in

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 6

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 6

MULKI KO SARAUTA 2* 👑 ©Fertymerh Xarah💞 3 I named him El’ameen (Sultan).. ta fad’a tana kallon suzana cikin murmushi mai bayyane da farin ciki. Suzana ma murmushi tayi tana kallon baby dake barci, bata taba ganin yaro mai kyau irin sa ba, ko da yaushe xaka same ta rungume dashi tana kallon sa tana murmushi, ko da Afiya tayi maganar nanny tace sam bata san xancen ba, ita xata kula da sultan, murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba. Tayi shiru sosai cikin nutsuwa tana sauraren labarin da Afiya ke bata game da rayuwar da tayi da yarima, sosai suzana ta tausaya mata, Afiya ta share hawaye sosai tana fad’in I have been right or wrong for running away from my family, I miss them badly I miss Ammi and I miss Abba, ko a wane hali suke ciki yanxu na rashina? Nasan hankalin su baya kwance nasan suna cikin matsinan cin damuwa dalilin rashin sanin inda nake, yarima ya cutar da ni I hate him. Suzana tayi shiru cikin tausayin Afiya sosai, da kyar ta bud’e baki tana kallon Afiya, how I wish xan ganshi ko sau d’aya, how did he look like? Afiya tayi murmushi tana goge hawayen ta, Prince Aiman Merah is handsome beyond your expectations, his face look so pure and innocent, so sweet and beautiful, he was screwed up and brilliant, he looked like an angel with a dangerous smile, his love had made me go crazy, I had become a psychopath, ta dafe kanta tana murza goshin ta Aiman yana da kyau sosai kamar yanda kika ga sultan, amma shi d’in miskiline na gaske mai ji da sarauta kuma mugu ne his every smiled is cruel, his entire existence was criminal, it was toxic, I was filled with his poison but blessed with his beauty and rage Sultan. Sultan is a gift to me gift to my life, ina son shi ina matuqar son sa fiye da son da nayi wa mahaifin sa a baya. Duk suka yi shiru na wani lokaci kowa da tunanin da yake a xuciyarsa kafin Afiya ta tashi ta bar falon cike da damuwa, ko kad’an bata son tuna aiman ko kad’an bata son tuna ta san shi ko wata alaqa ta taba had’a su. (Suzana baturiya ce dake xaune a qasar Portugal babu ta yanda xakuyi tunanin taji Hausa ko kad’an, ko da tana magana da turanci ne take magana bana son yawaita sa turanci a novel nawa tunda ba English novel bane, da fatar kun fahimta). * Shiru yayi yana kallon mahaifiyar sa cikin tashin hankali wanda sam fuskar sa bata nuna hakan ba sai da xuciyar sa dake masa xafi sosai jin itama sam bata bada goyon bayan ya bar qasar ba, idan har ya bar qasar to an sami Afiya kuma qafar sa qafar ta a duk inda xai je. Kamar baxai yi magana ba ya bud’e baki da kyar cikin sanyin murya yana kallon ta, Umma meyasa kuke ganin laifina akan abinda bani da hannu bani da masaniya akan sa, ni xan d’auki Afiya ne naje na batar da ita. Kai kuwa kake da sa hannu a batan ta tunda dalilin ka ta gudu, dalilin abin kunya da kaje ka aikata, ya rumtse idanun sa cikin jin xafin kalamanta. Yace kema kin yarda da maganar wannan dabbar kema kin yarda xan iya aikata zina, kema kin yarda xan xauna da wata mace ina mu’amala da ita bayan babu alaqa ta aure a tsakani na da ita, damn it ya fad’a yana kai hannu goshin sa tamkar ya fashe da kuka, ya tashi ya soma safa da marwa a tsakiyar qayataccen d’akin ta kafin ya juyo yana fad’in its your son umma, ban canxa ba, ina nan yanda kika sanni, matata yar uwata Afiya ban so ta ba sai wannan dabba, why umma meyasa keda dad kun kasa fahimta ta meyasa kun kasa gane cewa babu wanda nake so da qauna a duniyar nan bayan ku uku, ban taba son wani bayan ke da dad da rumaisa ba, bayan ku bansan taya Zan so wani mutum ba ban san ta inda xan fara son wani ba, bana son kowa sama da ku a duniyar nan kuma baxan so kowa ba. Innalillahi aiman ta fad’a

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 5

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 7