in

RAINA KAMA CHAPTER 3

RAINA KAMA CHAPTER 3

.Mun d’anji sanyi a ranmu, ganin kiran bamu kad’ai baneba, hardasu Safara’u Ashe, waje muka samu muka zauna, sannan muka gaidasu.
Fiddausi kad’ai ake jira, itama babu jimawa sai gata ta shigo da sallama, duk muka amsa, ta gaida su Abba.
Falon yay tsit Na mintuna biyu, sannan Abbanmu yay gyaran murya, kallonmu yake mu duka cikin nazari, ganin muduka mun hallara yace 鈥渕un kiraku nan ne saboda dalilin abinda yafaru kwanan nan, hankalina yakasa kwanciya da zamanku a gabanmu, mun yanke shawara nida ‘yan uwana zamu aurar daku duka kawai, kowace saita cigaba da karatunta a d’akinta, muma hakan zai sama mana kwanciyar hankali. dan haka kowacce saita sami mai zuwa wajenta ta sanar masa munason ganin magabatansa inhar da gaske yakeyi鈥?.
gaba d’aya muka amsa da to abba kanmu ak’asa.
Wasunmu murna suke da hakan, amma banda ni da Munubiya, dan bamuda wasu tsayayyu a hannu, bawai samarinne bamu dasuba, a’a wad’anda zamu kawo amatsayin Na aurene matsalarmu.
Maganar Dady ce ta katsemin tunani, danaji yana fad’in su sutashi suje, amma ni Na tsaya.
Haka suka fice suka barni, duk tsoro yakuma cika zuciyata. bayan fitarsu baba k’arami yanuna min gabansu alamar Na matso.
Tamkar kazar da kwai ya fashema a ciki haka natashi Na isa gabansu, na zauna kaina ak’asa.
Baba k’arami yace 鈥淢unaya!鈥?.
Muryata Na rawa Na amsa da 鈥渘a’am baba鈥?.
Ya gyara zamansa sosai, 鈥淢unaya na sanki bak’ya k’arya, kifad’a min tsakaninki da ALLAH miye had’inki da Galadima?鈥?.
Gabanane yafad’i daaam!, nai k’ok’arin had’iye kukan daya taho mini 鈥渨lhy Baba banida had’in komai dashi, hasalima ban ta6a saninsaba sai awajen hawan sallah, shima ba ganin fuskarsa na ta6a yiba, sai kuma randa mukai karo dashi a filin idi ina neman su kamal, kuma wlhy aranar hak’uri kawai nabashi, koma amsamin baiyiba yatafi, ni banma san shibane alokacin鈥?.
鈥渁mma miyasa aka buga hotonku kuna cikin plaza d’insa?鈥?.
鈥淒ady kuyi hak’uri, tabbas nasan munyi laifi anan, amma Ku yafemin, dan nasan da bamuje plaza d’inba a daren da k’ila hakan bai faruba, amma wlhy abinda yafaru shine……………….., cikin nutsuwa ta zayyane musu komai, saidai batace Munubiya ce zata fad’inba, tace itace.
Koda basuga ainahin abin da idonsu ba sai zukatansu sukayi sanyi, baba k’arami yace 鈥渢o ALLAH ya k’yauta, wannan akwai wani Abu daban dabamu saniba acikin lamarin, ALLAH ya warware komai cikin sauk’i鈥?.
Duk mukace amin.
Dady yace, 鈥淢unaya! bisa hak’uri damukaita bama yaya kin sami sassauci akan sati 2 daya ce ki fidda miji, yanzu saiki nutsu ki kawo kamar sauran ‘yan uwanki, insha ALLAH bayan babbar salla zamu aurar daku gaba d’aya kawai, ALLAH yayi muku albarka kinji, kucigaba da kare mutuncinku, sannan Ku koma zuwa makaranta tunda abin ya lafa鈥?.
Kai na gyad’a sannan nayi godiya.

Na iske innarmu da Munubiya jigum-jigum a falo suna jiran dawowata, nasami waje na zauna jikina a sanyaye.
Innarmu tace, 鈥渕iya faru kuma?鈥?.
Guntun murmushi nayi INA share kwallar data zubomin, 鈥渂abu komai innarmu, sun tanbayeni gaskiyar abinda yafaru ne, sannan since sun janye maganar sati biyu nafiddo miji da sukace nayi. nima za’a had’a danawa zuwa bayan salla kamar su Munubiya, kuma since mukoma makaranta鈥?..
Daga Munubiya har innarmu ajiyar zuciya suka sauke, 鈥渢o Alhmdllhi, ALLAH yabaku mazaje na gari鈥?. 鈥榗ewar innarmu鈥?.
A zukatanmu muka amsa mata da amin.

Washe gari.

Mukayi shirin zuwa makaranta, gudun abinda zaije yadawo sai muka saka nik’af dagani har Munubiya kamar yanda innarmu tabamu shawara muyi.
Alhmdllh tunda muka fita bamuci karo da abinda ya Sosa zuciyarmu ba, saboda fuskokinmu arufe suke.
A ajima babu Wanda ya shaidamu sai Bilkeesu, nanma dai munyi mun fito lafiya babu wata damuwa. amma saboda a d’ar-d’ar Muke bamu wani sakeba, ana fitowa lectures muka nufi gida.
Haka muka cigaba da zuwa makaranta kulum fuska arufe, ko cikin anguwa za’a aikemu saimun saka nik’af, dan yanzu fuskokinmu sunrigada sun zama sannanun fuskoki….

鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄鈽呪槄

Yana gama kimtsawa yafice, ko abincin da Samha ta shirya nasa bai sauraraba, kai tsaye yanufi Hospital d’i. da Abie ke jinya.
da jakadiya yafara cin karo tana rik’e da Khaleel a hannu, khaleel yakwace yataho da gudu yana fad’in 鈥淯ncle oyoyo鈥?.
Hannayensa ya bud’e masa yafad’a jikinsa, ya shafa kan yaron yana fad’in 鈥渕y boy ykk?鈥?.
鈥渓afiya Uncle Sam… yaushe kadawo?鈥?.
Murmushi Galadima yayi, yad’an ja kumatun khaleel 鈥渢o maganatu yau na dawo鈥?.
Dariya yaron yayi, zai sake joho wata maganar Galadima ya d’ora yatsansa akan bakin yaron alamun yayi shiru. Shirun kuwa khaleel yayi dan yasan halin Uncle Sam.. saraii.
Jakadiya ta rissina tana gaidashi, amsawa yayi fuskarsa da ‘Yar fara’a, ya tambayeta ya jikin Abie.
鈥渏iki Alhmdllh ranka ya dad’e鈥?.
Kansa kawai ya jinjina mata yay gaba rik’e da hannun Khalel.
Da sallama ya shigo d’akin da Abie ke jinya, d’akine babba kamar Bana asibitiba, daka gani Kasan anyisane saboda manyan mutane irinsu, Momma na zauna akujerar gaban gadon da Abie ke kwance, gadon Kansa bawai ainahin gado bane na asibiti, duk wasu na’urori ne ajikinsa, da alama sune suke taimakama jikin Abie d’in, k’umba Momma ke yanke masa.
Aunty Mimi na zaune bisa kujerun da aka shirya a gefe tamkar falo, System Ce agabanta tana danne-danne.
Sallamar Galadima yasata d’agowa tana murmushi, 鈥淢y k’ani oyoyo鈥? tafad’a tana ture system d’in daga cinyarta.
Murmushi yamata shima, cikin maganarnan tasa ta k’asaita maikama da anmasa tilas yace 鈥渕y dear aunty barkanki鈥?.
Hannu tasa tad’an bigi damtsen hannunsa, cikin wasa tace barka zakace ba bagyka ba鈥?.
Shafa Inda tad’an bigesan yakeyi yanda 6ata fuska kamar wani k’aramin yaro, 鈥淎LLAH akwai zafi aunty Mimi, wai har yanzu ban girma da buguba awajenki?鈥?.

鈥渢ab ai da sauranka, sai randa kayi aure zan daina鈥?.
Bakinsa ya ta6e yak’arasa inda Momma take yana fad’in, 鈥渁iko k’yadad’e baki barinba kenan鈥?.
Momma dake murmushi saboda drama d’in tasu ta kalli Abie da shima fuskarsa take a washe alamun yayi farinciki da ganin d’an nasa.
Gabansa yaje ya durk’usa, saitin Face d’insa, ya saka hannunsa cikin NASA fuskarsa d’auke da murmushi yace, 鈥渕y Abie barka da rana鈥?.
Da idanu Abie ya amsa masa, dan sune bakin maganar yanzu.
Yakuma masa magana da ido alamar yaka barosu?.
Murmushi Galadima yayi na takaici, sannan yace, 鈥渕ai martaba na gaidaka, shima zaizo nextweek鈥?.
Farin cikine Yakuma fad’ad’a a fuskar Abie, dasu sukasan yanayinsa, sukad’ai zasu iya fahimtar farin cikinsa ko damuwarsa, musamman ma Momma.
Momma dake kallonsu tayi murmushi, Galadima ya maida kallonsa gareta, 鈥淢omma na yana sameku?鈥?.
鈥淎lhmdllh Muh’d, yaka barosu?鈥?.
Baki yad’an ta6e sannan yace 鈥渓fy lau, ya jikin Abie?鈥?.
鈥渏iki Alhmdllhi, dan randa ka tafi yatsun hannun damarsa sund’an motsa鈥?.
Da Sauri Galadima yace 鈥渄a gaske Momma?鈥? yay maganarne yana kallon hannun Abie d’in, sannan cikeda farin cikin ya sumbaci hannun yana fad’in Alhmdllh ala kulli halin, ALLAH yabaka lafiya my sweet Abie鈥?.
Lumshe idanu Abie yayi farinciki na k’ara fad’ad’a a face nashi, aunty Mimi da momma da jakadiya suna kallonsu cikeda tausayi suka amsa da amin. khalel yata6a kafad’arsa, juyowa yayi yana kallonsa. yaron yakai hannu yana sharema Galadima hawayen dasuke kwance a kumatunsa. galadima yajawosa ya rungume yana sumbatar kan yaron, fuskarsa d’auke da murmushi.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAINA KAMA CHAPTER 2

RAINA KAMA CHAPTER 4