in

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 7

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 7

kaduna, ina so ku fahimci juna kafin auren nan da sati biyu. Aiman ya dubi sarki yana yatsina fuska, daddy ka manta acikin sharuddan amincewa da auren kace babu takura akan abinda bana so, na amince xan aure ta fahimtar juna na me. Xaka je yarima, bana son iyayen yarinyar su xargi kamar ina yi Ma dole ne akan auren, idan kaje yanxu shikenan baxaka qara xuwa ba I promise…… …….. Yau kam ilham kwalliyar ta daban ce da ta ko yaushe tun da aka sanar da ita xuwan yarima ta kasa samun nutsuwa wani farin ciki take ji yana shigar ta ta ko ina a jikinta, baqin cikin ta d’aya ayeesh bata garin duk da haka xata bata labarin komai ta san a yau kam yarima ko waye shi kome yake taqama dashi sai ya dube ta wanda kyawun ta kad’ai xai rikitashi ya so ta. Kayan abinci kala kala aka had’a masa naji da gani. Tun da ta shiga falon mahaifin ta sanyayyan qamshi mai dad’in gaske ya ratsa hancin ta wanda ya sakar mata da mutuwar jiki lokaci d’aya, sallama tayi ta shiga idanun ta na kansa. Duka guards da dogarawa dake falon sai da suka amsa banda shi wanda ko alamar motsi bata gani a fatar bakin sa ba. Yana xaune kamar ko yaushe fuskar nan tasa tamau ba walwala, yau kam ba glass a idonsa hakan ya bata damar qara ganin oily eyes d’in sa dake rikita mata akan shi, duk da idanun na kan wayarsa hakan bai hana mata hango hasken su ba, Dogarawa uku ne a qasa wurin qafafun sa xaune, wasu biyu suna saman kanshi suna masa fifita kamar yanda aka yiwa mahaifin sa a baya, sai guards dake tsaye bakin kowacce qofar shigowa falon sun tare ko ina kamar masu gudun wani abu yaxo ya same su. Dogarawa suka soma fad’in takawar ki lafiya yar manya, matar yarima, gimbiya, yar qasaita matar qasaitaccen namiji, yarima na gaishe ki yana miki sannu da xuwa. Aiman dake sauraren su ya yatsina fuska yana qara tsuke ta tamau cikin takaicin su. Ilham kuwa wannan ikirarin ba qaramin dad’i yayi mata ba, ta saki murmushi a hankali ta nemi daya daga cikin sofa ta xauna tana fuskantar sa, nan wasu dogari suka yo kanta da sauri suka soma mata fifita kamar yanda ake mashi wanda hakan ba qaramin dad’i taji ba sai take jin kanta a sarki ma, ina ga ta aure shi to. An d’auki tsawon mintuna talatin koma fiye da hakan babu wanda ya qara magana a wurin sai su dogari da jifa jifa suke fad’in, An gaishe ki, Allah ya taimaki gimbiya, d’an sarkin sarakuna yarima na gaishe ki, kuma munxo nan ne domin amsa gayyata ta alkhairi da kika mana, wannan shine yarima wanda yake jiran gado yau ko gobe, yarima aiman merah y… yayi shiru sakamakon wani kallo da aiman d’in yayi masa hakan ba qaramin qona xuciyar ta yayi ba, me yake nufi ita bata ishe shi kallo bane ko kuma bata isa ayi mata ikirari ba, tana son magana dashi a sirrance batare da sun ji ba dan ta lura tsab xai kunya ta ta a gaban su. Da kyar ta motsa baki cikin isar mu irin ta mata masu ji da kansu, ta dube su tana fad’in ina son yin magana da shugaban ku. Suka sunkuya suna fad’in godiya muke ranki shi dad’e, umarnin ki dole mu bi… Aiman yayi masu alama da hannu akan su dawo kada wanda ya fita. Cikin bacin rai ta dubi aiman da har yau bai d’ora idonsa akan ta ba, tace meyasa, ina son magana da kai ta sirri meyasa kake min haka me kake nufi ne iye? Duk falon yayi tsit suna cike da mamakin yanda take wa yarima magana bata da labarin baa masa tsawa ko kuma magana cikin d’aga murya ne chab. Tsawon mintuna babu wanda ya sake magana a falon, ilham ta soma raina kanta wannan wane irin miskilin mutum ne da ko magana wuya take masa, yau fa ake yin ta ta fada a xuciyar ta, a hakan kuma xance ya xo suyi, xancen kurame ko wulaqanci? Aiman cikin qaguwa da xama a wurin domin wata tsanar ta da yake ji a xuciyarsa ta linka wadda yake mata a baya, yayi wa d’aya dogarin nasa alama da hannu ya sunkuya kad’an ya gayamasa magana a kunne, ganin tayi dogarin ya fita da sauri tace ashe dai yana magana I wish ko kad’an ne naji yanda muryarsa take, bai jima da fita ba sai ta ganshi ya dawo d’auke