in

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 1

MU ZUBA MU GANI CHAPTER 1

MU ZUBA MU GANI CHAPTER 1

Kai kai wlh dan tani ga shegiyar yarinyannan kasan jiyafa a Wajejen layin mai gari ka zagi ubanta akan tayi fada da budurwarka tine, to wlh gwara yanzunan muyi ta kanmu dai ba kai ba nikaina ba raga mun zatayi ba…+ Wanda aka kira da dan tani ne ya bantara raken dayake sha yace to inbanda abunka dan lami ni ai bana tsoran yarcan maikama da yan ruwa, ba inda zani alquran kuma tazo nan tamun iskanci na hada mata jikin ta kara bantaran rakensa yayi tareda kara gyara zamansa, Kada kai dan lami yayi sannan yakala daya abokinsa yace kajifa Audu abunda dan tani kecewa ba shi alallai baijin tsoran yar inna ai ba karfinba fitsarar tata nake jimasa, kagafa ranan a burtsatsen malam haru abunda tayima garbe yanaji yanakallo tace ya tabata kuma dole gurin aka rufar masa da tsinanen duka har saida yayi jinya a binni, kar kade yarsharar sa yayi yace nikam yarinyar can tafi karfina haka kwai da mutuncina bazan bari yarinya karama da zubar minshiba dan haka ni kaga tafiyata.. Shima Audu cigaba yayi da shan rakensa yace mu Allah muntuba wacce tasha da iskanci ne bamu gani ba ai ba yar inna ba ko yar babace yau sai taci jakar ubanta takawo mana iskancii… Rufe bakin Audi keda wuya kuwa saiga yarinyan ta taho da wasu kayanta kirar Pakistan wadanda suka sha datti sabida wasan kasa, inda tayi amfani da dankwalin Kayan ta ci damara Kanta bude inda yake bayyana dogon gashinta Wanda ya watsu kafadunta yasha kitson maryam makiba, Wanda aka bule da kasa, gawata yar sandarta rike a ahannu tana ta kadawa tana yan raye rayenta na mutan kawye
, kanaganinta dai kasan ansha wasan kasa tana yan tsalle tsallenta tazo tawuce ta gefen dakalindasu dan tani ke zaune, har ta danyi gaba dasu sai kuma taja birki ta tsaya dan hannunta ta daura kan habarta tace “billahillazii kaman fa dan tani ne kan dakalin chan, in kuwa shine ashe kuwa akwai bura uba a garinnan da jiya da ya zagi ubana wlh yaci Saa maigari yana kofar gidansa shikaine yasaka ban fasa masa kai da dutse ba, Dan kuwa ni duk garin nan maigari da inna ne kwai zasuje mun bari in bari shima maigarin kawai dan ina kunyar farin gemunsa ne, Wani murmushin mugunta tayi dalilin wata dabara da ta fado mata! Juyawa tayi ta koma gurin da su dan tani ke zaune ta rike kugu tana kar Kada kafafuwa..
Wani kallon rainin wayau dan tani yabata sannan yace ke mai kikenema anan ko kina bin wani bashi ne yakarasa zancen yana wani zazzare ido ko Allah yasa taji tsoransa.. Murguda dan karamin pink lips dinta tayi sannan tace ai walh dan tani kafini sanin mai yafaru kuma da kace ina bin wani bashi ashe kanada ciwon mantuwa ban saniba dan quranin ubangiji tunda ka zagi ubana baicimaka ba baisha makaba haka nan yana kasa akwance kanasa sa tashi to yaseen wannan babban bashine Wanda duk Wanda yaci shi a kauyen nan sai biya sau goma ” kugunta takara rikewa tare da murguda baki ita a dole mara kunya… Audu ne yace me yanzu yarinyannan gani kike kowa saankine a garin nan ko, zaki wuce kibamu guri kosai na tattakaki, dakikawani tsaya kina mana karkace kar kade mai kikeso amaki… Sandra hannunta ta buga akasa tace nikuwa idan zan tuna dana zo gurinnan ai bance auduba, dan tani nace ko kuwa gulm da munafurcin naka har ya wuce kan manyan yn matan garinan yadawo kaina ne, to wlh idan kaga nabar gurinnan to dan tani ne yace mun ya janye zagin ubana da yayi inba haka ba kuwa kwarankwatsa ta dubu sai anyi alo tsiya alo danja anan gurin.. Daga hannu Audu yayi kaman zai mareta dantani yayi saurin tashi ya rike hannunsa yace haba Audu inakai ina Marin wannan kanwar shedan din ai kana taba ta wani sharrin dazaka kasa fita zata hada maka.. Juyawa yayi yakalleta yace badai zaginki nayiba shine kike wannan iskancin? To nakara

