in

MADADI CHAPTER 3

MADADI CHAPTER 3

Baba Talatu kullum koko da kosai take bani, sannan bata bani na siyo alawa da biscuit. ” Baba Talatu ta ri’ke ha’ba! tana fad’in “Ikon Allah! Wato Naja’atu abinda zakiyi mana kenan! kullum fa sai na dafa miki shayi malam ya siyi miki bredi da madara ga kwai amma kice koko da kosai nake baki.” ? Halimatu tace”Gaskiya Baba bakya ji da wannan autar taki! dubeta dan Allah yanda kika barta tayi daud’a dubi kitson kanta duk ya tsufa, gashi bakya bata ta siyi sweet da biscuit saboda haka ni zan tafi da ita gidana, zaki bini ko Auta.”!? tafada tana kallonta, Da sauri ta daga kanta tana dariya…..Baba Talatu ta gyara zamanta tana ta’be baki tace”Ai sai kuje dama nima na gaji da bari bari yarinya kullum nakan layi tana yawo ta’ki zama a makaranta malam na kaita kafin ya dawo gida ta rigashi, ki tafi da ita ku sata a makaranta tayi karatu watakila idan taga babu idanmu zata zauna a makarantar. Halima tace”Aikuwa dai bari Baba Malam ya shigo na fada masa…….To koda Baba malam yaji kudirin Halima na tafiya da Naja’atu gidanta, be’ki ba yace dai idan taga da akwai matsala to ta dawo da ita.” Baba Talatu ta hada mata kayanta tsaf suka tafi. *Wannan shine mafarin dawowar Naja’atu hannun ‘Yar uwarta, a lokacin tana da shekaru hud’u a duniya dalili kenan da yasa ta girma da tunanin cewar Abba Abbas da Halimatu sune suka haifeta.* Ita kuwa Halisa koda ta fita kai tsaye tudun wuzurci ta nufa gidan Yaya Ramlatu! basu ja dogon lokaci ba suka dauki hanyar gidan *’Yar Sa’adu* abin mamaki mata ne dan’kam! a gidan! d’aki guda idan waccan ta shiga ta fito sai waccan ma ta shiga ta fito har akazo kansu! koda suka shiga dakin *’Yar Sa’adu* na zaune kan wata kujera katuwar macace mai ki’ba taci uwar kwalliya ga hancinta da wani abu mai kyalli a jiki, hannu da wuyanta duk gold ne! taci ubab bleecig kana ganinta kaga ‘yar duniya, suka gaisa da juna, Halisa sai kallon dakin takeyi ganin ko ina manne da hotonan mace da namiji tsirara! sannan ga wasu manya manyan drowars ko wanne kayan mata ne a cike a gurin kala-kala! Yaya Ramlatu ta ciro kudin jakarta dubu talatin da biyar ta zube gaban *’Yar sa’adu* tace” Uwar dakina wannan itace matar ‘kanina da nake baki labari gata nan na kawo miki ita don Allah ki san maganin da zaki bata wanda zai sanya ta mallaki mijinta ita kad’ai.” *’Yar Sa’adu* tasa dariya ta bata hannu suka tafa tace”Lallai ‘kawata kina ji da matar ‘kanin nan naki! Allah yasa idan ta samu duniya ta tuna dake, akwai wata mallaka da zan bata! Amma gaskiya tana da tsada kuma naga kudin da kuka ajiye bashi da yawa! Wannan mallakar tana da sirri dan da yawa mutane sunyi amfani da ita sun tabbatar da gaskiyar maganata, ina zaune ake zuwa anayi min tukwuci da kujerar makka had’e da gida da filaye, dan haka idan kuna da bukatar na baku ita to gaskiya zaku ajiye min dubu dari biyu.” Halisa tayi saurin kallonta tana marairaice fuska tace”Dan Allah ki bani

wallahi nayi miki al’kawarin idan bukata tabiya zanzo na kawo miki kudinki har inda kike.” Ramlatu tace”Eh kwarai kuwa ni zan zama sheda a tsakaninku tunda dai kin tabbatar da ingantuwar maganinki to ki amince ki bamu insha Allah cikin sati guda za’a kawo miki sauran kudinki.” *’Yar Sa’adu* tayi shuru tana tunani! Wani littafi ta dauko ta mikawa Halisa da biro tace”To na amince zan baki amma kisa hannu! sannan ki rubuta abinda kika bani da farko.” Halisa ta kar’ba da sauri tasa hannu! sannan ta rubuta kudin data bayar dubu talatin da biyar! *’Yar Sa’adu* ta kar’ba ta ajiye, sannan ta mike taje ta dauko mata wata ‘yar mitsitsiyar kwalbar fiya-fiya! wani abu mai mai’ko da yau’ki! ne a ciki tace”Gashinan duk sanda zakuyi auratayya da mijinki to sai ki lakata kad’an a d’an yatsan ki! sai ki tofa maliki yaumin dini ‘kafa takwas a jiki sai ki lakata maganin a gabanki, kafin kwana biyu zaki bani labari.” Halisa ta dinga washe bakinta tana godiya, *’Yar Sa’adu* tace”Mijin ki zai zame miki kaska sannan ba’kin ciki zai kashe kishiyarki wannan shine la’kanin maganin.” Wani sanyi ya sauka a zuciyoyinsu jin abinda ‘Yar Sa’adu ta fada, godiya sukayi mata sosai tare da al’kawarin insha Allahu cikin satin nan zasu kawo mata kud’inta…….. *Ayar Allah da ita ake wasa, wai kuma mutum yace yana so yaga dai-dai a rayuwarsa, Ubangiji Allah ka karemu daga fad’awa halaka* Kamar dai yanda ‘Yar Sa’adu tafad’a musu hakane ya kasance, kwana biyu zamantakewar gidan ta samu tangard’a! Abbas hankalinsa ya dauke gabad’aya baya ganin kowa a gabansa sai Halisa! Komai ta tambayeshi baya yi mata musu da gardama, kuma koda ya duba gurin da yake ajiyar kudinsa yaga ba yanda yake ba, da yayi mata magana kai tsaye tace”Ita ta dauka tayi ba’ki ta sallamesu! shuru yayi mata baice komai ba, tana ganin ya shiga toilet ta bude drowr ta dauki dauri d’aya ta mayar ta rufe! Sai da ya fita sannan ta lissafa kudin dubu dari ne, kai tsaye ta yafa mayafinta ta nufi gidan Yaya Ramlatu da kudin, Gidan ‘Yar Sa’adu suka nufa, nan Halisa ta zauna tayi ta basu labarin yanda al’amura suka kasance ta dinga basu labarin irin abun da Abbas din yake mata idan suna kwance da daddare! ‘Yar Sa’adu da Ramlatu suka dinga dariya suna tafawa! ita kuwa Halisa tace”Ai gaskiya maganin nan karshene kuma yaci kudinsa, dan a tsakanin kwanaki bakwai d’in nan sai da na samu kudi a gurin sa sama da dubu dari! kullum in zai futa sai na

What do you think?

Written by BankinHausaNovels

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

MADADI CHAPTER 2

MADADI CHAPTER 4