in

MADADI CHAPTER 7

MADADI CHAPTER 7

motsinsu. Suna tsaka da aiki ta daka musu tsawa! Saddiqa ta juyo a firgice tana rawar baki ta fara gaisheta, ita kuwa Naja’atu ko gezau ba tayi ba ta dai tsaya da aikin da takeyi tana kallonta sai wani hayaniya take tana fuffuka! “Malama fito min daga kicin babu abinda kuka iya sai shashanci duba dan Allah duk kun cikawa mutane gida da k’auri!! soya doya kawai kamar kina soya kan uwarki.”!! Naja’atu ta kalleta da sauri tana mamakin zagin da tayi, to wa take zagi a cikinsu ita ko Saddiqa ai ko Saddiqa ta zaga ba zata bari ba sai ta rama. A nutse tace” Ni mutum idan ya zage ni wallahi ba zai min ciwo ba saboda nasan bani yake zagi ba kansa yake zagi kuma dai dan Allah mutum idan ya girma yasan ya girma mtssww!!! ta karasa maganar tana jan dogon tsaki! Halisa ta fusata sosai tace”To mara kunya mara mutunci ai dama kin saba yi min rashin kunya ohoo! yanzu dai kin ramawa Saddiqa zagin da nayi mata kenan.” Ta’be bakinta tayi tace”Eh tunda abinda kika fahimta kenan hakane.” Hanyar fita ta nuna mata da fad’in “Zoki fice min daga kicin ‘Yar iska mara mutunci masu mugun hali.” “Wallahi kece mara mutunci kuma ni ba ‘yar iska bace dan iska yasan kansa, mugun hali kuma kanki kike gorantawa tinda duk cikin danginmu ba’a ta’ba haifa mana d’an shege ba.” Jin tana nema ta ‘ballo mata ruwa yasa ta shiga kicin din tana d’ura mata ashar! tana ingizata wai sai ta fita, Naja’atu ‘yar taurin kai tace” Wallahi ba zata fita sai ta gama abinda take. Saddiqa ganin abin na neman ca’bewa sai ta fita daga kicin din tana share hawaye kai tsaye dakin Abbansu ta nufa tana kuka……….”Dan abu takazan ki a gidan ubanki muka goya d’an shege kinji yarinya da sharri.” Halisa tafada tana kokarin doke mata baki, ita kuwa fizgewa tayi ta matsa gefe tana gyara wuyan rigarta tace”Haba anti Halisa komai ‘boye-‘boyen ku mun sani Wannan Shamsiyyar sai da tayi cikin shege kafin ayi mata aure yanzu haka d’an data haifa yana gidanku gurin mahaif….Kafin ta ‘karasa halisa ta kaiwa bakinta duka! ta kauce da sauri tana fad’in “Allah ya isa wallahi.”! Karaf! a kunnansa lokacin da yake kokarin shigowa kicin din shida saddiqa, Halisa na ganinsa ta fashe da kuka tace” Yanzu Naja’atu ni kikewa Allah ya isa me nayi miki kawai daga na shigo kicin inayi muku sannu da aiki ashe zaki iya zagin Halimatu.”? Abbah Abbas ya dinga kallonta da ‘bacin rai a tare dashi yace.”Rashin kunyar taki ashe har ta kai haka? Yanzu baki duba girmanta ba kike zaginta wato kin manta maganar mu dake ko.” Kuka tasa tace”Wallahi ba haka bane dik abinda ta fad’a ‘karya takeyi ai ga Saddiqa nan a gabanta akayi komai kuma ka tambaye ta kaji, haka kawai muna aikinmu ta shigo tana zagin mu wai bamu iya komai ba mu fita mu bar mata kicin dinta, shine nace ta bari mu ‘karasa ta’ki bari tazo tana dukana.” Itama ta ‘karashe maganar tana kuka had’e da ri’ke bakinta. Abbah Abbas dik sai ya rasa ma maganar wa zai dauka, Halisa ta goge hawaye kamar gaske tace”Tunda fitina da sharri zaki dinga yi min a gida to zaki bar min gidana dama ni kikazo kika samu a gidan, dan bazan zauna dake ba watarana kisa hannu ki dake ni da girma da komai ni ba’sa’ar ki bace ballanta na nayi kishi dake, Halimatu ce dai-dai dani, dan haka ni a matsayin kanwa na dauke ki ba kishiyasa ba to tunda abin ya zama haka zaki bar min gida ki tafi naki ko kuma ni na bar miki gidan.” Tana gama maganarta ta fita daga kicin din tana goge fuskarta