in

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 10

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 10

Nesa kad’an da sarki ya xauna tare da sunkuyar da kansa kasa, bayan ya shiga falon sarki. Akwai damuwa ne yarima? Sarki ya tambaya yana kallon sa. Ina neman afuwa idan nayi ba dai dai ba daddy, na yanke hukunci batare da shawarar ku ko sanar da ku ba, kayi haquri daddy. Menene sarki ya qara tambaya Karo na biyu. Na yanke igiyar aure na d’aya da ilham, kayi min afuwa. Sarki ya sauya fuska sosai xuwa bacin rai yayi shiru ya rasa me xaice ma saboda baqin ciki daya ke ji, kallo d’aya aiman yayi masa ya maida kansa ya sunkuyar cikin tashin hankali da ganin yanayin sarki. Nan take ya soma yi masa bayanin komai da yanda suka yi da Saif har had’uwar afiya da saif kamar yanda ya bashi lbr da taimakon da yayi masu da alaqar sa da ilham, ya qara da fad’in na sake ta ne saboda tana da wanda take so yake son ta daddy, ban d’ora mata iddah ba har tsawon wannan lokacin, baxan iya kasancewa da kowa ba bayan afiya daddy dan Allah ka fahimce ni ya fada tare da riqo hannun sarki yana roqon sa. Sarki ya dafa kansa, wannan hukuncin bai yi ba aiman, meyasa xaka yanke hukunci batare da sanin mu ba, kuskuren ka d’aya na sakin ilham yarima, me kake so iyayen ta su d’auke mu, wane irin kallo kake tunanin xasu mana, na aura ma mace tsawon wannan shekaru baka taba kula ta ba wane irin mutum ne kai, kasan haqqoqi da xamantakewar aure kuwa, kasan hukuncin namijin da ya danne haqqin matar sa idan kai baka neman haqqin ita bata so ne, kaci amanar da na baka aiman, ka kasa kulawa da abinda na d’auko daga wani gari na raba ta da iyayen ta na baka ita ka cutar da ita, baka yiwa Alhaji Ahmed adalci ba daya nema maka wannan yarinyar aka aura maka ita, mata nawa ne a duniyar nan ake raba su da iyayen su ayi masu aure irin naka kuma su xauna lafiya, yarinyar ta xauna tayi wa iyayen ta biyayya amma kai ka kasa mana biyayya? Daddy kayi haquri, baka fahimce… Shut up, baxan fahimce ka ba saboda bani da fahimta da hankalin da xan gane abinda ka aikata right. Aiman ya xuba masa manyan idanuwan sa cikin tsoro da fargaba, ba haka nake nufi ba daddy am so sorry please. Cikin fusata sarki yace please get out. Aiman xai yi magana d’aya daga cikin dogari daga waje dake tsaye ya shigo da sauri ya durqusa tare da fad’in. Ranka shi dad’e gimbiya afiya ce ta aiko tana so ayi mata ixini taga wannan matar da aka rufe a rumfar hukunta bayi. Aiman ya dube sa cikin bacin rai, ka sanar da ita baa mata ixini ba. Ni nayi mata ixini taje, je ka sanar da ita hakan, ya fad’a cikin bacin rai. Godiya take ranka shi dad’e ya tashi ya fice da sauri, aiman ya maida duban sa ga sarki but daddy… Get out nace ya qara katse sa, jiki a sanyaye ya tashi ya fita mahaifin sa bai taba masa irin haka ba kenan yayi laifi babba na rabuwa da ilham a gurin sarki bai sani ba, meyasa baxai fahimce sa ba, yayi shiru yana kallon yanda ake fito da kayan ilham d’in ana sakawa a mota, ashe saif d’in Ma ya xo yana ganin aiman ya nufe sa da sauri tare da miqa masa hannun sa na dama suka gaisa. Nagode sosai Doctor bansan da wace irin kalma xan furta ma saboda farin ciki da wannan abin da kayi min ba, na roqi Allah ya saka ma da mafificin alkhairi akan abinda kayi. Aiman yayi murmushi duk da yana cikin bacin rai bai yi magana ba ya xubawa afiya idanu da ta fito daga sashen ta bayi suna bayan ta, kallo d’aya tayi masu daga shi har saif ta d’auke kanta ta nufi sashen umma, tana shiga ta tarad da ilham tare da umma, Fuskar umma ta nuna tana cikin damuwa da alhini sosai tun lokacin da ilham taxo ta sanar da ita maganar xata tafi auren ta ya qare da aiman, haka ma afiya lokacin da taji abin taji wani iri though bata nuna ba sai ma ta fice daga sashen duk yanda ilham taso tayi magana da afiya bata sami fuska a wurin ta ba, Suna tsaye ilham ta fito, ma’aikatan gidan da bayi duk sun mora mata baya sun mata rakiya, da yawa daga cikin su basu ji dad’in tafiyar ta ba, ilham tana da sauqin kai sosai a gidan bata taba samun matsala da kowa ba kamar yanda mai karatu ke tunanin ko ita d’in mafada’ciya ce. Falon sarki ta nufa, kallo daya yayi mata yaji tausayin yarinyar sosai tana da haquri da biyayya, baa taba kawo masa qarar ilham cewa tayi wani abin