in

MADADI CHAPTER 5

MADADI CHAPTER 5

maganinta…….Mufida na goge hawaye tace.”Mommy ya kike zaginsu su Yaya Saddiqa ne fa ‘yan uwana.” Wani irin bahagon mari ta kifawa yarinyar tana huci! tace”Zanci Kutumar ubanki wallahi shegiya munafuka ni zaki fad’awa su d’in ‘Yan uwanki ne? Wallahi duk ranar da kika ‘kara kiransu da sunan ‘yan uwanki sai naci ubanki.” Mufida tana kuka tace”To mommy me yasa kika tsanesu bayan mamansu ta mutu dan Allah ki daina yi musu abinda kike musu babu kyau.”! A fusace! ta sake gaura mata wani mari tana wata irin fuffuka tace”Tashi dan babanki mara mutunci ki bar min dakina ko kuma yanzu na sumar dake.” A gigice! yarinyar ta mike hannunta dafe da kuncinta ta fita daga dakin tana kuka, wanda yayi dai-dai da fitowarsa daga daki yana sanye da jallabiya ruwan toka, Ganinsu Saddiqa sunyi muzu-muzu a zaune yasa jikinsa yayi sanyi ya kalli Mufida dake dafe da kunci tana kuka, yace.”Menene? Cikin rawar murya tace”Mommy ce ta mare ni tace na fito mata daga d’aki. Ba tare da yace.”Komai ba ya kama hanyar dakin Halisan, Har yanzu tana zaune gefan gado ta had’a tagumi babu maganar sallah a tare da ita, cikin nutsuwa ya shiga dakin bakinsa dauke da sallama, Kallonsa ma ba tayi ba ballanta ta amsa masa sallamarsa, gefanta ya zauna yana kokarin ri’ke hannunta ta fizge a fusace! ta mike tsaye tana nunashi da hannu tace”Kaga dan girman Allah ka fita ka bani guri naji da abinda ke damuna baka da abinda zaka ce dani.” Yaji zafin maganarta amma sai ya danne ya mike ya iske inda take, Rungumeta yayi a jikinsa yayi amfani da wata murya wacce ya tanade ta dan rarrashinta, yace.”Haba Halisa wai duk me yayi zafi ne kike nema ki zautar da kanki akan abinda bai kai ya kawo ba! Menene abin damuwa dan nace zan auri Yarinyar nan Naja’atu? idan kin kwantar da hankalinki kin ri’ke girmanki sai kinfi daraja da kima da martaba a idona! Shin wai baki ga yanda Halimatu ta sadaukar da rayuwata a kaina ba, bana shakka ko tantama Halimatu yanzu tana gidan aljanna saboda ta rabu dani da iyayenta lafiya, kuma ta mutu hanyar haihuwa, har na gama rayuwata ta duniya bazan ta’ba mantawa da Halimatu ba, a kwanakin baya kin soma kwaiwayon hali da d’abi’unta amma tashi guda zaki watsar da abin da kika fara na alkairi, wallahi auran Naja’atu da zanyi ba zai sanya ni na daina kaunarki ba, kin san dai kece macen dana fara furtawa kalmar so, ko Halimatu ma kece kika jawo na aureta, to itama Naja’atun ina so ki sani bani ne nace inaso ta zama *Madadin ‘Yar uwarta ba* Iyayenta ne suka nemi haka dan ko yanzu sai da na fada musu cewar maganar auran su barta suka nuna sai anyi So inaso ki kwantar da hankali ki samu nutsuwa ki kula dani da yarana gasu nan na kawo miki su ni kuma insha Allahu zan baki mamaki zan nuna miki ni d’an halak ne auran Naja’atu ba zai sa na juya miki baya ba.” Shuru tayi jikinta duk yayi sanyi da kalamansa tace”Nifa ban hanaka aure ba wallahi ko budurwar zaka aura to kaje ka aura amma banda yarinyar nan bana kaunarta saboda bata ganin

