in

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 8

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 8

amma kinsan saura kad’an ya gane sultan yaron sane har tambaya yayi ko xan nuna masa mahaifiyar sultan, Afiya meyasa kika bar Aiman, Aiman ba irin maxan da mace suke gudu bane lokaci yayi da ya kamata ki sada sultan da mahaifin sa ki roqi gafarar iyayen ki tare da rungumar mijin ki. Innalillahi Afiya ta fada a hankali tare da tsinke wayar, duk abinda saif ke fada bata fahimci komai ba, Aiman a Portugal me yaxo yi, ya had’u da sultan har ya d’auki pic nasa, idan ya nuna a gida da inda ya had’u da sultan tabbas mahaifin ta xai gane tana nan kuma a gidan sa, xuwan sa ya same ta a wannan qasar ba kyau xai mata ba, is better taje da kanta, sanin mahaifin ta is a serious man kai tsaye a yau ma xai iya sauka a qasar idan yaji labari, hakan ya saka ta tunanin ta bar qasar yanxu. Aiman yana isa hotel d’in da ya sauka ya kira wanda ke tare da ilham su had’u airport yanxu, kana ya shiga wanka, bai jima ba ya fito da sauri dai dai lokacin wayar sa ta d’auki qara ganin mai martaba ne ya saka shi d’auka da sauri yana fad’in daddy yanxu xanje. Har yanxu kana Portugal d’in kenan, eh daddy but ehm.. ehm.. Sai ya rasa me ma xaice? Menene aiman? Daddy wani yaro nagani sak ni, sunan sa sultan yaxo tare da mahaifin sa d’axu asibitin da naje aiki. Murmushi mai martaba yayi tare da fad’in kana son yara yanxu kenan. Yace aa daddy wannan daban ne, yana kama dani sosai lemme send the pics 2ru family grup kagani sauran Ma su gani kaji me xasu ce. Yace tam shikenan, ya tsinke wayar yana kallon Alhaji Ahmad tare da fad’in kaji shirme irin na yarima daga ganin qaramin yaro dan kawai yana kama da kai sai ka rude haka. Abba yace da alama ya fara son yara yanxu amma a duniyar nan ai xaka had’u da wanda yayi kama da kai bayan babu alaqa ta jini. Sarki yace yanxu xai turo pic d’in mugani ai wace irin kama ce wannan da aiman ya rude akan ta. Yaya Aliyu dubi pic d’in da yaya Aiman ya turo a grup wallahi pic d’in yaron sak shi sanda yana qarami. Aliyu ya dubi pic d’in yana fad’in sosai suna da yanayi, ina ya sami yaron tam? Rumaisa ta kira umma tana fad’in umma kin ga wani yaro mai kama da yaya yarima da ya turo a yanxu, tace aa a ina yake. Tace ki duba yanxu ya turo bari na kira ammi ko ta ganshi yaya Aliyu ma yace suna da yanayi sosai, ta tsinke wayar tana kiran number ammi, bayan ta sanar da ita take cewa itama ta gani kada xargin ta ya xama gaskiya idan ta tuna afiya xata iya xuwa gidan ta buya acan Portugal wanda sam hankali da tunanin su bai taba basu hakan ba. Kallo d’aya sarki yayi wa pic d’in ya tabbatar da gaskiyar aiman, wannan kama ta baci akwai alaqa ta jini tare da wannan yaron domin bashi da banbanci ko kad’an da aiman sanda yana qarami, ina jin wani abu game da yaron ya fad’a yana miqawa su waziri wayar sa suga hoton da aiman ya turo. Abba ya dubi sarki bayan ya kalli pic d’in yace kace wace qasa aiman yaje. Sarki yace Portugal inaji. Abba yace Afiya tana can wannan yaron aiman ne, tabbas ban taba tunanin afiya xata iya barin qasar taje can ta buya ba ban taba tunanin haka ba, kasan ina da gida acan. Wani fain ciki ya lullube sarki yace kenan wannan yaron shine jaririn da afiya ta fita dashi, kira aiman ka sanar dashi kada ya kuskure ya bar qasar batare da afiya da yaron ba. Abba ya tashi yana dialing number aiman d’in tana ringing baa daga ba, sarki Ma ya gwada kiran nasa bai d’auka ba, Abba ya dubi sarki yana fad’in xan je qasar yanxu ta private jet d’ina. Aiman kuwa yanda yake shiri cikin sauri ya hana sa d’aukar wayar sa dake ringing yana gama shiri ya d’auki wayar batare da duba miss calls ba ya fice. Afiya kam tuni ta gama had’a kayan ta dana sultan bayan ta gama yiwa suzana bayanin abinda ke faruwa, bata tsaya kiran saif ko jiran sa ya dawo ya kawo drugs d’in sultan ba ta saka driver ya kaita airport. Mami