in

RAINA KAMA CHAPTER 1

RAINA KAMA CHAPTER 1

*Matsanan cigar* hayaniyar dake tashi agidan ce taja hankalina, cikeda bak’in ciki natashi daga barcin safen dana koma, fitinar gidanmu dabance data kowane family House dana Sani kona ta6a jin labarinsa a rayuwata, haka gidan namu yake kullum tamkar kasuwar ‘yan danbe, daga matan gidan zuwa ‘yan mata da yara tamkar muna ganin hanjin juna, saika rantse badaga tsatso d’aya muka fitoba.
Kururuwar danaji maman Safara’u ta kurma yasani kuma jan dogon tsaki, sai kuma najiyo muryar gwaggon haleema Na fad’in 鈥渒ai amma wannan lamari baiyi dad’iba, kekuwa maman biyu ya kamata ki canja wannan halin naki, dan tabbas inba wani abu kikayiba babu yanda za’ayi yaronan Sadeequ yadage shi cikinsu *MUNAYA* yakeso, duka yaushe aka gama maganar nan akan shafi’u amma shine zaki koma kan Sadeequ kuma yanzu?鈥?.
gaba nane ya fad’i, cikin zaro idanu waje nace, 鈥渁shema mu akanmu fitinar take yau?鈥?. yink’urin sakko nake daga gadon Munubiya tashigo tana share kwalla, binta nayi da kallo harta fad’a saman gadon ta kwanta rufda ciki tareda fashewa da kuka mai ban tausayi. Hakan Yakuma tabbatar min lallai mud’inne dai ake hargowar akanmu. a fusace Na dirgo daga gadon na nufi k’ofar fita, (ko kad’an banida hak’uri, musamman akan cin zarafin mahaifiyarmu da akeyi agidan lokuta da dama idan irin hakan ta taso), taku biyu nayi naji an damk’oni, najiyo cikin masifa dan nasan Munubiya ce.
鈥渨lhy ki sakeni kafin nafara huce haushina akanki munu! yau saina gyarama kowacce ‘yar iskar mata zama agidannan dan kutu…..
Bankai ga k’arasawa ba Munubiya tai saurin rufe bakina da tafin hannunta.
Kici-kicin kwacewa nafarayi amma nakasa, dan bak’aramin ruk’o taminba, raina yak’ara 6aci ainun danjin irin rashin kunyar da Safara’u ke zubama innarmu a tsakar gida, bansan na wancakalar da Munubiya gefe ba nafice da gudu.

Babu Wanda yaga fitowata sai dai saukar sautin marin dana zubama Safara’u a farar fuskarta sukaji.
Hakan yaja gidan yay tsit na wucin gadi, sai kuma hayaniya takuma 6allewa, Safara’u da mamarsu sukayo kaina danufin duka….
Tsawar da baba k’arami ya bugace tasaka kowa dakatawa tsakanin ni dasu, hakama matan gidan sai suka fara jan k’afafu danufin barin wajen.
A tsawace yace, 鈥渒ar wadda tabar wajen!!鈥?.
Tsitt kakeji gidan yayi, tamkar bashi bane d’azun ya cakud’e da hayaniya tamkar ana biki ko suna.
Jarabar gidanmu ba bak’on Abu bane a anguwarmu, danta rigada tazama tamkar ajininmu take (yo ajininmu mana zance) tunda kullumne babu fashi sai anyi hayaniya, kodai matan gidan kokuma mu ‘ya’yan gidan. Babu mai d’agama wani k’afa koda na second d’ayane kuwa, yanzun zakaji gidan shiru, anjima k’ad’an kaji an doka gangar shaid’an, musamman ma fad’an yara dayafi komai saurin had’a fad’an matan gidan da a kulum, a rana sai ayi fad’a biyar akan yara kawai, innarmu ce kawai da Maman Fauziyya keda k’ok’arin K’aucewa irin wannan fitintunun dasuka zama tamkar shan ruwa acikin gidanmu.
Baba k’arami yafara fad’a tamkar zai ari baki, inda yake shiga bata nan yake fitaba, kowa yayi tsit yana saurarensa, (saboda kasancewar masifaffe shima) sai da yayi mai isarsa sannan yajuya yafita yana fad’in nida Safara’u mu sameshi falonsa. harda iyayenmu mata.

Duk abinnan da akeyi innarmu na kicin tana had’a Karin kumallon safe, kuma kalma d’aya bata tofaba a zancen nasu, datasan ma zan fito bazata barniba nima.

A falon baba jafaru yanemi jin ba’asin tushen fitinar, cikin d’aga muryar da hargowa maman Safara’u tafara fad’in 鈥淎lhaji wlhy kashiga tsakanina da maman biyu a gidannan, idanfa tanama sauran matan gidannan Yanda taske so, suna barinta nibazan bartaba, tasanni tasan waye ubana ehe, kum…….
Hannu yay saurin d’aga mata, 鈥渒inga Suwaiba nifa ba wannan ne yasani kiranku ba, sonake naji minene ya kawo hayaniyar?鈥?.
Cikin jin haushin an tareta tace, 鈥淎lhaji akan yaronnan Sadeequ ne, kowa yasan wajen Safara’u yake zuwa a unguwarnan, amma jiya da yamma sai ya aiko kiran Munaya, dayake ALLAH yatashi tonon asirinsu sabida bayaune na farko ba sai d’an Aiken ya kwatsa maganar a tsakar gida, babu dai Wanda yace komai, dan azatonmu ba Sadeeq d’in Safara’u baneba, goshin magriba saiga Safara’u tashigo tana kuka. Na tsareta da tambaya da k’yar tacemin cikinsu ‘yan biyu tagani da Sadeeq a zauren gidan Malam halilu suna hira da dariya, kuma hardama mata gwalo akayi. Saboda na gaskata zancenta na sake aiken Rahma taganomin da idonta, harma taji Sadeeq d’in nafad’in ai koma miza’ayi bazai auri Safara’u ba, cikin wad’an nan munafukan yaran daba ganesu akeba zai aura, saboda darene yasani d’inne maganar a raina har safiyar yau d’inan, amma wlhy Alhaji da k’yar na iya barci nida Safara’u jiya.

鈥渉ummm鈥? kawai nafad’a ina dafe kaina, saboda jin Yanda aka canja maganar.

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

SOORAJ CHAPTER 5

RAINA KAMA CHAPTER 2