ba dai dai ba kamar yanda ake kawo masa na afiya, tayi haquri boye sirrin ta dana mijin ta batare da ta sanar da kowa irin xaman da take da yarima ba, tabbas ilham ta cancanci lambar yabo a gurin sa, yayi mata kyauta ta musamman mai girma da tsoka sa’anan ya had’a ta da waziri da galadima domin suje gida da ita suyi bayanin abinda ke faruwa da dalili baxaa barta ita kad’ai taje gida da wani ba alhali da kansu suka aika aka d’auko masu ita bayan auren ta da yarima, ya bata haquri sosai tare da yi mata godiya, itama godiyar tayi ta fito. Kallon aiman tayi Karo na biyu ta sakar mashi murmushi mai qayatarwa, tace nagode da dukkan abinda kayi min na alkhairi baxan manta da kai ba a rayuwa kuma duk wani laifi da kake ganin kayi min na yafe ma har abada. Yace nima na yafe maki ilham ballantana Ma babu abinda kika min nine Ma nayi maki, ina qara roqon da ki yafe min, ya juya yana kallon Saif ga amanar qanwata ilham idan ka cutar da ita baxan taba yafe ma ba. Saif yayi murmushi tare da fad’in na karbi wannan amanar da hannu biyu Doctor xanyi qoqarin kulawa da ita gwargwadon iyawa ta insha Allah. Ilham ta juya ga mutanen da suka mata rakiya tayi masu godiya sosai tare da masu alkhairi itama, aiman da kansa ya bud’e mata motar ta shiga yana murmushi tare da fad’in your Highness ki shiga ki xauna. Ta shiga motar tana hawaye bayan ta qarewa gidan kallo sosai, su waziri suka shiga tasu motar daban suna bayan su, aiman ya rufe motar tare da sunkuyawa ta glass ya dubi saif ya maida duban sa gare ta, you don’t have to cry my dear, saif xai kawo ki watarana I know and again nima xaki ganni naxo maki, kafin Ma kixo ni xan fara xuwa daurin aure idan an gayyace ni. Ta boye fuskar ta cikin jin nauyin sa ya matsa kad’an shima yana dariya tare da d’aga masu hannu har suka fice, da yawa bayi, fadawa da sauran mutanen dake harabar gidan xubawa aiman idanu suka yi cikin tsananin mamaki ashe yana dariya haka basu taba ganin dariyar sa, bai Ma san suna yi ba bai damu da su ba ya juya ya bar wurin yana jin duk ba dad’i, magen sa ta tafi ta bar sa sarkin son jiki Allah ya so sama da bai biye mata ba da yanxu mai afkuwa ta afku ina maganar sakin ta, baxai taba sakin ta ba komai halaccin saif a gare sa domin yana tsanani kishin wani yabi wannan hanyar da yabi koma ya kalle masa wurin. Afiya tun da taga halin da nabila take ciki da yanda ta koma hankalinta ya tashi sosai, tsananin tausayi ya saka ta fashewa da kuka musamman da ta tuna ko wacece nabila, yar gayu amma itace a haka yanxu. Nabila kuwa a xuciya da gangar jiki cike suke da tashin hankalin ganin yanda afiya ta koma kamar ba ita ba, ta xama qasaitacciyar mace mai kyau da aji not like before da take yarinya mai taqama da kud’i, wannan ganin da tayi wa afiya a yanxu ya tabbatar mata da har abada muddin aiman na ganin afiya baxai taba son ta ko kula da ita ba, baxata taba yarda aiman ya rayu da wata ya mace a duniya bayan ita ba da haka gwanda kowa ya rasa, tabbas ilham ba qaramin kyautawa kanta tayi ba da ta bar gidan dan yanxu labari yake xo mata na aiman ya saki ilham, dama xai saki afiya da ta barshi da rayuwar sa wanda take da tabbacin xai so ta tunda ya rasa afiya amma kashe tasan abu mai wahala ne wannan. A fuska kuwa kuka ta fashe da shi tare da rungumo qafafun afiya tana roqon ta da tayi mata hanyar da xata fitar da ita a gidan tun da dama an rufe ta ne saboda batan ta yau gashi ta dawo cikin yan uwan ta itama tana so a fidda ta. Babu kyama ko kyankyami afiya ta jawo ta tare da had’a ta da jikinta ta rungume. Nice sila da wanna yanayin da kike ciki, da ban tafi ba da baa rufe ki anan kika wulaqanta ba, ki yafe min nabila kuma nayi maki alqawari a yau baxa ki qara kwana a wannan wurin ba. Nabila ta d’ago tana kallon ta kafin tace baki da wani laifi anan afiya, nice na saka kaina a wannan wahala, soyayya ta janyo min wannan uquba nayi qarya akan ina da cikin aiman bayan ba haka bane nayi ne saboda a aura min shi ashe ban sani ba na jawa kaina babban kuskure a rayuwa. Dama sharri kike masa nabila, afiya ta tambaya cikin mamaki. Sharri ne nabila ta fad’a tana kuka. Amma nima kin cuce ni kin cutar da tawa rayuwar na

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 9

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 11 KARSHE