da paper da biro kunnen sa dai dai bakin aiman yana gayamasa magana shi kuma yana rubutawa a takarda. Bayan sun gama lokaci daya taga duk sun miqe kafin shi aiman ya tashi ko kallon inda take bai yi ba ya sa kai ya fice sauran suka Mora masa baya da sauri, dogarin ya ajiye takardar da kud’i a gabanta ya fice da sauri shima. Cikin rawar jiki ta d’auki takardar ta bud’a, _ashe baki da tarbiya, nayi mamakin kasancewar ki yar ministan ilimi bayan baa koya maki yanda xaki gaida mutane idan kin same su ba, ko a hakan ma Afiya ta fiki, xaki auri aiman amma kada ki taba tunanin xai so ki ko ya kula da ke, xaki xauna dani ne na dan wani lokaci kafin Afiya ta dawo, baxan damu da kowane hali xaki shiga ba I don’t care ke kika ji xaki iya aure na, Afiya kad’ai nake damuwa da ita a yanxu a wannan duniyar ma, ita kad’ai idanuwana suke kwadayin gani bake ba, ga kud’in biki nan kiyi amfani dasu idan basu isa ba akwai number daya daga cikin dogari akai ki kira ki sanar dashi xai gayamin_. Cabdi ta fada bayan ta gama karanta takardar cikin qunar xucci wannan wane irin wulqanci ne haka, ni xai had’a da dogari har yake sa yana rubutamin wannan takardar, wacece wannan Afiya da ya damu da ita haka, wane matsayi take dashi a xuciyarsa da yake ta ambaton ta haka, Afiya. Afiya.. Afiya… ta fada a hankali tare da lumshe idanuwanta hawaye masu xafi suka xubo mata. Mk Littafina na kud’i ne, dan Allah kada ka karanta idan baka biya ba, ga mai buqatar siya ya tuntubi wannan number 08169334980 Wlhy you will regret abinda kayi min yarima, sai ka xubar da hawaye akaina sai ka soni fiye da kowa a duniyar nan koda kuwa wacce tayi sanadiyar xuwan ka duniya ne, mtsew wai Afiya…. * Daddy xanje Phoenix na qara karatu akan gynecology and it will take me two years acan. Sarki ya dube sa yana fad’in amma da ilham d’in xaka je ko. Aiman ya yatsina fuska yana kallon sa, wacece haka kuma. Matar da xaka aura, ko kana nufin baka san sunan ta ba. Wani takaici yaji ya lullube shi ya dubi sarkin yana fad’in, ta xauna ba inda xanje da ita Afiya Ma naje da ita ne saboda karatun ta dama da kuma tirsasawar da kayi min amma wannan karon baxan je da kowa ba, just two years kamar gobe ne na dawo fa dad, please kada ka tursasani xuwa da yarinyar nan cos xata dawo da qafafun tane is better ta xauna anan. Murmushi sarki yayi yana fad’in shikenan babu damuwa, Allah ya bada sa’a, yaushe ne tafiyar? Jibi, some of my friends ma already har sun tafi dama mun dad’e muna plan akan course d’in musamman asibitin mu need gynecologist matsalolin mata yanxu yawa ne dasu. Yace hakane kayi tunani mai kyau, but ka qoqarta ko kad’an ne ka tsaya ayi biki da kai aiman. Bikin Afiya ma bana nan akayi balle akan wannan marar tarbiya d’in, ni xan tsaya ayi bikin ta dani, dad ka daina min mgnr wannan yarinyar haka. Amma yarima kayi aure har shekara biyu baka waiwayi matar ba ana haka? Tam a fasa auren daddy idan ta sami miji tayi aure idan bata samu ba sai ta jira har nadawo ayi auren, hakan yayi ma? ya tambaya yana kallonsa. Tun da labarin tafiyar aiman yaje wa iyayen ilham take ta kuka, sam iyayen basu ji dad’in haka ba sosai kuwa taya xaa yi auren mutumin da baya nan har tsawon shekara biyu ace ta xauna ta jira sa dama tare xasu je abin xai xo da sauqi, ganin ransu ya baci sosai sarki ya nemi da a d’aga auren xuwa lokacin da aiman d’in xai dawo amma fafur ilham taqi amincewa da hakan, ta yarda a d’aura auren xata xauna xaman jiran nasa har lokacin fa xai dawo cos tana da tabbacin watarana aiman sai ya mutu kanta ba irin su ake wulaqantawa haka a xauna lafiya ba. Bayan tafiyar aiman akayi auren ilham, ba wani shagali sosai akayi ba kasancewar uban gayyar baya qasar, tun bayan kawo ta gidan aka kaita nata sashen dake kusa dana Afiya, umma da kanta ta gayamata wacece Afiya a wurin aiman da kuma matsayin ta a wurin su, tun a lokacin ta qudira a ranta sai taga bayan Afiya domin baxata taba iya had’a abinda take so da wata macen ba. Auren

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 6

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 8