in

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 1

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 1

Danqareriyar motace tayi parking harabar gidan, yanayin parking din motar xai tabbatar ma ranta a bace yake da sauri ta fito ta nufi cikin gidan batare da ta kula da mutanen dake xubewa qasa wurin gaidata ba a babban falo ta taradda mahaifiyarta tare da maaikatan gidan , ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka tace ammi kinga yaya Aliyu ya hanamin sakewa a party ya hanamin sukuni duk yabi ya takuramin saboda kawai nasan wadannan kayan shine yace sai na dawo gida………sai hawaye sharrrrrrrr ammi ta dubi shigarta kafin ta maida kallonta ga aliyu dake shigowa falon tace Aliyu ko meye damuwarka akan shigar auta yace ammi da kanki kike wannan mgnr bayan kinsan wannan shigar bata kamace taba tana musulma, ammi ta bata rai tana kallon Affiya tace auta yi haquri kibarsa, jeki cnxa kayan ko ki dora jallabiya akai, affiya ta tunxure bakinta tayi kwafa tafice falon tana qunquni Aliyu ya xauna a luntsumemiyar kujerar dake falon yana kallonta yace ammi duk kece ke saganta yarinyar nan wlhy tace menene riba idan na hana mata yin abinda takeso a rayuwarta, yayi shiru ganin ta sauya fuskarta yace gobe xnje kaduna auren amir idan baffa ya sauko ki sanar dashi ta gyada kanta tace Allah ya kai lfy ya amsa da amin bayan ya maida idanuwansa ga t.v 2 TUSHEN LABARI Alhaji Ahmad merah wanda akafi sani da sarkin xamfara, yana xaune abuja tare da iyalinsa yana da mata biyu hjy xainab da hjy hadixa hjy xainab yayace a gurin hjy amina (mahaifiyar affiya da aliyu) tana da ya’ya biyu Aiman da rumaisa sai hjy hadixa dake da ya’ya uku duka mata asmau sumayya da firdausi (duk sunyi aure kasancewar sun girmi su aiman da rumaisa) gidansu qaton gidane kamr unguwa, gidane da yawanci mutane kewa laqabi da aljannah duniya kasancewar dukiyarda aka narka a gidan ga kuma sarauta * [8:54AM, 10/15/2015] Pherty: Alhaji usaman wanda akafi sani da president mahaifine a gun affiya da aliyu matarsa dayace hjy amina(qanwar hjy xainab mahaifiyar aiman da rumaisa) asalinsu shuwa’arab ne Alhaji Ahmad da Alhaji usman abokan junane shiyasa sukayi alqawarin aurad da ya’yansu batare da sanin juna ba kasancewar aiman na karatu a pheonix yarima aiman wnda akafi sani da prince a pheonix yana gab da kammala karatunsa na likita yafito amatsayin Dr.Merah wannan shine burinsa mutum ne miskilin gaske maiji da kansa maiji da qasaita da sarauta saboda miskilancinsa abinda bai shafe shi ba baya shiga kuma yana da kafiya da naci akan duk abinda yasawa gaba yana da tabbacin sai ya samesa mata da yawa na matuqar qaunarsa suna yawan kawo kansu garesa saboda kyawunsa da ynda yake tfyr da qasaitarsa 3 Bai taba shaawar ko daya daga cikinsu ba saboda ba halinsa bane neman mata acewarsa ma mata basa birgeshi sunfi bashi haushi shiyasa da yawa yake bata lokacinsa da tunaninsa a library yana karatu bai taba so ba, bai taba fadawa akan soba, bai san menene so ba bai dauki so da daraja ba ya daukeshi tamkar damuwa da bacin rai ne shiyasa baya sa kansa aciki yanajin haushin mutane dake bata lokacinsu akan soyayya suke bata tunaninsu da xuciyarsu akan so [9:04AM, 10/15/2015] Pherty: wani abune da xuciyarsa da gangar jikinsa sun kasa gasgasta masa muhimmancin so bai damu da kallon films ba musamman na india saboda haushinsu da yakeji yana gani aduniya ba mutanen dana kaisu xama wawaye kamr ynda suka maida kansu bayin mata aduniya yafi bawa kwallo da karatunsa muhimmanci haka duk tunaninsa da burinsa nakan kwallo da karatunsa sune ya dauka rayuwa sune yake gani kamar ginshiqin rayuwa hr yake ganin idan babusu rayuwarsa ta xama useless ba wai soyayya da kashi casa’in acikinta duk yaudara ne Hankalinsa da tunaninsa nakan laptop dinsa, xuciyarsa ta soma yimasa xafi saboda yakasa samun abinda yakeso ya duqufa neman hanyar da xai sami amsar assignment dinsa yaja dogon tsaki bayan ya kawar da laptop din daga gefensa badan ya haqura ba sai dan nemawa xuciyarsa sassauci daga xafin data dauka 4 Assalamu Alaikum ta fada cikin siririyar muryarta mai xaqin gaske, ya amsa sallamar sanin muhimmancinta batare da ya dubi mai sallamar ba saboda jin muryar macece bata damu da rashin nuna kulawarsa ba tasan sarai kowaye aiman merah taja kujerar dake kusa dashi ta xauna fuskarta dauke da murmushi [9:21AM, 10/15/2015] Pherty: tace sannu prince bai amsa ba bai kuma kalletaba kuma bashida niyar haka sai ya lumshe idanuwansa yana tunanin ummansa wanda ya xama dole yaje gida nigeria dan ganinta tace aiman kaqi ka kalleni balle nasami damar sanarda kai abinda k tafe dani nan ma shiru yayi idanuwansa a lumshe bata saduda ba taci gaba da fadin idan kudi kake taqama dasu mahaifina nadasu idanma kyawune nima inadashi amma meyasa kake wulaqantani meyasa kake nuna halin ko inkula agareni duk da dimbin soyayyar da bake ma sai alokacin ya ware manyan idanuwansa akanta sai da xuciyarta na buga saboda tsananin kyawun da yayi mata baqaramin tsaita hankalinta tayiba saboda mutuwar jiki da kasala dana saukar mata kallonta yake yanason gane wani abu atare da ita ba abibda ya fahimta illah ita farace kyakkyawa mai kaurin jiki gajera amma duk bata birgeshiba ya dauke dubansa gareta ya rasa da wace kalma xai mata mgn saboda baisaba da doguwar mgn ba ya soma kwashe manyan wayoyinsa da system dinsa ya tashi xai bar wurin itama tayi saurin tashi 5 tace koda baxaka aureniba ya kamata atleast ka bani lokaci na nunama irin soyayyar da nake ma kasoni koda na dan wani lokaci ne pls prince….. ta fada idanunta taf da hawaye saboda axabtuwa da take da qaunarsa sai alokacin yasami damar mgn yace kinga nayi kama da mutumin bnxane tayi saurin girgixa kanta yace kinga ina neman matane nan ma girgixa kanta tayi yaja dogon tsaki yace ke banxa dake kina a hakan kike neman da soyayya tace nice banxa aiman yace eh an fada idan k ba banxa bace meyasa kike kai kanki ga namiji tace laifine dan na nuna ma so aiman [9:51AM, 10/15/2015] Pherty: yace so? ta gyada kanta tana kallonsa yayi murmushin dana qara fito da kyawunsa karo na farko kenan a shekarun da ta hadu dashi a skul din data ga

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

YARIMA ASHMAN CHAPTER 14 KARSHE

MULKI KO SARAUTA CHAPTER 2