miki wani naci Bantan ubanki shegiyar yarinya mara tarbiya yar iska.. Ai kaman jira take tayi wani shewa tace wallahi badai Bantan ubanaba sai dai Bantan ubanka sai goma sha biyar, kuma ni ba yar iska bace, akwai dan iskama da Yawuce kai da kake tura tani lungu kana daneta shege tsinanne dan gidan kallamu mai magalar jakai .. Ai kaman jira yake kafun ta rufe baki ya kwashe ta da wasu maruka masu lapia.. Wani ihu tayi Wanda duk Wanda yaji a garin yasan natane. “Kan bura uba walh yau ta tabo jiniya, hannu tasaka cikin aljihun wandonta taciro wani kulli Wanda yaji ke a cikinsa danka tayi da yawa acikinsa bata tsaya dashi ko ina ba sai a fuskar Audu da dantani… Dagudu tadanyi nesadasu sai groaning suke in pain tace billahillazii kuma laure da ladi kanenka sungama yawo a cikin garin nan mai dadi, kuma tine ma sai natabbata naci kan uwarta kuma insha Allahu a iskancin da kuke sai ka dirko mata cikin shege kaga kallamu mai magala yayi jika shege, kai da kana tunanin kafi kowa iya iskanci ai infada maka nawa tunkan a haifi uwar mai tagiya na iyashi kuma ni da kai Mu ZUBA MUGANi shege kafasa a garin nan. Cike da ciwo yace wlh idan na rike ki garinan mai kwantar ki sai Allah,, gabatayi tana kar kadamasa kugu tace wlh sai dai ka damki wuyan mai dan wake! Alamu taji nakam anabinta aikuwa sa gudu ta kwasa bata tsaya ko inaba sai tsakar gidansu… Saura kadan tayi ball da kwaryar hatsin da inna ke fecewa., sai haki take. Da sauri inna tamike tace ke lapiayarki kuwa yaukuma waya biyo ki ni Hajara ace kullum ni banida kwanciyar hankali a cikin garin nan mai kikeson ki zamane.. Kujerar tsakar gidan BAZLA ta ja ta zauna tana ta haki tace alquran inna dan tani ne daga jiyafa tine ta zageki na mata shegen duka shine kwai fa ya kama zagin ubana nikuma Kinsan wlh bazan bari ana zagina agarinan ina shiru ba sai dai kowa ya mutu!2 Rike baki inna tayi tace kowa kuma yamutu yannan ina bayani, nidai wlh kwata kwata banasan wannan neman maganan Naki cikin garin nanke kenan fada a makaranta fada a kasuwa, fada a dandali ina kikeson kasaka kaina ni Hajara. Ace yarinya shekara goma sha biyu Kinci ace kina dakinki amma kin addabi kowa! duka duka nawa kike eye da zakina wannan abunda dan shekara sha biyar bazaiba… Zinburo baki tayi tace yo inna su daina tsokana ta mana eye hakanan sai na ringa shiru Ana zagan mun iyaye to aradu idan basu bari ba nima bazan bari na dan duk yaran kauyen nan ba mai nuna yatsa yakoma, yo to ai ni kullum kan gaskiyata nake ban tsokanan kowa amma duk Wanda yashiga gonata to walh wuta ya kamo ai shi ciki da gaskiya wuka bata hudashi… Rufe bakinta keda wuya sukaji sallama a soro ai damugun gudu bazla tafada Dakin inna….Da karfi ta bugo kofan Dakin inna tana ta haki.. Gyale inna ta jawo daga kan kyaure tanacewa to Allah yasa lapia bawani uban kikaje kika kar tsokanowaba.. Inna na fita kofar gida ta ga dan tani da Audu tsaye bakin kofa har kasa suka tsogunna suka gaidata cikeda Girma mamawa, amsa sutayi tana neman Karin bayani da daga kallo daya tamusu tasan ba lapia ba.. Dan tani ne yafara ma inna bayanin abunda ke faruwa, salami inna tafara dan dama tana ganin bazla tashigo gidan nan a hargitse tasan ba Kalau ba.. Hakuri tashiga basu tare da musu alkawarin hakan bazai kara faruwaba.. Bayan ta sallami su dan tani gidan tashiga tana kwalama ta kira bazla bazla fito dan kaniyanki.. Bayan door din kitchen taje ta dauko wata yar sandanta wadda dama da ita take yawan bugunta idan aka Kawo mata karanta, koda kuwa bata same taba haka zasuyita yar tsere a tsakar gidan,, Yau dinma kuwa haka ta faru bazla najinta tafito da gudu suka fara tsagaye inna nace cewa aradu yau sai naci kaniyar ki inbanda isakanci dan tani saankine da zaki na masa rashin kunya!! Yunkurin kamo ta take itakuma tana ta ihu tanacewa wlh

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

DAN MACE CHAPTER 3

MU ZUBA MU GABI CHAPTER 2