in

RAINA KAMA CHAPTER 2

RAINA KAMA CHAPTER 2

Hidimar biki ta kankama gadan-gadan, dan har bak’in nesa sun fara isowa, a ranar alhamis aka gudanar da sister’s and brother’s day Wanda mune k’annensu muka shirya musu da yayinmu maza. da farko a tsakar gidan innaro aka shirya, saboda su Abba bazasu barmu mu saka kid’aba a gidanmu, gashi mun gayyato k’awayenmu ne, sai abokan su yaa Nasser danasu Anas. daga baya kuma sai muka canja shawara saboda samun wani fili damukayi can k’asan layinmu, filin a zagaye yake da katanga an saka gate. Tunda safe suka fara shirye-shiryen gyara wajen, kasancewar sai 4pm za’a fara, mudai makaranta muka tafi nida fauziyya da Munubiya, dan munada lectures, amma sauran duk k’in zuwa sukayi, barema su Siyama amare.
Around 3pm muka dawo gida, yauma kam da alama wasu bak’in sun iso, dan gidan Yakuma cika da yara da ‘Yar hayaniya.
Mun tarrar innarmu tana d’akin abbanmu, dan haka mukayi wanka muka fara shirin tafiya wajen taron, ko abinci bamu nemaba, dagani har munubiya mun iya makeup, kasancewar mama Rabi’a tasakamu wajen koya muda Ayusher lokacin damuka gama secondary, a d’an tsakanin kafin fitowar results d’inmu, taga damuyi zaman banza gamma muje mukoya wata ‘Yar sana’ar, tunda bamusan inda rayuwa zata kaimuba. Ko gama shiryawa bamuyiba Rahma tashigo kiranmu inji su Aunty Rahaima, dan mune zamu musu kwalliya.

Mun tarar dasu duk sunyi wanka dama mu suke jira, zaman musu kwalliyar mukayi, ni nafarama Aunty Hauwa’u, yayinda Munubiya takema aunty Ramlah.
Kiran Ayusher yashigo wayar munu…., ta d’aga tana fad’in 鈥渒in isone?鈥?.
Bansan mitace mataba daga can, naji tace, 鈥渒izo muna 6angaren su Aunty Ramlah鈥?.
Babu dad’ewa saiga Ayusher itama, ta gaggada su Aunty’s d’in, sannan muma tabamu hannu muka gaggaisa cikina musabaha.
鈥渓ah dear nifa harna fidda ran zakizo ALLAH鈥?.
Ayusher tace 鈥渒ibari kawai, wancan jarabbaben ne yasakani aiki, tuwo mama tayi da rana, kinsan kuma bayaci shi, shinefa ya tsareni wai saina masa sakwara, harfa nayi shirin tahowa鈥?.
鈥渦hm ai lamarin yaa marwan saishi, matarsa dai taga banu wlhy, shi anya ma yata6a budurwa kuwa?鈥?.
Dariya duk muka sanya a d’akin, aunty Hauwa’u tace, 鈥渁i marwan akwai miskilanci wlhy shima, nifa zan iya cewa mun ta6a magana dashi kuwa?鈥?.
Ayusher tace, 鈥測o aunty ai wannan kowama haka yake masa, komu muka gaidashi sai yaso yake amsawa, kullum mama cikin masa fad’a take amma abanza wlhy?鈥?.
Nann dai hira Yakoma kan yaa Marwan da mutane masu muskilanci irinsa, Munubiya ce mai kareshi, (dama ita suna d’an d’asawa, nice dai kamar muna ganin hanjin juna dashi danma ina tsoronsa ).
Kasan cewar mu uku ne sai kwalliyar tai sauri, dan danan muka kammala, nida munubiya mukayi tamu muma, simple makeup mukayi, amma komai iri d’aya, dama haka mukeyi, komai namu kullmun iri d’ayane.
Munyi k’yau, 6angarenmu muka koma mukayi shiri cikin blue d’in skirt da pink d’in Riga kamar yanda aka tsara sai veil shima blue.
Na jujjuya ina kallon kaina a mirror, 鈥渒ai jama’a nikam bazan iya fita hakaba gaskiya鈥?.
Ayusher dake kwance tana danna wata tad’ago ta kalleni, 鈥渒ai amma kuma wlhy kayan sun miki k’yau, kinganki kuwa? dan ALLAH ki barsu, kiyi rolling veil naki kawai鈥?.