meyasa kike rufe fuskar ki da wannan baqin abun, ta janye hannunsa tana gyara niqab d’in ta tare da d’ora yatsanta akan lips d’in sa tace bana son surutu yanxu. Ko da aiman ya sauka airport tuni ilham ta dad’e a wurin tana jiran sa, shigar su jirgi keda wuya afiya ta iso, bayan dogon bincike da fad’i ka tashi da tayi kafin a barta tabi jirgin masu xuwa Jordan, ta kashe kud’i sosai amma bata damu da hakan ba, suka shiga jirgin tana riqe da hannun sultan. MS Littafina na kud’i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980. Shigar ta jirgin keda wuya aiman ya shiga, ta qanqame sultan dake riqe da ball d’in sa sosai a jikinta kamar xai ganshi ne ya kwace mata shi, cikin qanqanin lokaci barci ya d’auki sultan har suka iso bai tashi ba. A hankali take saukowa daga matattakalar jirgin cikin kasaita, hannunta riqe da hannun sultan d’aya hannunta kuma tana rataye da wata yar madaidaciyar jaka mai matuqar kyau. Sanye take cikin doguwar riga pink, mai tarin duwatsu (stones) a gaban rigar, kanta nannade yake da gyalen rigar, sai fuskarta dake sanye da niqab, duk da haka kyawun idanunta kadai xai bayyana ita din kyakkyawar gaske ce. Ga tsayi ga diri, ta ko ina bata da makusa, kallo d’aya xaka mata kasan hutu da wayewa suna aiki a tattare da ita. A sanyaye ta cigaba da saukowa xuciyarta tamkar xata hudo qirjinta ta fito saboda tsananin bugawa da take, me hakan ke nufi har yanxu tana son Dr. Aiman Merah ne kome? No… ta girgiza kanta da sauri cikin son basar da xancen xuciyarta, tana son ta qaryata xuciyarta ta hanyar kauda tunanin sa ta kowane fannin, sautin muryar Sultan taji wanda ya maido hankalinta xuwa gare sa, ‘Mami na bar Ball dita acikin jirgi, ki jirani anan xanje na dauko, kafin tayi wani yunquri tuni ya fisge hannunsa daga nata yayi cikin jirgin da gudu. Hankalinta ya tashi sosai musamman da ta tuna Aiman Merah yana d’aya daga cikin mutanen da suka shigo jirgin tare dashi. Ta tuna sanda suke xaune cikin jirgin, tana rungume da Sultan da yayi barci, Dr merah ya shigo cikin isa da qasaitar sa, kallo d’aya tayi masa ta nemi gusar da hankalinta, Aiman yana nan yanda ta sansa ba abinda ya canxa daga gare sa na halinsa acikin shekaru hudu da tayi batare da shi ba, wannan qasaitar tana nan, wannan ji da kai da taqama duk sunanan sai Ma abinda ya qaru, haka kyawun fuskar sa ba qaramin rudata yayi ba, kallonsa take qasa da sama yana sanye cikin kayan sarauta dana qara fito dashi, tare da wata budurwa da nayi matuqar girgiza tunanin ta. Wacece wannan? Miye tsakanin ta da Aiman Merah? Me xasu je yi qasar Jordan? Duk bata da amsar wadannan tambayoyi nata ta lumshe idanuwanta yayin da xuciyarta ta cigaba da bugawa, ko dai Aiman ya manta da ita ne, yayi aure yake rayuwa da wata mace ba ita ba? Innalillahi ta fad’a a hankali cikin tashin hankali, duk gudun ta dalilin kada su had’u gasu a jirgi daya kuma xasu sauka a qasa d’aya, Allah ka dube ni gwanda na gujewa had’uwa ta da mahaifina akan aiman amma wacece wannan yarinyar da kaf a family d’in mu ban san ta ba, ko yayi aure wata xuciyar ta tambaya. No.. ta fada a hankali tana furzar da iska daga bakin ta a hankali, dan ma tana sanye da niqab da tuni mutane sun fahimci halin da take ciki, ta sake bude idanunta a Karo na biyu tana kallonsa, wannan Karon ya maida idanunsa da hankalinsa kan wayar sa, ta qanqame sultan a jikinta, yanda taga Aiman merah yau ya qara tabbatar mata da cewa babu ta a xuciyar shi ya manta da shafinta a rayuwar sa, taji tana qara son nisanta kanta daga gare sa, bata son yaga Sultan ko kadan yanda kamaninsa da komai nasa da yaron ya dauko. Wannan dalilin ne ya saka hankalin ta tashi sanda sultan ya nufi cikin jirgin, da sauri tabi bayansa dai dai lokacin Aiman ya sauko daga jirgin, yana tafiya cikin isa da qasaita tamkar baya son taka qasa, har yanxu wannan budurwar tana tare dashi. Kasancewar ita taxo da hanxari shi kuma yana tafe