in

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 2

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 2

MU ZUBA MU GANI CHAPTER 2

Haysam ne ke tsaye tareda nasu amsan uban Wanda ta tsokano, da sauri inna da daddy har suna hada baki sukace waye kenan daga kafada haysam yayi yace kutambayeta ni shigowanta kenan..+ Kai ar cewan inna ai sai nayi tunanin agabanka akayima shashncin banza kawai, yar inna kifadamun ubanwaye wane tatsaya masa agarinnan.. Cikin kuka tace wani ne inna a chan kasan layi daga yazage ni Rama shikenan fa ya titseni a lungu yayi ta marina harda sani tsalen kwadi.. Ai nan inma ta dire tace inna wlh sai taga Wanda yatsaya masa a garinan gyalenta ta jawo tace taso muje.. Cikin sauri daddy yasha babanta yace inna abi abin a hankali, Cikeda fada inna tace anki abi a hankali yar
muhammadu tilo din zaama haka ace kuma nayi shiru ke taso ki nunamun gidansu naje nasamu uwarsa.. Da sauri bazla tamike sanin batasan wazata ce shibane tace inna badan garin nan ne bafa dama garinsun zaije Lokacin da abun yafaru.. Dan wane garine cewan daddy, da sauri bazla tace ni daddy na riga na yafe masa abar maganan dama ai ni na tsokanesa… Duk yarda innata kada hakanan bazla ta dage ita tafa yafe masa dan a dole inna ta hakura ta gasa ta.. Washe gari da kyar aka shawo kan bazla ta yarda zata bisu kano so da safe suka dauka hanyen cikin garin kano..a yankaba suka isa gaban bakin wani katoton gida kanakallan gidan kasan ba karamin uban kudi aka kashe cikin gidan ba, horn haysam yayi mai gadi ya wangale masu gate din gidan parking space ya nifa inda motochi sunyi biyar a gurin farka motan yayi, daddy ne yafara fita kana wa budema inna tafito kana bazla ta fito, makale wa tayi bayan inna dan ita hakanan taji gidan bai mata ba.. Jagora daddy ya musu zuwa main cikin gidan da gudu wata yarinya da kana ganinta kadan bazla zata girmeta tafito ta rungume daddy in tana oyoyo daddy oyoyo daga ta sama yayi yace oyoyo mamana, kallan bayan daddy yarinyan da aka kira da mamana tayi kallon inna ta danyi kafun ta kalla bazla then kuma ta kalla babanta tace daddy? Alamun su wanene. Dan shafa kanta daddy yayi yace your grand ma da kuma yayarki cikeda murna yarinyan ta je ta rungume inna tace oyoyo takwara dama daddy yanata ban labarinki inatasan na ganki sosai sosai, rugometa inna tayi kafun suka shiga cikin parlour din.. Large parlour ne da yaji luxuries,gwanin shaawa, kujera inna taja ta zauna tana mamakin yarda danta yayi kudin da batasan dasu ba a zuciyarta taringa debema Hafsat Matar daddy dan tace ita tarabatadshi… Sunfi minti biyar a zaune amma ba matar gida ba alamarta ” “Ita isashiyar batasan uwarka ta ISO bane da bazata iyazuwa ta gaishe ni ba ko kuwa yayane “cewar inna, dan yake daddy yayi dan shima abun Bakadan yabata masa raiba dan tun shigowarsu yakira wayanta a kan ta sauko amma shiru, Mikewa yayi ya nufa wani staircase in ran sa ba dadi, part in ta yanufa bako sallama ya shiga bedroom dintan kai tsaye, zaune yaganta gaban mirror tanata yan shafe shafenta, “hafsa yakira sunanta mene kike daukan kanki ko kike tunanine da har mahaifiyata zata zo gidananan sama da minti biyar amma kina zaune bamaki da akaman zuwa ki gaishe ta.. Mikewa tayi tana masa wani kallo kafun tace to nasani tazo sai mene shikenan kuma ni bazan gyarjikina ba? Inacewa bayanzu zata tafiba? Kuma nace talatu mai aikina ta kaimata duk mai takeso, sai mene kuma goyata kakeso nayine.. Tas bata anakaraba taji ya