鈥渒ai ba munaya kad’aibafa, nima bazan iyaba, after dress zan d’ora wlhy鈥?.
Dariya Ayusher tayi, ta tashi zaune tana ajiye wayar, 鈥渨aiku miyasa k’auyawane sister’s, naga a ke6antaccen waje za’ayi?鈥?.
鈥渁mma kuma dai ai akwai maza kema kin sani鈥?.
鈥渢o alaranmiya, Ku saka, amma kafin Ku saka d’in nidai kuzo miyi hotuna鈥?.
Gaskiya koni nasan munyi k’yau, kasancewar mud’in fararene, kalolin duk sai suka kar6i jikinmu blue & pink. Wanda bai saniba saiya ce mu ‘yan uku ne har Ayusher, dan muna matuk’ar kama da juna, sai dai Ayusher tafimu haske da d’an jiki.
Sai da mukad’anyi hotuna sannan muka fito. Innarmu tace kunyi k’yau, amma dan ALLAH kar inji wani yayi abinda za’ace gashi-gashi, Ku kama kanku da mutuncinku kunga dai acikin anguwane, idon kowa akanku yake鈥?.
Mukace to innarmu insha ALLAH. mun fita tana binmu da addu’a.

A k’afa muka taka har wajen taron, tunkan mu k’arasa muke jiyo tashin kid’a. wajen dank’am yake da ‘yanmata da samari, k’awayen amare da namu muma, sai ‘yan uwa kuma da abokan su yaa Nasser, dama shi ya Hameed bai gayyaci kowaba, yace ya bar mana mu k’anne (shidama ba auren farko bane).
Tunda muka shigo akai mana caa da idanu, wasu tsantsar kamarmu ce tajawo hankalinsu kanmu, wasukuma burgesu mukayi, wasu kuma gulmarmu sukeyi da zaginmu, to dama shi taro ya gaji hakan, ballemu da ake ganinmu k’ask’antattu agidanmu, kamar kowama yafimu komai.
Amare suma duk sunyi k’yau cikin tasu shigar ta Riga da wando pink gaba d’aya, sai suka d’aure k’ugunsu da blue d’in belt, suka d’aura jacket blue.
Snacks ne kawai akad’anci a wajen da drinks, sai pictures da’aka d’auka da video, ‘yan mata sunata casar rawarsu da samari, mudai muna daga gefe zaune muna shan kallo. mun rarraba gifts d’in damuka tanada, bawani Abu bane masu tsada. silifas d’in wankane sai brush, MacLean, soson wanka da sabulu d’ad’d’aya aciki, gifts d’in nan mun shiryashine kawai dan tsokana dama. gabda magriba taro yatashi lfy, kowa ya kama gabansa. muma gida muka koma.

鈽呪槄鈽呪槄鈽?

Washe garima saida mukaje makaranta, sai dai 11:30 muka fito lecture, ALLAH ya taimakemu muka samu taxi da wuri.
Sanda muka dawo har ‘yan jere sun dawo, kowa dangin mamarsa sukaje jerensa, shiyyasa mukaji tsitt babu gutsiri tsoma.
Muna dawowa ko wanka bamu tsaya yiba mukaci abinci muka tafi shagon auntynmu data koyar damu makeup domin yin k’unshi da saloons.
Cikin farin ciki ta tarbemu, dan mun rabu da ita cikin mutunci bayan mun iya aiki, Aunty salamah batada damuwa, inkaga tana maka fad’a to baka fahimtar abinda take koyar dakai ne, kwazon damuka nuna alokacin yasa takeji damu over. Tana kiranmu ‘yan ukun ta.
K’unshi aka mana mai k’yau da gyaran kai, (dan d’aurema k’arya gindi irinnan aunty salamah harda mana gyaran jiki馃槉, wai tanaso muma musamo mazajen aure馃檲).
Kowa ya gammu yasan munyi k’yau sosai.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RAINA KAMA CHAPTER 1

RAINA KAMA CHAPTER 3