yana latsa wayar hannunsa yasa basu Ankara ba suka yi Karo da juna, jakar ta dake hannunta ta subulce ta fadi haka shima wayoyin sa ya saka lokaci d’aya. Da sauri ta russuna qasa domin tattara kayan ba don komai ba, bata son koda wasa yaga kwayar idonta tabbas xai gane ta, idanunta suka sauka akan dalleliyar wayar sa iPad mai kyau da tsada, ta ware idanunta sosai cikin faduwar gaba ganin pic din tane bayyane a wayar tana sanye da alkyabba, baxata manta lokacin da ya dauke ta pic din ba tana da cikin sultan acikin falon mahaifiyar sa, ta tsurawa photo ido tana tuno rayuwar ta da mai wayar, shin yarima ya sauya xuciyar sa daga qin mace ko me, yana sonta a ynxu kuwa, ita wannan da yake tare da ita mecece alaqarta dashi, da sauri ta dauki jakarta jin muryar sultan na kiran ‘Mami. Har yanxu Aiman na tsaye yana kallonta, baxaka tantance yanayin fuskar sa ba, bacin rai ko sabanin haka,tun lokacin da ya kula ta tsurawa photon wayar sa kallo, miye nata da photon ko kuma me take kallo acikin photon, me yiwuwa ta San ta ne? Dam xuciyar sa na buga, Affiya ta dago daga tsugunnen da take batare da ta kalle sa ba ta miqawa budurwar dake tare dashi wayoyinsa sannan ta juya da sauri ta bar gurin, daukar sultan tayi jikinta na rawa ta bar gurin kada tayi wata katobarar da xata sanya yarima ya fahimci ko ita wacece. Tsananin mamakin ta ya hana Aiman motsi, meyasa xata baiwa ilham wayarsa bayan ta san a hannunsa ta fadi, ya tabe bakinsa wannan ba damuwar sa bane can ta matse mata yaga alamar bata cikin nutsuwar ta daga yanda yaga jikinta yana rawa gashi garin sauri ita tabar tata wayar a qasa bata dauka ba, ya waiga a hankali yana kallon airport din babu ta babu alamarta, har xai juya ya tafi sai kuma yaji yana son daukar wayar kada wani ya dauka daban meyiyuwa akwai wani abu mai muhimmanci a wayar qila xasu sake haduwa ya bata wayar. Meyasa kake son ku sake haduwa, wata xuciyar ta tambayeshi da sauri ya kauda wannan tunanin ta hanyar yiwa ilham alamar da ta bashi wayar dake qasa batare da yayi magana ba. Ilham ta sunkuya ta dauko ta hada da nashi ta bashi, ya karba ya soma tafiya a hankali yana juya wayar a hannunsa cikin yatsina fuska kamar wanda ya dauki kashi a hannun sa. A hotel ta sauka bayan ta biya kud’in kwanakin da take gani xata iya kafin ta tattara ta koma gida inda sarki tasan shi kad’ai ne xata sami sassauci a wurin sa akan ta nufi nata iyayen. Mami meyasa muka xo wannan gidan ni bana son sa ina uncle da suzana. 2 days kawai xamuyi mu tafi, xo naji ko cikin har yanxu yana yima ciwo. Yace aa ya daina, mami wannan Doctor bai iya allura ba shi yace baxai min ba, he like me as a friend, babba ne haka kamar uncle saif yana da kyau sosai….. Hotel daya suka sauka wannan karon tare da ilham sai dai kowa da nashi d’aki, yana so ya kwanta ya huta xuwa anjima yaje asibiti ya duba fadila, wayar afiya ya ajiye gefe kafin ya soma dialing number Abba da ya ga miss call nashi sai dai wayar bata shiga yana kiran sarki ya d’aga tare da tambayar kana Portugal har yanxu? Yace yanxu na sauka Jordan daddy duk nagaji. Yace wannan yaron da ka turo pic d’insa yaron kane aiman na wajen afiya. Murmushi aiman yayi yana shafa sumar kanshi bayan ya lumshe idanuwan sa, yace daddy kaima kaga kamannin mu ashe dan ma baka ganshi sosai ba xaka fi yarda da maganar da nake gayama. Sarki yace ba wannan ba aiman afiya tana Portugal wannan yaron da ka gani tabbas jinin kane shine wannan jinjirin da ta tsere dashi tun baa yi sunan sa ba. Xumbur aiman ya miqe ya qara duba ko da wa yake waya tabbas mahaifin sa ne, da ba dan shi bane da ya qaryata abinda kunnuwansa suke jiyo masa, sarki ya cigaba da fad’in koma menene ka nutsu Alhaji Ahmed tuni ya isa qasar kada ka kuskura kace xaka je neman ta acan shi xai dawo da ita domin kai baxaka iya

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 7

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 9