Halisa na fita ya juyo kanta tana rab’e jikin bango (garu) tana matse fuskarta, fad’a ya shiga yi mata wanda yake nuna mata cewar ya yarda da duk maganganun da Halisa ta fad’a tunda gashi da kunnansa yaji lokacin da take yi mata Allah ya isa! Sunkuyar da kanta ‘kasa tayi tana hawaye tana jinsa sai fad’a yake mata wai lallai idan tana son zama dashi to ta zauna lafiya da kowa a gidansa, taji kamar tace masa ai dama ba sonsa take ba da zaiyi wannan maganar ko yanzu akan ‘kaya take ya saketa ai babu dole, kwarjinsa ya hanata cewa komai kawai sai ta fita daga kicin din da gudu ta nufi dakin su Saddiqa tana kuka! Ya bita da kallo mamaki wato yana mata fada ta mai dashi soko ta barshi a tsaye, girgiza kansa yayi ya nufi palon….Ita kuwa Halisa taga lokacin da Naja’atun ta shigo palon tana kuka, sai farin ciki ya cika mata zuciya dama tasan da wuya ya’ki daukar maganar da tayi, Gani yayi duk yaran sun shirya cikin uniform ya kalli Saddiqa yace.” Yi sauri ki fito muku da bresk fast di n kafin Salim din yazo.” Saddiqa da Mufida suka nufi kicin din da sauri sune suka shirya gurin cin abincin tsaf! yaje ya zauna gurin cin abincin tare da yaransa, Saddiqa ta had’a masa tea ta zuba masa doya wacce zata isheshi, Albarka yasa mata ya dauki cup din tea yana sha, yana neman numbar Salim a wayarsa. Salim na draving yaja tsaki kafin ya dauki wayar, Yace”Afuwa Kawu ganinan kan hanya.” Yace.”Okey kayi sauri kada kasa su makara ko.” Yace.”Insha Allah nan da mintina biyar zan karaso dan na shigo unguwar.” “Okey.” Yace ya kashe wayarsa ya maida hankalinsa gurun abincin dake gabansa… Halisa ce ta fito daga daki tana wani salo-salo idanunta sunyi jawur! zama tayi kusa da kujerar Saddiqa ta dafa kanta cikin kissa tace”Sannu da aiki Saddiqa .” A dan tsorace ta amsa da “Yawwa Mommy.” Kallonta yayi yace.”Zamu fita tare yanzu za muje hospital mafi kusa a dubaki dan bana son zama da lalura.” Ta sake marairaicewa da fadin “Wallahi ba kaji yanda nake jin jiki ba gashi yarinyar nan ta ‘kara mun wani ‘bacin ran.” Yace.”Ai laifin ki ne tunda kin san halinta me yasa zaki biye mata kuyi ta cacar baki a gaban yara duk ranar data zage ki a gaban yaran nan mutunci ki ya zube wallahi gwara ki kama kanki.” Da sauri tace”Dan Allah ka bar wannan maganar da kake kamar baka san halinta ba kafin na fad’i d’aya ta fad’a min goma ni wallahi ban shiga kicin din da wata manufa kawai dai ta raina ni ne shiyasa bata ganin girmana amma yanzu na yanke hukunci kawai ta bar min gidana shi yafi amfani idan kuma lallai a gidan nan zata zauna to a gyara mata d’aya side din taje can ta ‘karata.” Yace.”Sai an kwana biyu tukkuna abinda dai nake so dake anan shine ki cigaba da hakuri kuma kina kokarin ri’ke girmanki idan kin kama mutuncinki na tabbata komai rashin kunyarta ba zata zage ki ba…..Halisa shuru tayi tana jijjiga ‘kafafunta, Saddiqa ce ta had’a mata tea ta zuba mata soyayya doya da wainar ‘kawai akai tace “Mommy gashi kiyi break .” Cikin ya’ke tace”Nagode Saddiqa Allah yayi muku albarka.” Duka suka amsa da amin harda shi, Salim ne yayi sallama ya shigo hannunsa rike da key na mota, Yaran ne duk suka mike suna gyara zaman jakar makarantarsu, Salim ya shiga rarraba ido a palon Naja’atu kawai yake so yayi tozali da ita, da bai ganta ba sai ya nufi dannig area d’in yana wani shafa kansa kai daka ganinsa kaga munafiki….Hannu ya mikawa Abba Abbas suka gaisawa yana wani risinawa kamar mutumin kirki! Ya gaishe