uncle Sam 鈥?.
Duk da mamakin daya cika zuciyata, hakan bai hani mata murmushiba, nace 鈥渘agode Samha鈥?.
Tad’an langa6e kai alamar itad’in shagwa66iyace tace , 鈥渮an dai fad’ama Uncle Sam kin gode, lallai Uncle ya iya za6en k’yak’yk’yawar sarauniyar gagara badau mai jiran gado insha ALLAHU鈥?.
dariya su Bilkisu sukayi, nidai nakasa cewa komai, sai d’an murmushi danayi.
Ta dafa munubiya takuma fad’in inason twins sisters arayuwata, dan ALLAH nima kuna sona?鈥?.
Yanzun kam kasa daurewa nayi, nima saida na dara kamar yanda su munubiya ke dariyar, nakula ko kad’an Samha batada girman kai irinna ‘ya’yan sarauta, sannan tanada surutu gaskiya鈥?.
Cikin shagwa6a ta langa6e kai gefe, 鈥淎LLAH da gaske nake kubarmin dariya, ina addu’ar ALLAH yasa nanda wata 9 aunty ki Haifa mana twins muma鈥?.
Amin su Ayusher suka amsa atare.
Matsowa tayi kusa dani tafara mana hotuna, nidai nakasa ma magana, lallai Samha akwai rawar kai, ta tubure da shagwa6a wai sainayi murmushi kamar yanda munubiya tayi, tanason taje tabama Galadima tagani kozai iya banbancemu. Babu yanda na iya dole na murmusa akayi, sannan mukayi gaba d’aya.
Bata bar d’akinba saida mama Rabi’a tashigo kiranta zasu tafi, aikam kamar tayi kuka, dan bataso tafiyarba, sai dai tace anjima zasuzo wajen brothers and sister’s event.
Har k’ofar gida su Ayusher suka mata rakkiya, dan lokacin su aunty Mimi harsun fita, sunso ganina amma sukayi shiru kar aga kamar dawata manufa sukayi hakan, sun hak’ura tunda dai insha ALLAH gobe ina cikinsu.
Basuci komaiba dai a kayan da’aka jibge musu sai ruwa, dan haka baba k’arami yasaka aka bisu dashi mota, yace inhar ba wai bazasu iya cin cimar tamu bane to dan ALLAH suje dashi koda bazasuci ba su bada.
Godiya sukayi, suna mai yaba halaccin wannan gida mai cikeda karamci, dukda dai sunkula akwai lauje cikin nad’i gameda wannan family d’in, musamman yanda wasu suka kasa 6oye hassadarsu, aunty Mimi ta murmusa a zuciyarta tana fad’in Ashe ba masarautar mu kawai baceba keda irin wannan kitimurmurar ta family.
Mukulin farar motar da aka zubo akwatinan suka dank’ama baba k’arami sukace ta amaryace.
ai yanzu kam rasa abin fad’a baba k’arami yayi, yak’agara ‘yan uwansa su dawo suga wad’annan tarin baiwa da hikimar ubangiji da yayma d’iyarsu, wadda akulum ake ganin mahaifiyar yaran a k’ask’ance acikin gidan, sai gashi tazama *RAINA KAMA…..*

Bak’i na tafiya gwaggo Safiyya tasaka aka baje manyan tabarmi a tsakar gida, aka fiddo akwatinan domin kowa yagani, makwafta duk sun shigo suma kam dan kar ayi babusu.
Gaba d’aya gidan yacike da shewa da hayaniya, tun anama irga kayan har aka bari, saibi da idanu, ‘yan bak’in ciki kam sun kume waje guda, sai kukan zuci, wasuma kasa daurewa sukayi suka bar wajen.
Kasancewar su Ayusher duk suna can nashige toilet d’inmu nashiga raira kuka, nifa bammasan yanda zan fasalta muku yanda nakejiba wlhy.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAINA KAMA CHAPTER 3

RAINA KAMA CHAPTER 5