in

MADADI CHAPTER 6

MADADI CHAPTER 6

hard’e a kan kujera tana jiran zuwansu……… Saboda yasan zai samu matsala daga gurinta yasa ya shiga gidan fuskarsa a murtuke dan baya so tayi masa rashin arziki ya lura ba tayi maraba da zuwan Naja’atun ba……Mussadiq na ganin Naja’atu tare da Abbansu ya tashi a guje yaje ya rungumeta, Allah sarki yaro kenan har ya mance abinda tayi musu, tsugunawa tayi ta rungumeshi tana sumbatarsa a fuska, Abba Abbas kuwa bai tsaya ba kai tsaye dakinsa ya nufa, Halisa ta mike ta bishi tana huci!! Dama ya tsammaci shigowarta, ya tsira mata ido yana kallonta ganin yanda idonta yayi jajawur lokaci guda, Ri’ke ‘kugu tayi tace”Nifa bangane ba meye amfanin kawo ita gidana naga harda jakar kayanta.” Yace.”Eh kamar yanda na fad’a miki a waya hakane tana jin tsoron zaman gidan ita kadai shine dalilin da yasa na daukota na kawo ta ta zauna nan kafin na yanke hukunci.” Murya na rawa tace”To ba sai ka kai mata su Saddiqa su taya zama ba, meye sai ka kawo min ita gida.” Yace.”Ina tunanin ko ta ganta tare dasu Saddiqar ba zata samu nutsuwar da ake bukata ba.” Tace”To naji a’ina kake shirin ajiyeta.” Cikin jin haushin titsiyen da take masa yace.”A duk inda nayi ra’ayi gidana ne ai.” Ganin ya fusata! yasa ta dan sassauta tace”Sai dai a gyara mata d’aya sashen ta zauna dan ni bana jin zan iya zama tare da ita.” Yace.”Ai dama ba’ace dole ki zauna da ita ba tunda ita tafi so ta zauna anan ke yanzu zanyi duk yanda zanyi cikin satin nan a gyara miki inda zaki zauna a can gidan.” Girgiza kanta tayi tana ‘kas-‘kas! da cingum! din bakinta tayi wani murmushi tace”Ba zai yiwu ba! ai na fad’a maka ba zan amince da wannan rabe raben gidan ba, nima ina nan babu inda zanje.” Daga mata hannu yayi yace.”To magana ta ‘kare kada nan gaba kice min zaki koma can dan ba zaki koma wallahi.” Tace.”Ai duk inda kake ina nan idan ka tattara ka koma can nima zan tattaro nawa nawa na biyo bayanka.” Shuru yayi mata ya zauna gefan gado, ta juya ta fita tana fadin “Bari na kawo maka kayan break din.” Tana fita ta

gansu zaune a kujera sun kewaye ta har da Mufida sai murna sukeyi tamkar sunga wata sabuwar hallita, ita kuma sai murmushi take musu…..Halisa taja tsaki cikin tsawa tace”Ke Mufida me kike anan zo nan ki taya ni ‘aiki.” Yarinyar ta mike da sauri! Halisa ta nuna mata hanyar kicin tana fad’in “Bana son shashanci ni kun wani zauna kuna dariyar banza.” Naja’atu dasu Saddiqa suka bita da kallo tana kokarin shiga kicin tana surutai………Bayan shigewar Halisan, ta kalli Su Saddiq tana nazarinsu, kwana biyu da bata gansu ba sai taga kamar sunyi rama ta rike hannun Mussadiq tare da fad’in “Kayi rashin lafiya ne.”? Girgiza kansa yayi yace.” Yaya Naja’atu kema kin dawo nan kenan na dauki akwatin kayan ki na kai miki dakinmu.”? Kanta ta d’aga masa idanunta na kawo ruwa, da sauri yaron yaje ya shiga jan jakar kayan Saddiqa ta mike taje tana taimaka masa, Naja’atu binsu tayi da kallo hawaye ya zubo mata tausayi yaran suka bata, tana ganin ko dan saboda su zata dinga adduar Allah ya sanya mata dangana domin ta zauna tare da dasu…….Halisa ce ta fito daga kicin hannunta ri’ke da tire jere da kayan tea ko kallon inda Naja’atun take ba tayi ba tayi ba ta nufi dakin maigidan, Naja’atu ita dai binta da kallo kawai take………. Yana zaune ‘kasan kafet ta shiga dakin, ajiye tiren tayi ta zauna tana kokarin had’a masa tea din yace.”Ki bawa Naja’atu abinci dan bana tsammanin taci wani abu tun jiya.” Kallonsa tayi kamar za tayi magana kuma sai ta fasa, ta hada masa tea kana ta zuba masa farfesun kayan cikin rago wanda yaji magani! ta mike ta fita daga dakin………..Saddiqa ta kalla tace”Ke Saddiqa ki shiga kicin ki girka muku abinda zaku ci dan ni ba baiwar kowa bace.”! tana gama maganarta ta shiga dakinta…… Saddiqa ta mike da sauri tana kallon Naja’atun tace.”Don Allah Yaya Naja’atu kada ki kulata.” Murmushin takaici tayi tace.”Jeki yi aikin ni ba’a gabana take ba ballanta na tanka mata.” Saddiqa ta sauke ajiyar zuciya ta wuce kicin din, mikewa tayi ta nufi dakin su Saddiqar nan ta tarar da Mussadiq yana ta jera mata kayanta a cikin wardorbe dinsu, Tace”Mussadiq daka bar kayan ma a jakar da yafi.” Yace.”Ai akwai guri a wardrobe din shiyasa nake shirya miki kayanki a ciki.” Zama tayi tana bin dakin da kallo, gado uku ne kananu irin na ‘yan boarding….Mussadiq yace.”Yaya Naja’atu zan baki gado na ki kwanta kafin Abbanmu ya kawo miki naki.” Tace”To nagode Mussadiq.” ya mike da sauri yana fad’in “Bari ma naje na fada masa.” Kallo ta bishi dashi har ya fita daga dakin….Dakin Abban nasu yake kokarin shiga Halisa ta hangoshi tsawa ta buga masa da fad’in “Me zaka shiga kayi.”? Yace.”Zan fad’awa Abbanmu ne cewar Yaya Naja’atu bata da gado.” Cikin tsawa! tace”To sarkin iyayi da rawar kai ai ya fika sani.” Abbah Abbas din ne ya fito daga dakin nan Halisa ta gyara yanayin fuskarta Tace.”Gashinan wai yana so ya shiga yayi magana da kai shine nace masa kana cin abinci sai ka fito tukkuna.” Ya kalli Mussadiq din a nutse yace.”Menene.”? Mussadiq yace.”Abbah Yaya Naja’atu bata da gadon kwanciya amma kayanta sun samu guri a wardrobe d’in mu.” Murmushi yayi yace.”Gaskiya Magaji kana son Yaya Naja’atu sosai kada ka damu zansa a kawo mata gadonta

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 5

MADADI CHAPTER 7