girmana.” Yace.”Na fad’a miki fa cewa kece uwargidana duk ragamar mu tana hannuki har ita Naja”atun idan tazo a ‘karkashin ki take sai abinda kika tsara a gidan shi za’ayi.” Jin wannan maganar tasa yasa ta sauke ajiyar zuciya tace”Nifa wallahi nasan dadin baki ne kake mun yarinyar nan na zuwa zaka manta dani, dan haka gwara tun kafin tazo na san inda dare yayi min dan bana tunanin zan zauna da ita a karkashin inuwa guda.” Yace.”In banda abinki ba gidanku daya ba to me zai dame ki da ita ko wacce na gidanta idan wannan da kike ciki bai miki ba sai na sauya miki wani.” Tsaki taja tace.” bazan yarda ba wallahi sai dai ka had’amu gida daya dan bazan amince a cutar dani ba.” Yace.”To shikkenan duk abinda kike so shi za’ayi, Zan sa a gyara miki side d’inki dake gidana na *’Danbare* ina fata hakan yayi miki.” shuru tayi tana zum’bura baki, Ya saketa yaja hannunta suka zauna a nutse yace.”Ki fad’a mun duk abinda kike so na siya miki na fad’ar kishiya komai tsadarsa zan siya miki.” Tace”Sai nayi shawara tukkuna.” Dariya ta bashi amma beyi ba yace.”To shikkenan inaso na baki kudi kije ki had’o mata lefe kuma kema ki had’a naki hakan yayi miki.” Dadi ne ya rufe ta tace”To Hakan yayi amma inaso ka sanja min mota.” Yace.”An gama ranki ya d’ade! amma dan Allah daga yau sai yau kada ki sake aikata abinda kika aikata a d’azu! rashin hankali ne kawai kije ki dauko wu’ka kina so ki kashe ni! kina tare da shed’an a lokacin idan da tsautsayi sai ki aikata aikin dana sani ki ‘kare rayuwarki cikin uku’ba kuma ki mayar min da yara marayu.” Hanci ta sha’ka! cikin takaici tace”Haba ai wallahi idan ma nayi maka rauni ban huce bacin raina ba, kana kallonta ina magana ka tsalleke ni ka tafi ai dole zuciya ta ta tunzurani a kanka.” Yace.”Tom yanzu dai duk magana ta wuce Gobe insha Allahu bayan sakkowar sallahr juma’a za’a daura auran amma ina tunanin ba zata tare ba sai nan da sati biyu.” Halisa gabanta ya fad’i tace”Da wuri za’a daura auran ashe.”? Yace.”Baba Malam ne ya yanke hukuncin haka.” Cikin tsabar bakin ciki da takaici tace”Aikin banza aikin hofi ‘kwad’ayayyen tsoho mai son abin duniya ai dama dole ya gaggauta yin abun kodan bukatarsa ta biya.” ‘Bata rai yayi yace.”To yanzu zamu ‘bata dake kuma bana son wannan d’abi’ar taki ta zage-zage da rashin ganin girman manya.” Cikin fusata! ta mike ta nufi toilet tana surutai da ‘kananun maganganu, kallo ya bita dashi, Al’amarin Halisa dai sai gyaran Allah, yaji dadi sosai da ya shawo kanta cikin ruwan sanyi *(Tabbas haka maza ya kamata su dinga rarrashin matansu idan zasu ‘kara aure, sau tari wasu mazan sune suke ingiza zuciyoyin matansu ga aikata abinda ba shikkenan ba, idan ya kasance zaka ‘kara aure to yana da kyau ka dinga nuna kulawarka a kan matarka ta gida, kuma banda kiran wayar amarya a cikin gidan dan hakan ma na iya janyo muku samun sa’bani a tsakaninku*) Mikewa yayi ya fita daga dakin yana dan jin sassauci a cikin zuciyarsa tunda ya gama da matsalar Halisa yana ganin duk abinda zai biyo baya mai sauki ne. Yana fitowa palon ya gansu a zaune duk sunyi tsuru-tsuru Mussadiq ma gyangyadi yake, Ya kalli Saddiqa data had’a tagumi hannu bibbiyu har yanzu zuciyarta na jin ciwon abinda Naja’atu tayi musu a d’azu duk da take yarinya wacce bata gama mallakar hankalin kanta ba ta gane ba ‘karamar ‘kiyayya Naja’atu keyi wa Abbansu ba, sai ta dinga tunanin to wai meye aibunsa da har zata dinga ‘kinsa da kuma zaginsa, sam bata ta’ba tsammanin haka daga gareta ba…… a nutse yace.”Saddiqa kuje ku kwanta kinji ko, dukkaninku ku daina damuwa ku saki

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 4

MADADI CHAPTER 6