dauke ta da wani zazzafan Mari tareda nuna ta da dan yatsa jikinsa har wani rawa yake sabida baccin rai yace”ki san mai zakinafada kan mahaifiyata wlh sosai zan saba miki akanta haka zalika zama tazo na dindin din idan na din gidankine to yau ki kureta, . Dafe gurin tayi tace ni kamara Daddyn haysam for the first time Akan wata ni, saiga hawaye… Wani mugun kallo yabata yace yes namarekidin, fingers dinsa yashiga kadawa yace’ ke wlh next time nasake jin wani disrespectful words tsakanin ki da inna wlh saina sake ki dan a duniyar nan banga macen da zata raina mahaifiyata ba na jureta Kema dinkinci darajar yaranki uku ne and yanzunan nakeso kije kigaidata tareda bata hakurin kin fitowan ki with full respect… Bam yamata banging door din yamata ya juya ya fita, wani still tayi agurin dan bata taba tunanin zai fada mata hakan ba, wani mugun tsorone yashigeta dan tasan hakan bakaramin bakinsa bane itakuma duk duniya batajin akwai Wanda zata iya zaman aure dashi bayan shidin, zullumi tafara a ranta ta ayyana yazama dole ta koma gun bokanta dan gadukkan allamu abun yakunce, mutum da intace abu yau yazauna yau shi yamata hka,, da sauri tanufa hanyan sauka dan wani sabon tsorone ya shigeta dolene tayi taka tsantsan da lamarin nan.. Zaune tagan haysam yana danma inna hira kadan kadan gakuma Amrah tayi Kane Kane jikin inna whilst jamaludeen autanta kan cinyan inna Wanda bata san lokacin da yabaro lesson yazo gunba, wani tukukin bakinciki taji yarufeta dan ita gani take kaman kwacemata yara inna zatayi daga zuwanta, danne abunda ke damunta tayi takarasa ta zauna gefen daddy, dan durkuso tayi tace inna ina wuni, kinzo lapia! Nashiga wankane shiyasa ban fito da wuriba… Wani kallo inna tabata sanan tace ai karkiji komai isace tasa hakan sanan mu lapianmu kalau, juyawa tayi tacigaba dajin hirar school da jamal ke bata.. Dan zingurin bazla haysam yafara da kafa yarda bawanda zai gani, dago ido tayi tasa cikin nasa, alama yamata Akan ta gaida mommy, zinbur tayida baki kafun tace ina wuni, Banza mommy tamata kaman batajitaba, kara gaisheta bazla tayi tace cewa nake ina wunifa Maman ya haysam. Ke rufe mun baki shashasha yar kauye uban wane kikema magana haka din, sai kuma ta maida kallonta kan haysam tace ita kuma wanan yar aikin da kuka taho da ai ban ne maba talatu ma kadai isheni ni banasan tarkace.. Wani warning tone inna tafitar tace ke ke hafsatu kifita idona na rufe wlh kul a hir dinki nuna bazla tayi tace kinga Akan wanan yarinyar to wlh kano tamana kadan dan wlh da ki tabata gwara ki tabani Nasan ke din yar karasa tarbiyace, dan yar Muhammad tilo banga shegen da yaisa yamata tozarciba duk kudinsa kuwa., kuma wannan gida da kika muzo bacin arziki mukazo ba ki tambaya mijinki zaifada miki, ni da kike ganina hakanan magana daya zanyi a fitar minke a cikin gidan.. Dan tsugunnawa mommy tayi da wani fake ladabinta tace kiyi hakuri inna wlh banganetaba bane hakan bazai sake faruwaba insha Allahu.. Mikewa inna tayi rike da hannun jamal tace yafidai kinga kowa sai ya zauna lapia cikin gidan nan! Kallon daddy tayi tace to malam a bamu masauki ko ma zauna sosai ko? Da sauri daddy yayi gaba dan musu Jagora already dama haysam yagama kai musu luggage’s in su, wani part yakaisu daban Wanda dagani ba zama akai cikinsa ba sosai gurin ya kayato babban parlour ne sai two bedroom , kitchen then dining area sosai inna tayaba gurin inda daddy yafada mata dama dan ita yayi gurin, albarka tayi tasaka masa whilst shikuma yakara bata hakuri kan abunda matarsa tayi tareda tabbacin hakan bazai kuma faruwaba… Koda aka nuna ma bazla dakinta inacewa tayi ina ai bazasuraba gun kwanaba saita kara wayau hakadai sukayi ta Santin guri!!Haysam ne ke tsaye tareda nasu amsan uban Wanda ta tsokano, da sauri inna da daddy har suna hada baki sukace waye kenan daga kafada haysam yayi yace kutambayeta ni shigowanta kenan..+ Kai ar cewan inna ai sai nayi tunanin agabanka akayima shashncin banza kawai, yar inna kifadamun ubanwaye wane tatsaya masa agarinnan.. Cikin kuka tace wani ne inna a chan kasan layi daga yazage ni Rama shikenan fa ya titseni a lungu yayi ta marina harda sani tsalen kwadi.. Ai nan inma ta dire tace inna wlh sai taga Wanda yatsaya masa a garinan gyalenta ta jawo tace taso muje.. Cikin sauri daddy yasha babanta yace inna abi abin a hankali, Cikeda fada inna tace anki abi a hankali yar muhammadu tilo din zaama haka ace kuma nayi shiru ke taso ki nunamun gidansu naje nasamu uwarsa.. Da sauri bazla tamike sanin batasan wazata ce shibane tace inna badan garin nan ne bafa dama garinsun zaije Lokacin da abun yafaru.. Dan wane garine cewan daddy, da sauri bazla tace ni daddy na riga na yafe masa abar maganan dama ai ni na tsokanesa… Duk yarda innata kada

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 1

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 3