da Halisa, tana washe baki ta amsa tana tambayarsa Yaya Ramlatu. Abba Abbas ya mike hade da daukar wayoyinsa dake kan teble din, ya kalli Salim da fad’in “Ka kai yara skullu daga bisani sai ka biyo ni kasuwar daga baya zamuje hospital da Halisa bata jin dadi.” Salim yace.”Ayya Sannu Big Aunty ashe ba kiji dadi ba Allah ya sawwak’e yasa kaffara ne.” Halisa ta mi’ke tana dan ya mutsa fuska tace”Wallahi kuwa ” ameen ya rabbi idan ka koma gida ka gaishe min da Yaya.” Ya amsa da za taji insha Allahu………Gabadaya suka fita harabar gidan yaran suka nufi motarsu ta makaranta, shi kuma Salim din ya dan tsaya suna magana da Abba Abbas din kafin yaje ya shiga motar da sauri yaja motar ya fita daga gidan, Halisa ta kame a gidan gaba tana jira ya shigo kawai sai taga ya juya da nufin komawa cikin gidan, cike da mamaki take kallonsa, to me zai komar dashi kuma! ‘kwafa tayi ranta ya ‘baci babu shakka gurin yarinyar zaije, mtsssw! an girma kamar ba a girma ba a dinga abu irin na yara abinda ta fada kenan a fili tana jan tsaki!…….Ganinshi zai dawo cikin gidan yasa tayi saurin sakin labulan window din data la’be tana le’kensu, da sauri ta nufi toilet ta kulle kofa……Kai tsaye daya shigo d’akinsu Saddiqa ya nufa saboda yasan tana ciki…..Koda bai ganta a dakin ba, sai yayi tunanin tana toilet, ya karasa bakin toilet din yana k’wank’wasawa! da kiran sunanta, tana jinsa tayi masa shuru mugun haushinsa take ji shiyasa ma bata so ta kalli fuskarsa, Abbah Abbas haka ya ‘karaci buga kofar toilet din ya hakura, dan ya kai minti goma sha biyar yana tsaye yana aikin buga kofa da kiran sunanta bata saurareshi ba, ransa a ‘bace ya fita daga dakin…..Halisa kuwa cika tayi tai fam! ta dinga hura hanci takaici da bakin ciki kamar su kasheta, haka ita dashi sukayi tafiyar kowa ransa a ‘bace! BHRBN *24* Tana jin fitarsa daga dakin ta fito daga toilet din, zama tayi k’asan kafet ta had’a kai da gwiwa abin duniya duk ya isheta, ta kai minti ashirin a zaune tana sa’kawa da kwancewa kafin ta yanke shawarar mi’kewa ta dauki hijabinta tasa, hanyar fita ta nufa, Gidan Abbah Magaji za taje dan ba za tayi zaman kad’aici ba gabadaya gidan girma yayi mata ta dinga jin tsoro na shigarta…..Koda maigadi yaga zata fita baice mata komai ba dan shine ma ya bude mata karamar kofa ta fita yana yi mata adawo lafiya…..Tana kokarin shiga gidan Abbah Magaji Salim ya shigo da mota, tsayawa tayi har yayi parking ya le’ko da kansa yana d’aga mata hannu wai taje, dama sabida ita ya dawo gidan bayan ya ajiye yara a skull, cikin zumudi gami da farin cikin ganinsa ta nufi inda motar take, Ya bude mata ta shiga ta zauna kusa dashi tana fara’a da fadin “Wallahi naji dadin ganinka.” Ya saki wani murmushi yana shafa sumarsa hade da yi mata shegen kallonsa yace.”Na shigo gidan tun dazu ina ta rarraba ido banga sanyin idaniya taba, shiyasa na kasa wucewa kasuwa kamar yanda mijinki ya bukata nace sai na dawo nayi tozali dake.” Tana murmushi tace”Ina dakin su Saddiqa ban san kazo gidan ba.” Yace.”Ina fatan dai wani abu bai shiga tsakaninki da wannan dattijon ba.” Gabanta ne ya fadi ta kalleshi a sanyaye tace”Babu wani abu da ya shiga tsakaninmu ai nayi maka al’kawarin kai zan mallakawa kaina.” munafikin murmushi yayi yace.”Nagode Princess yanzu inaso ki d’an yi min abinda zai d’ebi min kewarki idan naje kasuwa.” Tace”Ban gane abinda kake nufi ba.” Kallon kasan ido yayi mata yace.”Haba baby sai nayi miki bayani dalla-dallah ashe har kin manta hirarmu ta jiya da irin amsar da kika bani, yanzu fa kika gama cewa jikin ki da komai naki nawa ne to inaso ki d’an fara gwada min soyayyar da kikeyi min a zahiri.” Cike da mamaki take kallonsa dan ta fahimci inda maganar sa ta dosa, shuru tayi ta kasa magana, kawai taji ya kama hannunta ya rike yana shafawa, Da sauri ta cire tana d’an hararasa tace”Idan sai na rungume ka ko nayi maka kiss sannan zaka gane kaunar da nake maka gaskiya ce, to kuwa sai dai kada ka yarda dani da son da nake maka koda nake cewa komai nawa naka ne ai ba ina nufin mu aikata haramci ba inaso bayan na rabu da wannan ‘kaddararran auran muyi aure da kai mu mori junanmu shine abinda nake nufi.” ‘Bata fuska yayi yace.”Dan kiyi kissing d’ina ko kin rungume ni ai ba wani abu bane amma tunda kince haka shikkenan.” Cikin rashin walwala ya ‘karasa maganar, Tace”Gaskiya kayi hakuri ba zan iya ba.” Cikin fusata yace.”Okey fita a motar nan na tafi inda zani dama duk karya ce ba wani sona kike ba da kina sona ba zaki tsaya jayayya dani ba.” Ganin ya fusata! yasa jikinta yayi sanyi murya na rawa tace”Dan Allah kayi hakuri ka gane abinda nake nufi bana so ranka ya ‘baci.”! Yaja tsaki mai tsayi da fad’in “Bacin rai kuma wane iri ai raina ya gama ‘baci dake.” Tace.”To kayi hakuri my love kada kayi fushi dani zuciyata zata shiga wani yanayi mutukar kana fushi da ita.” Ta’be bakinsa yayi yace!.”Ai kin bani mamaki wallahi amma babu komai ina ganin zan hakura dake na fara duba ‘yan matan da suke sona sai na fitar da gwanata a cikinsu.” Jin ya fad’i haka sai hankalinta ya tashi murya na rawa tace”Dan Allah kada kayi min haka my Prince. ” Fuskarsa ya mi’ka mata da fadin” Okey oya kiss me idan kina sona.” Ta dinga dawurwura kafin ta kai bakinta fuskarsa ta manna masa kissi da sauri ta cire bakinta tana jin nauyi da kunyar abinda tayi, murmushi yayi yana shafa gurin da tayi masa kiss din ya kalleta yana wani lumshe idonsa yace.”Allah ya nuna min ranar da zan had’a bakina da naki ina mutukar so naji ina tsotsar wannan lips din naki masu kyau da daukar hankali.” Yana kokarin kai hannusa kan le’bunanta yake maganar, ba ta bari ya kai hannunsa fuskarta ba ta bude motar da sauri ta fita daga ciki gabanta sai faduwa yake……Salim ya kalleta cike da mamaki! kamar xaiyi magana kuma sai yayi murmushi yana girgiza kansa ya kunna motar had’e da daga mata hannu da fadin “Zan kira ki a waya idan anjima akwai labarai masu dadi ina so ki tanadi amsar da zaki bani.” Hannunta ta d’aga masa tana ya’ke tace”To shikkenan sai na jika.” Motar yaja ya bar gurin ita kuma da sauri ta nufi gidan Abba Magaji tana waiwayen bayanta kamar wata mara gaskiya…….Salim yana draving yana duba wayarsa yana sakin wani shegen murmushi ashe lokacin da take kiss d’insa ya saita camera……Hoton ya fita sosai kamar dama da son ranta hakan ya kasance fuskarsa da murmushi itama tata fuskarsa a sake duk wanda yaga hoton zai fahimci cewar masoya ne, ba tare da ‘bata lokaci ba ya d’ora hoton a fuskar wayarsa domin yana so Allah ya nunawa Kawun nasa hoton ya gani yasan dole ransa zai ‘baci ! idan ya tambaye shi shi kuma yana da amsar da zai bashi. Aunty Maryam na zaune a palo ita kadai yaran duk sun tafi makaranta kawai taji sallamar Naja’atun, cike da mamaki take kallonta har ta ‘karaso inda take ta zauna kujerar kusa da ita tana gaisheta, Aunty Maryam ta amsa mata cike da kulawa tace”Naja’atu me ya fito dake ina fatan dai lafiya.” Murya na rawa tace”Lafiya lau Anty gidan ne shuru su Saddiqa sun tafi skull Anty Halisa da Abba sun fita a tare ni kuma tsoron gidan nake.” Anty Maryam tace”Ayya ai sai a hankali zaki saba ina fatan maigidan ya san zaki zo nan.” Shuru tayi tana wasa da hannunta. Anty Maryam tace”Be sani ba kenan naga kinyi shuru.” Tace”Ai na dauka babu wani abu dan nazo tunda koda can muna zuwa da Yaya Halimatu.” Anty Maryam tace”Eh duk da haka dai yana da kyau ya san zaki zo itama marigayi ya kafin ta fita zuwa wani guri ai tana fad’a masa ko baki san yanzu haka mala’iku na tsine miki ba.” A sanyaye tace”Na sani anty.” Tace”To amma kin sani kika take.”! Shuru tayi dan bata da abinda zata ce, Anty Maryam tace”Yanzu ki kira wayarsa ki fada masa gaki anan gidan nasan ba zaiyi fad’a ba.” zum’bura baki tayi gaskiya ba tajin zata iya kiran wayarsa dan ba ‘karamin haushinsa take ji ba. Anty Maryam

tace”Dake nake magana fa kodai har yanzu baki saduda kin kar’bi auran ba.” Fashewa tayi da kuka tace”Dan Allah anty ki kyaleni ni bazan kira wayarsa ba saboda bashi da adalci.” Cike da mamaki antyn take kallonta tace”To ikon Allah wane iri rashin adalci yayi miki kuma.”? Hawaye ta goge tace”Anty duk da bana sonsa da auransa ya dace ya bawa Anty Halisa ta had’a min lefe baki ga banzayen kayan data siyo min ba kuma wallahi nasan tana sane tayi haka dan ta bani haushi! sannan kuma d’azu tazo tana zagina harda dukana a baki a maimakon ya tambayi ba’asi kawai sai ya dauki laifi ya d’ora mun.” Anty Maryam tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas komai akace Halisa ta aikata ba zata musa ba saboda dama tasan halinta, Halimatu tasha wahala a hannunta, dalili kenan da ya sanya basa shiri da juna da ita gasu dai ma’kota kuma mazajensu abokan juna ne amma kowa sabgarsa yake a tsakaninsu babu jituwa ko ta kwabo……Cikin rarrashi tace”Kiyi hakuri da Halisa nasan dai kin san hakurin da Marigayiya tayi da ita to kema inaso ki kwatanta ko kifi nat…..”Gaskiya anty ba zan iya ba wallahi.” Ta katse tun kafin ta ‘karasa maganar. Anty Maryam tace”Ke me yasa bakya tsawa a baki shawara ne? Halisa bata da kirki macace muguwa mai shegen kissar tsiya babbar macace ma ya ta iya da Halisa ballanta na ke! ki tsaya ki saurare ni da kyau! yanzu fushi ke ba naki bane! kamata yayi lokacin da yake fadan sai ki bashi hakuri ki fad’a masa yanda abun yake ba kiyi zuciya ba, kinga yanzu ita bukatarta ta biya ta had’aku fad’a sun ma fita unguwa tare dashi babu abinda ya dameta, to gobe ma haka zata sake miki ke kuma gaki mara wayo sai kiyi fushi ki tsaya girman kai ke ba zaki bada hakuri ba to ba haka ake zamantakewa ba.” Tana kuka tace”Anty nayi yunkurin fad’a masa abinda ya faru ya’ki saurarata shiyasa nima na bashi guri.” Anty Maryam tace”Yanzu dai magana ta wuce kodan gaba kada ki sake aikata hakan idan wani abun ya shiga tsakaninki da Halisa yazo yana miki fada ki bari ya gama tukkuna sai ki fada masa abinda ya faru kada ki sake bar masa gurin bai dace ba.” Cike da mamaki take kallonta tace”Anty sai na zauna kawai ya dinga yi mun fada alhalin ba laifina bane.” Anty Maryam tace”To meye yau da gobe da kansa zai gane gaskiya dan me yasa Halimatu ta ciri tuta a gurinsa nasan har ya mutu ba zai mance da ita ba saboda tayi masa ladabi da biyayya.” Girgixa kanta ta shigayi gaskiya da kamar wuya wai gurguwa da auran nesa Halimatu daban

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 6

MADADI CHAPTER 8